check your best novels here

Saturday 11 March 2017

SABON AL'AMAREE 23/26

[16/02 16:55] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE


BILKEESA IBRAHEEM
      {♡bilyn Abdul♡}


23
   

..........Kai tsaye gidan daddy yanufa, tun a gate yafara karo dasu Mubarak zasu tafi wajen aiki, suka gaisheshi, bai amsaba ya ce, "musu Nurr tazo gidannan??.
    Saida suka kalli juna sanan suka dawo da kallonsu gareshi, mustapha ya ce, "ya mahmud Nurr kuma??, mizai kawo Nurr nan gidan??.
    Ya haďe fuska, ya ina tambayarku kuma kuna tambayata??, sunsan halinsa sarai dan haka sukace wlhy basu saniba saidai sukoma ciki su tambaya??, baibi takansuba yayi gaba, suma baya suka take masa, falon babu kowa sai masu aiki suna gyarawa, suka dur'kusa suna gaida ya mahmud sau ďaya ya amsa ya ce, "Nurr tashigo gidannan??, A'a suka faďa kansu a'kasa.
    Mama tafito daga ďaki da sauri danjin ankira Nurr, ya Mahmud ya rissina yana gaisheta, ta amsa kai agefe, ta ďora da tambayar lafiya kaikuma da sassafenan???, ya Mahmud yaďan shafa kansa mama nazo neman Nurr ne.
   Nurr kuma??, bangane kazo neman Nurr ba??, Nurr ďin ba'a gidanka ta kwanaba???.
    Acan ta kwana bamatada lafiya, dan saida doctor yazo yabata taimako, amma da safenan mun nemeta mun rasa acikin gidan, nama zata kotazo nan ne shiyyasa nazo???.
   Daddy da mami ma suka sakko daga sama dayake yau itace dashi,, neman Nurr aka shigayi acikin gidan amma sama da 'kasa babu ita, saidaga baya Saiff ya ce, "bari na duba ďakinsu kotanacan.
    Yana shiga yaganta kwance tana barci, da 'karfi ya ce, "ya Mahmud gata anan tana barci, hakan yayi dai2 da farkawar Nurr, suma suka 'karaso ďakin, da gudu Nurr taje ta rungume mama tana kuka, mama tashiga lallashinta tana shafa kanta, daganan falon daddy suka koma, kowa yasamu muhalli ya zauna.
       Falon yayi shiru bakajin komai sai shashshekar kukan Nurr, daddy yagyaran murya tareda kiran Nurr!!, Nurr taďago kai tana kallon daddy batareda ta amsaba, daddy ya ce, "zonan!!.
     jiki a sanyaye tatashi taje gaban daddy ta dur'kusa, hannunta daddy yakamo ya matsoda ita sosai kusadashi.
    Cikin taushin murya ya ce, "haba ďiyata Nurr kukan ya isa haka ko??, kinga share hawayenki.
   Babu musu ta share hawayenta"". 
  Daddy ya ce, "yauwa ďiyar albarka, yanzu in tanbayeki mana??,, kai ta jinjina batareda tayi maganaba, saboda datayi magana kukane zai taho mata.
   Yauwa miyasa kika baro gidan mijinki da sassafennan??.
   Jajayen idanuwanta taďago tana kallon daddy cikin raunin murya ta ce, "daddy bazan iya zamaba ina kallon ya Mahmud amatsayin wanda muka fito ciki ďaya, har yanzu inaji ajikina mama ce mahaigiyata, dan haka ALLAH daddy bazan iyaba, tafaďa cikin raunin murya, inko kunaso na zauna dashi to sai kunmin bayani akan iyayena, miyasa basa taredani??, miyasa suka barni??, kuma yanzu suna inane??, sun rasune kokuwa suna raye???.
    Ďan murmushin takaici daddy yayi, yashafa kan Nurr, karki damu ďiyata nanbada daďewaba za'a amsa miki dukkan tanbayoyinki, kije kizauna gidan mijinki kamar yanda 'yar uwarki deena ta zauna,, yau zansanar da family bu'katarki, insha ALLAHU zuwa gobe idan ALLAH yakaimu zakiji ranar damuka tsaida dominjin amsoshin tanbayoyinki kinji..??
   To daddy zanyi kamar yanda kace insha ALLAHU.
   Yauwa Nurri na ALLAH yayi miki al'barka kinji, yanzu tashi kibi mijinki ku koma gida.
   To, tafaďa tana mi'kewa, ya Mahmud ma yami'ke suka fice, yayinda su mama suka bisu da kallo,, mamakam kuka takeyi.
   
