check your best novels here

Saturday 11 March 2017

SABON AL'AMAREE 19/22

[13/02 11:54] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE


 BILKEESA IBRAHEEM
     {♡bilyn Abdul♡}


                             
                        19                         
......Alh usman yaja nunfashi tarda furzarda huci mai zafin gaske, kuyi ha'kuri 'yan uwana yakamata mu buďe sirrin dake cin zuciyarmu domin samun nutsuwar zukatanmu...............da sauri Alh habib ya katseshi yaya nikam daza'abi tatawa dakawai anzartar da wasiyyar baba batareda an tono sirrin daya wuceba a baya,, bayyanar wanan sirrin zaisa wasu suji wani SABON AL'AMAREE a rayuwarsu, koya kuka gani 'yan uwa???, yafaďa yanamai kallon fuskokin 'yan uwannasa.
    Gaba ďaya suka amsa da eh hakanma yayi, basai antuna bayaba, alh usman ya jinjina kai to shikenan hakanma yayi nima nayarda da shawarar ku.
   Wani littafi yajawo yashiga buďewa sanan yay gyaran murya, ina bu'katar nutsuwarku da hankalinku,, gaba ďaya suka maida hankalinsu gareshi, yajawo farin gilas ďinsa yasaka yafara karanta takardar kamar haka.....
       ASSALAMU ALAIKUM. Yaku 'ya'yana, inafatan takardarnan tawa zata riskeku alokacin dakuke cikin farinci dakuma haďinkai,, ina addu'ar ALLAH ya haďamin kanku har bayan raina.
    ALLAH yasaukar da farinciki da 'kaunar juna da zuminci arayuwarku,, ni Alh mutallaf ina maimuku wasiyya akan na aurar da ďiyar MUSBAHU ga yaron ABDUL'MALIK wato MAHMUD, nayanke wanan hukuncine domin yabawa da hankalin yaron inada tabbacin bazai ta6a 'kyamartaba bare watarana ya goranta mata.
   Kukuma karkusaka wani abu azuviyarku, karku ďauka na fifita Abdul'malik ne akanku, karku ďauka nafiyarda da tarbiyyar 'ya'yansane fiye da naku,, A'a nayi hakane saboda aranar da ASMA'U zata rasu tayi al'kawarin mallakawa mahmud ďiyarta inhar ta girma saboda son dayakema yarinyar.
   Saikuma ALLAH ya amshi rayuwarta awanan ranar tatafi batareda cika alkawarin data ďaukaba,, to dan haka nina cika mata kafin nabar duniyar nima,, dan banida tabbacin kaiwa lokacin da yarinyar zata mallaki hankalinta ta isa aure,
    inafata ko bayan raina ku ida cika wanan al'kawarin ku mallaka masa matarsa alokacin bu'katar hakan ta taso, ALLAH yayimuku al'barka ya 'kyautata rayuwarku data 'ya'yanku data 'ya'yan 'ya'yanku.

                   Alhji mutallaf mahaifinku....

Kowa ka kalla fuskarsa tana zubar da hawaye, lalai yau ansosowa wanan family inda yake musu 'kay'kayi,, da'alama kuma akwai wani 6oyayyen al'amaree dabasu bayyanaba, basaso 'ya'yansu suji wani SABON AL'AMAREE dayake arufe kuma sirrin wanana family,, tokomadai miye idan tayi wari aizamuji.
   Daga nan suyi addu'a da tattaunawa akan abinda yashige musu duhu, aka kuma tsaida ranar biki kowa yakama gabansa. (Tofa kowacece wanan amaryar ta ya mahmud,, kudai kubiyoni kawai).
      Tunda daddy yadawo gidan baibi takan kowaba ya haye samansa ya kwanta, sai gabda azhur yatashi yay wanka yasakko zuwa masallaci, koda yadawo saiya zauna a falon 'kasa, tabbas muhimmin abune yake zaunar da daddy falon 'kasa, dan haka kodasu Nurr suka fito suka ganshi sai tsoro yakamasu, gashi fuskarsa babu walwala sosai, ya ce, "suje su kira masa mama da mami, to suka amsa cikin girmamawa,, babu daďewa suka fito sudasu mama, saidai suma idan ka kalli fuskokinsu zakaga basuda walwala, lalai akwai damuwa tattareda wannan family ayau saidai basusan wane SABON AL'AMAREE bane ya kunno kai acikin family ďin nasa, su mama suka nemi guri suka zauna,, babu daďewa saiga ya Mahmud da ya faisal, suma suka nemi guri suka zauna bayan sun gaida iyayen nasu,, su ya Mustapha ma suka shigo suma gaisuwa sukayi suka zauna,, su deena dai suna kallon ikon ALLAH, saiff yafito shima ya zauna, saida daddy ya gama binsu da kallo sanan yay gyaran murya, tareda yin sallama, gaba ďaya suka amsa akasalance.
   Ya gyara zamansa ya share kwalla, sukam cikin tsoro suke kallonsa dan ganin yana matse hawaye, dama mama da mami tun ďazu suke nasu kukan.
   Cikin sar'kewar murya daddy ya ce, yau zan faďa muku wani abu game da kanku ammafa kuyi ha'kuri ba komaine zan iya warware mukuba,, maganata tafi 'karfi akanka kai Mahmud, dan adalilinkane komai zai fito fili,, cikin tsoro ya Mahmud yake kallon daddy, daddy ya jin jina kai, eh akankane, kwanaki likita yayimin bayani akanka da matarka saikuma abinda yadace kayi, amma sainayi burus dakai inga kozakazo min da zancen kaima, to amma sai bakayi maganarba har gashi tsawon shekara biyu,, shekaran jiya waccan matarka tazomin akiďeme takuma sanar dani itama batasan komai gameda shawarar da likita yabakaba sai aranar dataji a wajen doctor, taro'keni akan nasaka ka 'kara aure.
   To zan iya cewa fađuwace tazo dai2 da zama, damancan kanada matar aure ahannu, abinda yasa ba'a baka itaba saboda bata isa aureba sai yanzu..... arikice dukkan ahalin gidan suke kallonsa musammanma ya mahmud.
   Daddy yaďora da faďin matarka tana nan gidan!!!,  kuma munyanke hukunci baka ita a 'karshen wannan shekarar,, bazan faďi kowaceceba saboda banason tashiga ruďani tun yanzu dan zataji wani SABON AL'AMAREE daban....... yana kaiwa nan yami'ke da sauri ya haye samansa yana hawaye.....................tab ďijan nifa nagaza gane wanan lamari,, wane irin SABON AL'AMAREE ne yake shirin faruwa a gidananne???????, to komadai miye muna biye daku su daddy........................


luv u oll my fan's
2017
[13/02 16:21] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE


BILKEESA IBRAHEEM
   {♡bilyn Abdul♡}

        
                      20                                        
.........cikin tsoro deena da Nurr suke kallon juna, tabbas akan ďaya daga cikinsu ake magana, kenan akwai wadda ba 'yar gidanba acikinsu, hawayene suka shiga silalomusu akumatu, lallai suna cikin ruďani,, wannan wane irin SABON AL'AMAREE ne mara daďin ji??????.
   To a 6angarensu ya Mahmud ma hakane, tunda daddy yabar gurin zufa ta wanke dukkan sassan jikinsa, jiyake kansa yana sara masa tamkar zai rabe gida biyu yadafe kai yana fidda numfashi da'kyar wanan wane irin SABON AL'AMAREE ne mai rikitarwa dasaka ruďani, ahankali mama ta mi'ke ta bar gurin tana kwararar da hawaye hakama mami kuka take, ganin haka sai suma sauran yaran suka shiga nasu raira kukan, amma babu mai lallashi.
    Sunkai tsawon awa ďaya suna abu ďaya daga baya ya mahmud yamike yana tangaďi yafice, shima ya fahad baya yatake masa, ahankali kowa ya fice amma banda deena da Nurr dasuka shiga cikin ruďani, daga 'karshema saisuka zame suka kwanta a falon suna cigaba da kuka mai bantausayi, (gsky koni na tausaya musu, saboda basusan wacece acikinsuba????, to ALLAH yabaku ha'urin jurewa)