Koda suka fita babu wanda ya tankama wani, Nurr tana gaba ya Mahmud yana biye da ita, tafiya kaďan takaisu cikin gidan, da sauri aunty bily tazo ta rungume Nurr tana faďin haba Nurr ina kika tafi da sassafen nan?, kin tayar mana da hankali gsky.
    Nurr ta share hawaye ta ce, "kuyi ha'kuri aunty bazan sakeba.
      yauwa Nurr karki sake kinji, ta ďagota tana share mata hawaye, to kukan ya isa haka kinji zomuje kici abinci kinga bakida cikakkiyar lafiya.
  Duk abinda sukeyi ya Mahmud yana zaune a dani yana hidimar haďama kansa breakfast, suma zuwa sukayi suka zauna aunty bily ta kar6a ta 'karasa haďama ya Mahmud abincinsa, tagama tazubawa Nurr nata sanan tazuba itama.
     Shikam ya Mahmud sai dannama cikinsa abinci yakeyi babu ruwansa, hakama aunty bily, amma Nurr sai juya cokalo takeyi acikin kofin shayi har yanzu ko lauma ďaya batakai bakintaba, aunty bily taďan ta6ata haba Nurr kici abincin mana.
   ALLAH aunty banajin cin komai,,.
     aiko bazai yuwu kizauna da yunwaba, kidaure ko kaďan kici kinji, to aunty Nurr tafaďa tana kur6ar shayin.
   Ya mahmud yana jinsu amma bai tanka ba, yadai ďago ido ya kallesu har suka haďa ido da Nurr, tai saurin yin 'kasa da idanunta.
   Aunty bily tayita lalla6a Nurr harta đanci abincin sanan ta 'kyaleta, suna gamawa Nurr takoma ďakinta ta kwanta, shikam ficewa ma yayi daga gidan, suka bar aunty bily ita kaďai afalon.

DEENA.
      a6angaren deena kuwa, tunda taga ya Suraj amatsayin mijinta sai tausayin Nurr yakamata tasan Nurr tanada rauni, gashi kuma rayuwar ta tazo da SABON AL'AMAREE lallai tana tausayin wanan baiwa, da'kyar ya Suraj ya lallasheta tayi shiru daga kukan tausayin datakeyi a kan Nurr.
     Shikam bai ďaga mata 'kafaba aranar ya more sadakinsa, saidai tasha kuka sosai, daga baya yayta lallashin matarsa da saka mata albarka.