Har tsawon kwana biyu gidan bai dawo dai2ba kowa kagani yana cikin wani yanayi lallai SABON AL'AMAREE ya shigo wanan gida.
    Ya mahmud kuwa aiko office baya fita, saidama yayi ďan zazza6i saboda damuwa, daga baya kuma saiya dake,, kunsan maza akwai juriya.
   Tundaga ranar babu wanda yasake tada maganar nan, ahankali kowa yafara komawa kan harkokinsa, rayuwar tafara komawa dai2, amma a 6angaten Nurr da deena bahaka baneba,, sukam babu abinda yacanja musu saima 'kara ta6ar6arewa da al'amura suke musu, dan danan suka shiga rama mara 'kyau, garama deena tanada 'yar 'kiba amma Nurr sai ahankali.
   Nurr farace tas amma zamu iya kiranta gajera gsky, gata 'yar fit dan batada jiki ko kaďan idan kaganta zaka iya cewa batakai shekara sha bakwai ba saboda rashin girman jiki,, tanada idanuwa dai2 wadaida suba 'kananaba kuma ba manyaba, tanada ďan gashinta dai2 musali amma bai cika tsawoba,, tabbas Nurr 'kya'kyawace sosai dan duk namiji mai lafiya yaganta saiya 'kyasa, idan tayi dariya kumatunta sai sun lotsa akwai ilimi saidai akwai rashinji.
    Deenama dai farace zan iya cemuku tana matu'ar kama da Nurr saidai ita tafita tsayi da 'kiba, ita idan kagantama akace kabata shekaru to ashirin zakace amma shekararta sha bakwai itama harda wata biyar asama dan tagirmisu Nurr da Saiff.
    Ko tsakar guda basa fitowa abincima sai an tilasta musu sukecinshi, idan kazo gidan saikace babukowa saboda sarakan hidima sunyi laushi suna cikin yanayin SABON AL'AMAREE, dahaka komai yayta tafiya rana tana gudu bikin su Nurr yana isowa, sukuma suna 'kara shiga ruďani, dan har yanzu basusan wacece matar ya mahmud ba,, shiko ko gidan yazo baya nemansu kwata2, saidai nakula shifa kamar yasan matar tashi yana basarwane kawai kokuwa baisaniba oho dai.
    Ana cikin haka sa'ko ya isowa family ďin Sardauna Alh musbahu yarasu,, kunsan abinda yabani mamaki kuwa???, amsar itace babu wanda yadamu ko jimamin rasuwarsa, kai bammaji wanda ya ce, "ALLAH yaji'kansaba,, toko miyayi musu dazafi hakane?????.

NOVEMBER/25/2016.
    A yawune daddy yadawo daga 'kasar London, cikin murna su deena suka taroshi dan sunďan fara sakin jikinsu yanzu,, ayayinda aka shigo da akwatina gidan sai tsoro da fargaba yashihesu tabbas akwatinan aurensune dan yanzu ance suduka za ayima auren zasu cigaba da karatunsu agidan mijinsu,, babu wanda yatambayi daddy akwatinan waye dan kowa yasan konasu waye.
   Da daddare ya Mahmud ya amsa kiran daddy bayan sun gaisa daddy ya nuna masa akwatina, gasunan na matarka shidda na matar Suraj shida, saika za6i ďaya tunda kaine babba, ya mahmud ya langwa6e kai yana faďin daddy duk wanda aka bata ai yayi ALLAH yasaka da alkairi ya ji'kan mahaifa.
  To amin shikenan,, amma daka duba kayan ko kana bu'katar 'kara wani abun??, kai ya girgiza daddy koban ganiba nasan sunyi, idanma tana bu'katar wani abu, idan taje gidan saina saya mata,, okey shikenan,, yanzu yamaganar ďaurin auren ďayar 'kanwar taka, dan komai kasandai kaine zakayi amatsayinka na babba, wanan shine zaisa su ji'kanka wataran, kuma ko babu ranka zasu tallafi 'ya'yanku,, shiyyasa muke ďora muku nauyinsu tun yanzu.
   Saida ya sosa 'keya sanan ya ce, "babu damuwa daddy insha ALLAHU komai ashirye yake rana kawai mike jira,, daddy ya ji jina kai yana murmushi to ALLAH dai yakaimu darai da lafiya,, amin ya Mahmud yafaďa yana mi'keawa, daddy bari nawuce gida naga rana tafara yi.
   To saida safe agaida min da bilkeesun, to daddy zataji,, harya fice daddy na binsa da kallo afili ya furta Mahmud yaron kirki kenan, kaima ALLAH yabaka masu yimaka addu'a kaji,, kullum addu'ata ALLAH ya nuna mini 'ya'yanka a duniya, tabbas zanyi farincikin samun jika daga tsatsaonka.
   Yana sakkowa yaci karo da deena da Nurr suna zagaye falon, dagasu sai best da zani saboda yanayin zafin garin,, deena ta ce, "ALLAH kinga Nurr kibani banason wula'kanci, Nurr ta ta6e baki karkiso wula'kancin mana aibani nace ki ajiyeba ko???, kumani ita zan saka wlhy.
   Ya Mahmud yay gyaran murya da hanzari suka juyo suna kallonshi gaba ďaya suka shiga ruďani, ya bisu da kallo fuska a ďaure, agurin suka dur 'kushe suna gaisheshi, batarda ya amsaba ya ce, "waiku bazakuyi hankaliba ko??, ya wurgama Nurr harara uban miye kika ďaukar mata, Nurr ta buntsuro baki gaba yaya rigacefa kuma saida taga na ďauka zan saka sanan ta ce, "itama shi zata saka,, hannu ya 'mi'ka mata batareda yace komai ba, tasan miyake nufi dan haka ta mi'ka masa rigar kawai, kar6a yayi yay ficewarsa batareda yatanka musuba.
   Suka bishi da kallo kowa tana 'kyafta idanu................... 