Sai 'karfe ďaya ya mahmud yadawo gidan lokacin Nurr ta tashi tayi wanka dukda bawata kwalliya tayiba amma tayi 'kyau, wando da riga tasaka rigar yar mitsila sunyi mugun fitar mata da surarta, tariga tasaba da saka 'kananun kaya sosai, dan haka idan basu tasakaba batajin daďi, gashi garin kuma akwai zafi, duk yawancin kayansu 'kanane itada deena.
    Tun ďazu tanajin motsin da aunty bily takeyi a babban falo amma takasa fita, har yanzu batajin daďin jikinta dan haka tayi zamanta aďaki, batasan inda wayarta takeba data kira deena sun gaisa, kwana ďaya kacal harta fara kewarta, ALLAH sarki 'yar uwa deena muyi faďa mu shirya kullum sai munyi ashe wata rana aure zai rabamu munaji muna gani, ta goge hawayen dasuka sulalo mata.
     Ahankali ya turo 'kofar yashigo da sallama, Nurr ta amsa can "kasan ma'koshinta, ya 'karaso tsakar ďakin idonsa akanta, tashi tayi zaune da sauri tana rarumar gyale danta lullu6e jikinta,  dan bata manta da dukan dayayi mata ranarba akan saka 'kananun kayaba, cikin rawar murya take gaisheshi, bai amsaba saima zama dayayi a bakin gado, ya ce, "yajikinki??.
    Da sau'ki ta amsa kai a 'kasa, leda ya mi'ko mata, hannu biyu tasaka ta 'kar6a, ki ajiye anjima zanyi miki bayani yafaďa yana mi'kewa.
    "Ta ce, "ALLAH yakaimu.
   Amin yafaďa kan la66ansa ya fice.
     Binsa tayi da kallo a zuciyarta ta ce, "lallai aunty bily tana fama da wanan ďan bala'in, wanda babu abinda ya iya arayuwarsa sai muguntar tsiya, ledar tabuďe ta le'ka saitaga magunguna, baki ta ta6e ta ce, "kona miye??, oho masa.
     Ma'ajiya maikyau ta ajiye tadawo saman kujerar tayi kwanciyarta.
    Bata fitaba saida aunty bily tazo takirata dansuci abinci, after dress ta ďora akan kayanta sanan tafice,, koda suka gama cin abinci saita dawo ďaki abinta tabarosu afalon suna hira, konace aunty bily tana hira danshi sarakin sai'ayi magana sama da ashirin baifi yabada amasar biyu ba..................


luv u oll my fan's
©2017
[20/02 17:09] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE




BILKEESA IBRAHEEM
      {♡bilyn Abdul♡}

Assalamu alaikum 
  'Yan uwa kuyi ha'kuri da rashin posting ďina, murace tayimin kamun kazar kuku,, dan haka ina jiran kaji masu yaji awajanku, gashin gida, ga wanna kuďanyi manage kafin gobe idan ALLAH yakaimu, ko anjima I dan nasamu dama.
Luv u oll



24
   


.........Tana zaune abakin gado bayan ta kammala shirin barci, sotake ta kwanta amma tanajin tsoro, bata saba kwana ita kaďaiba, to kodai ďakin aunty bily zatane saisu kwana??, taďanja tsaki kai amma saitaga kamar bai daceba, to amma idan ba haka tayiba aibatada wata mafita bayan wanan, ta mi'ke tsaye tana gyara ďaurin ďankwalinta, itakam wlhy can zata tasandai babu mai cemata dammi, fitilar ďakin takashe tafito, 'akofar ďaki sukai karo ita tana 'ko'karin fita shikuma yana 'ko'karin shigowa, abisa tsaushayi 'kafarta tabigi 'kofa zafi yasa ta tuzguďe zata faďi, da sauri ya ri'ko 'kugunta zuwa jikinsa, sorry yafaďa ata'kaice.
    Ajiyar zuciya tasaki tareda zame jikinta daga nasa, baibi takantaba ya tura 'kofar ya shige ďakin.
   Nurr ta ce, "yau naga 'karfin hali mai ďaki tana fita kai kana tura kai ciki, babu yanda zatayi dole tabishi zuwa ciki, a bakin gado ta tarar dashi zaune, jiki asanayaye ta 'karasa saman kujera ta zauna.
  "To da ina zakije???.".
  " kai taďago taďan kalleshi, saikuma tamaida kasa dan ganin ya kafeta da idanuwansa, cikin rawar murya ta ce, "wajen aunty bilkee zanje.
   Baki yaďan ta6e ya ce, "yanzu a darennan??.
   Shiru tayi bata bashi amsaba, dan batasan mizata faďa masaba..
    Bani ledar ďazu yafaďa yana sauka saman carpet ďin dake gaban gadon, mi'kewa tayi ta ďako masa, har zata koma saman kujera ta zauna, sai ya ce, "dawo nan.
    Zuwa tayi ta zauna inda ya nuna mata, ya buďe ledar yana fito da magungunan, bayan yagama yashiga yimata bayanin yanda zatayi dasu, wato dai idan ta fahimta saboda Aljanunta yaje ya kar6o mata magani..  
    Saida yagama yimata bayani dalla2 sanan ya ce, "gashi nan idan kin gadama ki ajiye, idankuma kinyi tofa kanki kika taimaka, yana gama fađa yatashi ya fice.
    Binsa kawai tayi da kallo, azuciyarta ta ce, "saiikace wani ďan sarauta.

Koda yafita ďakin aunty bily yanufa, baiwar ALLAH harma tayi barci abinta, bargon yaďaga yashiga, cikin barci taji ana shafata ta mi'ke afirgice, shikam ko motsi baiyiba saidai binta da kallo fayakeyi.
     Cikin rawar murya ta ce, my handsome baka kwantaba ne??,         eh", yafaďa ata'kaice.
  To miya faru naganka anan??, fuska ya haďe tamau, sai wani abu yafaru nake zuwa ďakinki??, bahaka nake nufiba my handsome, ina tuna makane banan yadace agankaba, yakamata ace kana ďakin Nurr dan baka gama mata kwana bakwai na al'ada ba, daga baya saika raba mana kwana ko??.
    Harararta yayi tareda jan tsaki, ta marairaice fuska plzz ya Mahmud gsky nake faďa maka, jiyafa aka kawo yarinyar nan gashi kuma batada isashiyar lafiyama..
   Mi'kewa yayi tsam yabar ďakin, tabishi da kallo tana girgiza kai, wai har sai yaushe zata gane mijinta wane irin mutumne??, kanta tamaida ta kwanta, tasan kodata bishi saidai ta 'kara tunzurashi ya hau sama, dan haka garama tayi kwanciyarta.

Shikam ďakinsa yatafi yayi kwanciyarsa, sai mita yakeyi wai ya za'ayi ya haďa makwanci da Nurr ta rainashi wanan yarinyar daba kunya garesuba ahakama yasuka 'kare bare taga gadon barcinsa, hakadai yayta mitarsa har barci ya kwasheshi.