luv u oll my fan's
 2017
[13/02 18:46] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE



BILKEESA IBRAHEEM
       {♡bilyn Abdul♡}

         
                            
      21                                         
........Nurr ta harari deena aikinga kinja ya kwace ko??, sai kowa ya huta aii,, deena ta tuntsure da dariya aigarama daya kwace ni wlhy banji haushiba,, tsaki Nurr taja tawuce ďaki tana faďin matsalarkice kuma wannan,, hhhhhh 'yammata kodai matsalarmu deena tabi Nurr tana dariya.
    Shiko koda yafita mota yashige, kai tsaye gidansa yanufa abinsa, yay fakin a yalwatacciyar harabar gidan, ya fito zuwa cikin gidan hannunsa ri'ke da rigarsu Nurr wadda ya kwave,, babu kowa a falon dan haka kai tsaye yanufi saman sa, dirowa ya buďe ya jefa rigar ciki, sanan yacire kayan jikinshi yashiga wanka,, sai asannan aunty bily tashigo, ganin yashiga wanka sai kawai tashiga tattare kayansa daya zube akan gado, inda yadace ta ajiyesu sanan tafito masa da farar jallabiya tas, tananan zaune yafito daga bayi saidai fuskarsa babu walwala,, tasan halin kayanta dan hakama bata cika damuwa da ďaurewar fuskarsaba, dan hakan ajininsa yake, ta ce, "sannu da zuwa my handsome,, yauwa sannuki yafaďa shima yana goge jikinsa da 'karamin tawul dake hannunsa,, ta 'karaso gareshi hannunta ri'keda man shafawa, tawul ďin ta kar6a ta 'karasa goge masa jikin, sannan ta shafa masa man, ya zura jallabiyar data fiddo masa suka sakko falon 'kasa.
   Saman doguwar kujera ya kwanta tabishi da kallo tana faďin yaya abincinfa??, yaďan yatsine fuska saika ce mace, bayanzu zanciba yafaďa yana gyara kwanciyarsa, okey tafaďa tana zama kujerar dake kallonsa.
   Ta ce, "yauwa na manta ya mujaheed yazo nemanka ďazu bayan kafita.
  Okey miya cemiki??.
  Baice komaiba ya ce da daddare zai dawo.
      Okey ALLAH yakaimu.
  Amin tafaďa tana jawo wayarta,, garama tayi catin da 'yan uwa dan idan bai gadamaba saisuyi zaman awa ďaya batareda ya tankaba, sabodashi mutumne bamai yawan surutuba, ilai kuwa remote ya ďauka yafara canja tashoshi, idonsa ya tsaya akan tashar MAX TV, suna wani American film mai 'kyau.
   Haka sukayita zaman kurame har la'asar daga nan yatafi masallaci domin sauke farali.
  Itama ďaki tanufa tayi tata, tana zaune tana lazumi taji 'kiriniyar Abdul, tashafa addu'ar sanan tafito ilaiko shine shida ya Mahmud 'kila gidan yaje ya ďakkoshi dan idan ba'a kawoshiba saiyaje dakansa ya đakkoshi,, dagudu yazo ya rungume aunty bily yana kiran momy oyoyo,, ta ďagashi sama tana faďin my boy yaushe kazone??
   Cikin muryarsa dabata fita ya ce, "yanju dad ya tacconi.
  Ayya ykk my boy??.
    Yaron yay 'yar dariyarsa mai 'kayatarwa ya ce, "lfy momyna.
Yauwa yaron dad tafaďa tana saukeshi akan cinyar ya Mahmud,, abinci tazo ta shirya masa akan tebir ďin dake tsakkiyar falon,, yanata wasa da Abdul suna dariya kamar bashiba,, dama idan kanaso kaga yana tuntsura dariya to ka kawo masa yaro.
   Tare sukaci abincin yanaci yana bashi harsuka gama sukaci gaba da wasa shima yana biye masa kamar yaron lol.