Itako Nurr takasa barci, har wajen 'karfe ďaya na dare, mi'kewa tayi dan tsoro sake shigarta yakeyi, rufo ďakinta tayi tashiga ďakin aunty bily, itakam zuwa sanan barcinta yayi nisa, saman kujera tayi kwanciyarta.
     Da asuba aunty bily ta tashi zatayi sallah saitaga Nurr saman kujera tana barci, kai ta girgiza dan yarinyar tabata matu'kar tausayi, saida tayo alwala sanan ta tada ita, Nur ta mi'ke bakinta da addu'ar tashi barci, aunty bily ta ce, "haba Nurr miyasa baki hau hadoba kika kwanta anan?? aisai wuyanki yayi ciwo kowani sashe najikinki.
    Murmushi Nurr tayi tana mi'kewa babu komai aunty bana son na tadakine shiyyasa na kwanta anan,, to shikenan jekiyi sallah, ďakinta tawuce tayi sallah daganan tahaye gado sai barci.
    Yauma bata tashiba saida aka tadata, tana mamakin yanda take barci kwana biyunnan kodan tadaďe batayi barcin daya isheta bane????, tunda aka tsira maganarta da ya Mahmud barci ya 'kauracema idanunta saifa akwana biyunnan datake yinsa baji babu gani, bayi tashiga tayo wanka, kwalliya tayi cikin shadda mai ruwan kasa tayi "kyau sosai dukda yanzu ta daina kwalliya, falo tafito kamar yanda aunty bily tafaďa mata, kusan tare suka fito da ya Mahmud, rissinawa tai ta gaidashi sau đaya ya amsa yayi gaba itakuma tarakasa da harara.
    Kai tsaye saman dani yanufa ya zauna, aunty bily tafito daga kichin itama gaidashi tayi cikin girmamawa, ya amsa fuska acunkushe hakan bai dametaba dan idan da sabo sun saba, abincin ta zuba masa kamar yanda ta saba.
   Itama Nurr ta haďa abinda take bu'kata, daganan kowa yacigaba da cin abincinsa, aunty bily ta ce,  "yaya yaufane zanje gurinnan.
    Batareda ya kalletaba ya ce, "ina kenan??.
    Cikin mamaki take kallonsa, ta daure ta ce, "kamanta nagaya maka Ramla ta haihu,, okey yafaďa yana Kur6ar lemo, ki shirya sai direba ya kaiki kokuma idan zaki iya kije da kanki, babu damuwa zanma iya zuwa da kainan, nandai da Marafa ai bawani nisa bane.
   Shiru yayi bai sake cewa komaiba,, Nurr ta ce, "aunty dan ALLAH nima zanje, jinjina kai tayi tareda nuna mata ya Mahmud da idanu, Nurr ta ďan ta6e baki dan tagane mi aunty bily take nufi, ta ďan kalli fuskar ya mahmud ya 'kara wani ďaure fuska dan yana kallon duk abinda sukeyi, itama fuskar ta đaure ta ce, "yaya zanbi aunty bily.
    Banza yay mata yacigaba da cin abincin sa, ya gama ya mi'ke tsam yabar wajen, Nurr ta kalli aunty bily ido cike da hawaye, aunty kina ganifa bai amsaniba.
   Ďan murmushi tayi, Nurr kenan kemafa kinsan halinsa, mi'kewa zakiyi ki bishi, aii kinsan saida lallashi, nima bakiga da buyagi zaiminba, kinga tashi kije ki sake lalla6arsa nasan zai barki.
    To Nurr tafaďa tana mi'kewa jiki a sanyaye, samansa tanufa, yauce rana ta farko data fara zuwa ďakinsa, 'kofar falon ta tura tashiga wani 'kamshi ya bugi hancinta, tabbas tasan dama ya Mahmud mutumne mai tsafta da gwalli tamkar mace, bayason huđa da kazamin mutum ko kađan.
   Saman doguwar kujera ta iskeshi kwance, hannunsa ri'ke da remote, tunda tashigo yana kallonta ta gefen ido amma sai yayi fuska tamkar bai gantaba, takai minti goma atsaye tana tunanin yanda zata tunkareshi.........jitayi kamar daga sama ance mikike sone???, da sauri take kallonsa jikinta sai rawa yakeyi, itafa azatonta baimasan ta shigoba, kai wanan mutumi sai abarshi kawai,, murya na rawa ta ce, "wajenka nazo.
    Tashi yayi zaune batareda ya tanka mataba, saima nuna mata kujerar datake kallonsa yayi da hannu, babu musu tanufa ta zauna, idonshi nakan tv ya ce, "ina sauraraenki faďi bu'katarki dan inada aikin yi.
    Yatsun hannunta ta lan'kwasa yayi 'kara cikin in ina ta ce  "dan ALLAH kabarni nabi aunty nace, ďan tsaki yaja sanan ya ďago idanu yana kallonta, itama ta đago suka hađa ido  da sauri ta maida nata dan bazata iya jurar kallonsaba.
   Ya ce, "k idan an barki saikije??.
 Nurr batasan gatseba ta ce, "eh mana da 'karfin gwuywarta tafaďa, saida ya hararaeta sanan ya ce, "to bazakijeba, idan kin bita waye zaiyi abincin rana???.
    Baga masu aiki nanba, Nurr tafaďa tana turo baki .
    Banxa yay mata yakoma ya kwanta, dandanan idanunta suka cika da hawaye, aunty bily tashigo falon da sallama, suduka suka amsa taje gabansa tana fađin yaya kabarta mu tafi ďin, bai bata amsaba saiya zaro kuďi a aljihunsa ya mi'ka mata, saura kuma ki yuce 'karfe biyar yafaďa yana kwanciya, wannan amsarma ta wadatar da ita dan haka tayi musu sallama ta fice....................


luv oll my fan's
©2017
[21/02 11:39] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE



BILKEESA IBRAHEEM
     {♡bilyn Abdul♡}



25
   


..........Tunda aunty bily ta fice sai hawaye suka fara zirara a kumatun Nurr,, yana kallonta ta gefen ido amma ko kallo bata isheshiba ma, ahankali ta 'mi'ke tabar ďakin, falon 'kasa tadawo ta zauna, saikuma ta tashi tashige ďakinta ta kwanta tanata kuka.
      Saida tayi mai isarta daga baya barci yay gaba da'ita.
   Tunda tabar ďakin bai motsa daga inda tabarshiba, yana kwance yana kallon kwallo, saida aka kira sallar azuhur sanan yami'ke yay alwala yafito, al'adarsa ce ko masallaci zaije saiya sanarwa matarsa, dan haka yafara le'ka kicin, a irin wannan lokacin yakan samu aunty bily ne akicin, tsayawa yayi yana bin ko'ina na kichin ďin da kallo dan babu alamar anyi girki aciki bare ya ce har angama.
    Fitowa yayi zuwa ďakin Nurr, tana kwance saman gado tayi ďai2 iskar AC tana ratsata, yaďan runtse ido tareda cije le6ensa na 'kasa lallai yarinyarnan 'yar rainin hankalice, watoma barci takeyi.
    Bakin gadon ya 'karasa cikin faďa ya ke kiran Nurr! Nurr!!, taďan buďe ido saikuma tamaida ta lumshe abinta ya daka mata tsawa 'k!!!! Wai wane irin iskancine wanan.
     Agirgice ta tashi tana murza idanu ta waresu akan ya Mahmud dake tsaye tamkar dogari.
    Ya 'kara tsare gida yana faďin incedai kin mana girki kafin kizo ki kwanta?.
   Girki kuma?? Nurr tafaďa tana 6ata fuska, nifa banyi wani girkiba dan barci nakeyi tun ďazu, wata uwar harara yake watsa mata wadda tunda tafara magana yake mata ita, jiyake tamkar ya bugeta, dan haushi saikawai ya juya zai fita, Nurr kuma tana binsa da kallo, saida yaje hanyar fita sanan ya juyo nabaki nanda kafin indawo wlhy natarar kin girka abinci yafice abinsa.
    Tabďijan kajimun mutum saikace wata inji?, zaka wanice daganan kafin kadawo na girka abinci, munti nawa ake idar da sallah, kaini wlhy katakura min gida zankoma danni ba matarka bace daka raina kake juyata yanda kakakeso, ita sonka take niko banta6a jin sonka ko kaďanba azuciyata wlhy, hasalima haushi kake bani masifaffe kawai mtsowwwwww!!! Ta 'karashe maganar da tsaki.
    Bayi tashiga tayo alwala saida tayi sallah sanan tanufi kicin ďin tana tunanin mizata dafa dazaiyi saurin dahuwa???, murmushi tayi dan tagano muguntar dazayimasa, afili ta furta idan kasan wata aibakasan wataba Alhaji, badai girki kake bu'kataba kafin kadawo? zaka kuwa samu.
    Kayan miya ta gyara ta wankesu sanan ta markaďa, ta ďaura kifi awuta, tashiga yanke2n su karas da sauran kayan haďinsa, tanata hidimar girkinta yadawo yawuce ďaki yay wanka sanan yadawo falon 'kasa, zuwa sanan tagama girkin harma tajereshi a dani tatafi ďaki yin wanka.
   Yana nan zaune tafito cikin 'kananun kaya, siket dakaďan yawuce gwuywarta sai 'yar riga mara nauyi kanta ko ďankwali babu.
    Saida gabansa yafaďi yayinda yaďago yana kallonta dan tunkafin ta iso 'kamshinta ya iso, kayan sunyi mugun zauna mata ajiki saikace ajikinta aka haliccesu, kaďan yarage ta harbo jirginsa saboda ruďani dayaďan shiga, yarinyar tanada 'kira mai 'kyawun gani, da burgewa, amma saiyayi saurin kama kansa, ya gimtse fuska 'k wane irin iskancine wanan?, koma ki ďakko ďankwali, zakiwani fitowa mutane da wanan daddagaggen gashin naki abin amai.