Bikifa yazo anata shirye2n hidima kowa kagani yana cikin farin cikin,, duk wata al'ada dama sunayinta ne kafin ďaurin aure, dan haka akayi kamu yau,, saidai amaren duk suna cikin damuwa kowa yana fargabar mijin dazai tarrar musamman ma wadda ta kasance matar ya Mahmud, washe gari akayi 'qauyawa, saikuma Arabiyan day, komai ya 'kayatar amare sunata shan 'kamshi da gyara, sunyi 'kyau harsun gaji,, yaune akayi Loncin amma ya mahmud bai jeba ya Suraj ne kawai yaje, saiya shiga tsakkiyarsu sukuma suna gefenshi na haggu da dama,, hakama wajen dina ya mahmud baijeba zama sukayi kamar a wajen loncin, washe gari aka tashi da shirin ďaurin aure.
    Saidai abin haushi har aka ďaura my Abdul bai barni na fitaba, wai yau agida zai wuni, gsky naji haushi sosai naso ace naje naji wacece amaryar ya mahmud tunda banda ita za'a ďaura dan tuni ita da aurenta akanta,, yazanyi dole na ha'kura da ďakko muku rahoto sai yamma daya fita ya ce, "naje.
   Ammafa badan kuba dabazanjeba lol.

Sanda na iso su Nurr suna harabar gidan sunci kwalliya dawani ďan ubasu less skyblue doguwar rigace  an naďe musu kai da darkblue ďin ďankwali, sarkar wuyansu ma darkblue ce ta zallar duwatsu atsakkiya an ratsa skyblue ďin bit, hannunsu yasha bangus da zobuna masu matu'kar 'kyau fuskarnan tasha kwalliya irin wanda amaren zamani suke yayi, kai masu karatu abin sai wanda yagani dai,, ga wani ďan ubansu takalmi sun kwama mai shegen tsini,,  'yan uwa sai ďaukar hutuna suke dasu,, ana cikin ďaukar hoto saiga ya muhsin ri'keda ya mahmud wow!! Mutumin nakufa ya kashe kala wlhy,, shima yaci ado cikin wata farar shadda mai shegen mai'ko da 'kyawu tasha sirfani na alfarma ya murza ba'kar hula akansa mai suna (president) hannunsa ďaure da ba'kin agogo mai 'kyau hakama 'kafarsa,, tunda yashigo su Nurr yake kallo dansunyi matu'kar burgeshi yaran sun 'kayatu da kyawu.......... ya Sultan ya 'katse masa tunani da faďin ango shiga a ďauka dakai dama tun ďazu kai muke nema, ďan murmushi ya Mahmud yayi ya 'karasa wajen 'kannen nasa dake tsaye ya Suraj yana gefensu shima yatsaya aďayan gefen suka sakasu tsakkiya, bayan anďaukesu saikuma aka ďaukesu su biyu, shida deena dakuma shida Nurr daganan dai akaita ďaukar hotunan,, nima danaga ba'ada niyyar kirana saina lalla6a tabayan aunty bily naďan le'ko da kaina, lol, itama tayi matu'kar 'kayatuwa cikin kwalliya ta alfarma.
    Inama duk wadda za'yima kishiya taďau 'kya'ky'kyawan hali irinna aunty bily,, tabbas data more, da mijinta ya girmamata yakumayi alfahari da'ita,, ALLAH yasa mudace amin.
      Bayan angama hidimar ďaukar hoto akacigaba da shagali har zuwa dare,, 'karfe takwas aka shirya amare tsaf cikin jar lifaya sai zabga 'kamshi sukeyi maidaďi, gakuma uban kuka suna shar6a tunda suke basu ta6a rabuwa da junaba kodana wuni ďayane,, tunda suka girma sukai wayau suna tare har yau da aure zai rabasu,, sau'kinsuma suna kusada juna sosai suke,, gefe guda kuma kowa tana fargabar kasancewar ta matar ya Mahmud,, falon daddy aka kaisu inda dukkan iyaye maza da mata suke zaune, dayake falon babbane kuma duk yarinyar daza'a aurar sai ammata wanan taron dagi wajen faďa da nasiha,, tunda aka farayimusu faďan suke kuka kamar ransu zai fita,, wasuma dayawa a falon kuka sukeyi saboda tuna abubuwa masu yawa abaya, hakadai akai musu nasiha sanna aka dan'kasu ga iyaye mata domin kaisu gidajensu..
     Da'aka kaisu wajen mama kasa magana tayi saboda kuka,  dole akayi mata uzuri aka fito dasu zuwa ďakin mami,, itadai taďan yimusu kaďan itama kuka yaci 'karfinta, daganan aka fito dasu sai mota sunata kuka dafaďin sufa bazasujeba sun fasa abarsu taredasu mama zasu zauna anan basa son auren,, haka sukaita sambatu da kuka mai ban tausayi bayanda za'ayi afasa dan haka aka dannasu mota sai gidan mazajensu dake nan cikin anguwar, (nima bari naďan matse hawayen)