    Nurr ta 6ata fuska danjin ankushe mata gashinta datakeji dashi (tasan dai gashinta yafi na Sadiya sulaiman tyw) amma zai wani kushe mata gashi, saidai taďan murguďa baki tace aidai yafi naka acan 'kasan makoshi tafađa.
    Ya ce, "mikikace??.
    Da sauri ta ce, "nifa bance komaiba.
  Kedai kika sani kuma ki 6acemin da gani anan, ďaki ta koma amma koda ta ďaura ďankwalin saitayi zamanta a ďakin, shikam yana zaune yana jiranta, baifargaba har minti talatin tacika da tafiyarta, afusace yami'ke yanufi ďakin, rainin hankali yafaďa zuciyarsa yayinda yaga Nurr zaune a kujera tana duban hotuna, mima yakamata yay wa yarinyar nane danta shiga hankalinta yagafa raini yana niyyar shiga tsakaninsu.
    Gabanta ya'karasa yayinda itakuma taďago arikice tana kallonsa (na ce, "garashin kunya gakuma tsoro Nurr ďin mama kenan), albom ďin yakwace ya wurgar gefe, tuni ta tashi tana rawar jiki taje jikin dirowa ta ma'kale, yazazzare mata idanu waini sa'ankine??, cikin rawar jiki ta ce, "A'a.
   Okey rainine yakeson shiga tskaninmu?, yafaďa yana zare belt ďin wandonsa, tuni mutuniyar taku tafara kuka tana faďin ALLAH niban rainakaba, dan ALLAH karka dakeni natuba.
    Ai yau sakin gayamin rainin dake shirin shiga tsakaninmu, inbanda iskanci kinsan inacan ina jiranki kizo ki bani abinci shine zakizo kiyi zamanki, watoma kin manta akwai mai jiranki??.
    Kaifa kace natashi maka dagani.
    Haushi ya'kara kamashi ya ďaga belt ďin zai bata ďaya ai dagudu tafice tayo falo shikuma yadaki dirowa, yadafe kai oh ni Mahmud wauy sai yaushe Nurr zata bar shiriritane??, ahaka zata haifamini yaran danake buri daga gareta?, yarinya kamar ďiyar goye?, ALLAH ya shiryaki yafaďa yana maida belt ďinsa ajikin wandonsa.
   Falon yafito, tana ganinsa tasake ranta anakare, ko inda take bai kallaba yanufi dani yazauna, dakansa yabuďe abincin zai zuba, "innalillihi" ya faďa tareda maida kallonsa ga Nurr dake tsaye tana kallonsa, zonan ya ce, "tareda tamke fuska.
    Tayi burus dashi dan tasan laifinta, tsawa yadaka mata wlhy idan bakizoba saina zaneki yau agidanan, da sauri ta'iso wajen amma 'kirjinta na dukan uku2 na tsoro, kujera ya nuna mata ya ce, "zauna, babu yanda zatayi dole tajawo kujerar ta zauna, ya tura mata kular abinci yana nunawa 'k! Tunda kika tashi kinga nata6a cin kus2?, kuma da ubawa da ubanwa zasuci wanan uban abincin dakika dafa??, komu ashirinne agidan??, shiru tayi masa tana kallon kus kus ďin, yasake daka mata tsawa badake nakeyiba???.
   Tai saurin cewa ainazata yanzu kafara ci tunda kayi aure, ta'kare maganar da zum6ura baki, dukda yana cikin jin haushinta tabbas tabashi dariya amma saiya gimtse, ya watsa mata harara, k wai yaushe zakiyi hankaline??.
     Ta ce, "ai mama tace sainan gaba.
   Tsaki yaja okey zaki gane sainan gaba, oya ďauki cokali yau saikin cinye abincin nan duka, zakiga asalin rainin hankali.....................