Kowa gidanta aka kaita bayan wasu 'yan muntuna gidajen sukayi tsit, garama wadda aka kaima ya Mahmud an haďasune da aunty bily,, amma dukda haka gidan tsit kamar babu kowa.
    Daga deena har Nurr sun kasa motsi daga gadon da'a ajiyeshi,, kowacce tana fargabar abinda zai biyo baya, shiyyasa sukayi zaune akan gadajen nasu suna cigaba da kuka..
    Ku kasance dani danjin wadda zata kasance agidan ya Mahmuddddddd!!!!!!!!!!!!!..................



luv u oll my fan's 
2017
[16/02 12:49] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE


BILKEESA IBRAHEEM
      {♡Bilyn Abdul♡}

    
       22                   
                                               
........A hanakali aka turo 'kofar aka shigo batareda yayi ko sallamaba, tana lilli6e cikin lafayar tana rusar kuka, jigina yayi da 'kofar ya harďe hannayensa a 'kirji idanunsa 'kyam akanta, zuciyarsa cike da fargaba, bayason hankalin yarinyar nan yatashi, yakuma san tabbas tana ganinsa komai zai dagule, zataga SABON AL'AMAREE mai ban mamaki.
   Tunďazu taji motsin buďe 'kofa amma firgici da ruďani sun hanata ďagowa jikinta sai rawa yakeyi, gabanta kam dukan tara2 yakeyi bama uku2ba, sunkai minti talatin ahaka babu wanda yayi wani yin'kuri ga ďan uwansa, harya buďe 'kofar zai fice saiya tuna dawani furici na daddy, ya fitar da huci mai zafi daga bakinsa tareda cije le6ensa na 'kasa, ahankali yataka zuwa bakin gadon, yazauna kamar mai zama akan wuta, nanma shiru yayi baiyi maganaba, itako amarya wani sabon ruďani tashiga danjin angon nata zaune kusada ita, sai hawaye ke zurara akuma tunta.
    Ahankali ya furta kicire wanan abun kisha iska mana.........arikice ta ďago danjin muryar ya Mahmud, jadabaya tafarayi tana girgiza kai ga hawaye share2, innalillah wa inna ilaihirraji'un kawai take ambata, kafin ya farga ta sassan'kame agurin, da sauri ya tallafota dan tana niyyar fađuwa daga gado,, girgizata yafarayi yana kiran Nurr! Nurr!! Nurr!!!, ina Nurr tayi nisa batajin kira, da sauri yaciro wayarsa daga aljihu yafara kiran bily, minti biyar ta'iso ďakin aruďe, ganin Nurr a sassan'kame ajikinsa saita 'kara firgicewa tashiga tambayar lafiya.
        Bai bata amsaba ya ce, "ďakkomin alkur'ani, da hanzari takoma ďaki ta ďakko masa, ya kwantar da Nirr saman gado, ya kar6i alkur'anin yafara karatu, fisge2 tafara ya mi'kawa aunty bily alkur'anin cigaba da karatun tayi shikuma yari'ke Nurr.
      Tafara magana cikin wata irin muraya, kudaina 'konamu munzo tayata murmane da samun gwarzon namiji irinka, lallai tayi dace dasamun miji nagari, ya Mahmud yay tsaki to haka ake taya murna saikuzo ku sassan'kame yarinya, waiku baza kubar jikinta bane, shuru sukayi basu bashi amsaba, ya mi'ka hannu ya kar6i alkur'anin zai cigaba da karatun, da sauri tayi atshawa sun fita kenan.
    Ya mahmud yay tsaki yana fađin daku tsaya mana, koda Nurra tadawo saita ganta ajikin ya Mahmud da sauri tatashi taje ta 'kan'kame aunty bily tana kuka.
    Aunty dan ALLAH ki rufa min asiri nashiga uku ni Maryam dan ALLAH kice mafarki nakeyi ba gsk baneba, ya za'ayi na auri ya mahmud bayan duk mamace ta haifemu, dan ALLAH kigaya min gsky ta 'kara fashewa da kuka mai ban tausayi.
   Itama aunty bily kuka takeyi yayin da ya mahmud ke zaune kamar gunki gaba ďaya kansa acunkushe yake, inama su daddy sun ha'kura sun binne wanan sirrin??, afirgice yadawo da hankalinsa akan Nurr danjin ta kwalla wata 'kara mai firgitarwa, jikinta sai rawa yakeyi, aunty bily nari'ke da ita tana kuka, ya Mahmud ya 'kar6eta yana cigaba damata addu'oi, ahanlai zufa tafara keto mata adukkan sassan jikinta, sai kuma jikinta yay lakwas, aunty bily ta fashe da kuka tana faďin yaya ta mutu mun shiga uku.
   Bai cemata komaiba danshima nasa hankalin atashe yake yama rasa wane mataki yakamata yaďauka, dabara ta faďoma aunty bily ta tashi tafita da hanzari, waya ta ďauka takira ya fahad, cikin ruďewa ta ce, "yazo.
    Babu 6ata lokaci ya iso gidan dama shima hankalinsa atashe yake, yasan dole Nurr tashiga ruďani da SABON AL'AMAREEn dazata gani, shine yay kokarin kiran likita, lokaci kalilan doctor ya iso, har sanan Nurr tana jikin Ya Mahmud a sume, babu 6ata lokaci yasaka mata abinda zai taimaka mata wajen jawo numfashi, sanan yay mata wata allura ya li'ka mata 'karin ruwa.
   Ya Mahmud ya ce, "yaya dai?? Doctor!!, doctor ashir ya ce, "karka damu mubata awa ďaya insha ALLAHU zata dawo daidai, tashiga ruďanine ma yanzu shiyya kawo bugawar zuciyarta da 'karfin gsk amma komai zai dai2ta insha ALLAHU.
     Haka sukayi zaune jigum2 saikace gidan mutuwa, awa ďaya tana cika Nurr tafara numfashi sama2, doctor yasake yimata wata allurar, ahankali kuma sai numfashinta yafara dai2ta, barci yay awon gaba da'ita, doctor ya ce, "Alhmdllh yanzu komai normal tana barcine, zuwa lokacin da ruwan ya 'kare saika cire mata, nibari na wuce saida safenku.
  To ALLAH yakaimu doctor mungodefa sosai sannu da 'ko'kari, saida suka rakashi yashiga mota daganan ya fahad shima yashige gidansa, ya Mahmud kuma yadawo.
    Ďakinsa ya wuce yay shirin barci sanan ya sakko 'kasa ďakin Nurr, aunty bily tana zaune a bakin gadon, yana shigowa ta mi'ke tsaye, ya bita da kallo yana faďin ina zuwa kuma??, taďan marairaice fuska zanje na kwanta mana my handsome tunda naga itama tasamu barci.
   Yaďan matso kusada ita haba bilyna ince anan kema zaki kwana??, ido ta zaro waje, kai idan nace zan kwana saika yarda???.
         Cikin mamaki yake kallonta, miyasa zan'ki yarda to??,  'yar dariya tayi tana tafiya saboda bai daceba mana ta 'kare maganar da ficewa daga ďakin.
      Murmushi kawai yayi yana girgiza kai, bayan wasu 'yan mintina yabi bayanta, yata6a kofarta yaji akulle gam, dawowa yayi ďakin Nurr, tsaye yayi yana bin Nurr da kallo, duk ta 'kara ramewa dama gata kamar sillen kara, idanunta duk sunshige ciki, yaďan share zufar data taru mata agoshi, yaje ya'karama AC 'karfi sannan yadawo gefen gadon ya kwanta (na ce, "asuba tagari ya mahmud).