Luv u oll my fan's
©2017
[21/02 11:50] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE.







®BILKEESA IBRAHEEM
      {♡Bilyn Abdul♡}






26

.......Tazaro ido haba yaya yaza'ayi na iya cinye wanan abincin sokake nazama mai 'katon ciki??.
     Kizama mana ubanwa yace kidafa??, wlhy koki faraci kokuma yanzu jikinki yagaya miki, jan kular tayi zuwa gabanta tana hawaye tanaci, shikam yana zaune da caja ahannunsa, tun tanaci da dauriya harta kasa tafara yun'kurin amai,, kinsan ALLAH kikayi min amai anan saina baki mamaki garama ki ri'ke abinki, dan ALLAH yaya kayi ha'kuri wlhy na 'koshi jinake tamkar na mutu ka tausaya min plzzzzz.
       Haba yarinya aisai kin cinyeshi tas, keba 'yar rainin hankaliba?, kinga gobe aii saiki sake dafa abinda banaci ko??, ta fashe da kuka tana ri'ke ciki wayyo mama nashiga ukku kinacan ana ana za'a kashe miki ďiya, ni wlhy gida zan koma bazan iya da wanan bala'inba........kafin ta'karasa ya mi'ke yana faďin nine bala'in kenan??, ya tsula mata caja ajiki, da sauri ta ru'kun'kumeshi tana kuka, tari'keshi tsam harya kasa wani motsi bare yasamu damar sake dukanta, sai kuka takeyi tana jijjigashi wajan ďaďaďaga 'kafafu.
    Tsaye yake kamar gunki yakasa koda motsi dan gabaďaya tatafi da imaninsa, ana cikin haka aunty bilkee tayi sallama da sauri Nurr tasakeahi taje ta ru'kun'kume ta tana kuka, aunty wlhy ni gida zani, bazan zauna ayita dukanaba, nidai bazan zaunaba.
    Aunty bilkee ta ďagota tana lallashi kinga yi shiru to ya isa haka, hannu ta ri'ke mata suka 'karasa inda ya Mahmud yake tsaye, ta ce, "my handaome miyake faruwane??.
    Kular abincin kawai ya nuna mata batareda yayi magana ba, gaban dani ta 'karasa ta kalli kus2 ďin dake ciki taďan zaro ido, Nurr kece kika dafa??,.
   Bkai Nurr taďaga tana hawaye.
    oh ke Nurr yanzu nan yazamuyi da wanan abincin??, kinsan kuma yaya baya cin kus2?, yanzu dan ALLAH ina zamu da wanan uban abincin kamar mu ashirin ne agidan?.
       aunty nifa bansan yanda ake zuba yawan abincin gidanananba, shiyyasa nayi kamar yanda mukeyi agida.
    Dariya sosai ta tahoma aunty bily tasaka hannu tana gimtsewa dan karta tunzura ogan nasu, dataga zata fito fili saita ďauki kular abincin tanufi kichin, tashiga bin ledojin kus2 da Nurr tabuđe wato biyar tadafa kenan?, kai ALLAH yashirya kuruci dangin hauka. agurguje tayi wani girkin dan tasan tabbas yanajin yunwa, kamar tasani tabaro gidan sunan badan angama shagalinba.
    Zuwa tayi ta jere abincin sanan ta ce, "yaya ga abinci nasan kanajin yunwa, mi'kewa yayi yanufota ai wlhy bily idanma kinji yinwa ďaya, yarinyar nan tunda kika bar gidanan take bani hauka, ni kainama harya fara ciwo, dariya aunty bily tayi my handsome ai saidai ha'kuri kasan har yanzu akwai kuruciya atattare da Nurr, sai munringa lalla6ata da sakata a hanya, nasan wataran komai zai daidaita.
       hummm to ALLAH yasa amma nidai banhango ranar hankalin Nurr ba anan kusa.
    Haba yaya zatayi wlhy, bari kaga tafara haihuwa.
   tabďi jana wace zata haihu yanzu??.
    Nurr mana.
  Lallai to idan ta