WASHR GARI.
       da asuba yatashi yatafi masallaci, bai tadata ba itakam, dama tunda yacire mata 'karin ruwan tasake canja salon kwanciyarta alamun barcin yana mata daďi kenan, koda yadawo daga sallah bai koma ďakintaba saiya wuce ďakinsa.
    Sai wajen 7:12am Nurr ta farka, ta tashi tayi wanka sanan tayi sallar asuba, tana idarwa ta shirya cikin siket da riga ta zura dogon hijjabi, saida tafara le'kowa taga falon babu kowa sanan tafito cikin sanďa tabar gidan sai gidan daddy, koda ta isa canma duk suna ďaki suna barci, kai tsaye ďakinsu nada tawuce takwanta, barci ne yakwasheta dama bai ishetaba ta tashi.
               Aunty bily tagama haďa breakfast tsaf, laure mai aikinta ta gyara gidan aka baďeshi da 'kamshi, ďakin ya Mahmud ta nufa da nufin gyarawa tayi turus dan ganinsa kwance yana barci, badai mutiminnan anan yakwanaba??, tafađa tana 'karasawa  bakin gadon, tasan halinsa sarai bayason katasheshi da hayaniya, dan haka saita ďan ja hancinsa ya motsa kaďan, ta sake ja sannan ya buďe ido yana kallonta 'kasa2, agogo ta nuna masa, yatashi zaune yana mi'ka sanan ya ce, "wai lokaci har yakai haka??, ehmana yakai, katashi kayi wanka.
    'Kafafunsa yazuro 'kasa tareda sakkowa, haryakai 'kofar bayi aunty bily ta ce, "wai anan ka kwanane??, juyowa yayi yana kallonta baice mata komaiba yashigewarsa bayi, kai ta girgiza kawai itakam batasan ranarda ya Mahmud zai fara baka amsoshin dukkan tanbayoyo yin da kamasaba, ko magana dakayi masaba, gadon tafara gyarawa, daganan tagyara ďakin tsaf, ta ajiye masa kayan dazaisa tafice domin tada Nurr itama.
    Ďakin ta tura tashiga saidai babu wakowa aďakin, azatonta bayi tashiga dan haka tafara kakka6e mata gadon, hartagama gyaran ďakin bata fitoba, bakin bayi taje tana faďin Nurr wai wanka kikeyine???, shiru babu amasa, ta 'kara kiran Nurr! Nurr!!!, shiru babu amasa da sauri ta tura 'kofar bayin wayam babu kowa, da gudu tafita sai ďakin ya Mahmud, yana tsaye gaban madubi yana gyara kwalar rigarsa, aunty bily ta ce, "ya Mahmud Nurr fa bata cikin gidannan, bai fasa abinda yajeyiba, idinsa nakan madubi ya ce, "kamarya bata cikin gidannan??, ba tana ďakinta ba??.
      A'a gsky babu kowa đakinta, nakuma duba duk inda yadace amma bata nan, sai asannan ya juyo to ina tashiga??, ina zan sani yaya kasan Nurr zata iya fitafa sarai........kafin ta 'karasa ya fito, itama baya ta take masa, lungu da sa'ko na gidan suka shiga dubawa amma babu Nurr babu alamarta, hankali tashe ya Mahmud ya ce, "ina yarinyar nan tashiga ne??, aunty bily ta ce, "kodai gidan daddy zakaje kotaje can.
    Okey ina zuwa yafaďa yana fita..........................



Luv u oll my fan's
2017
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *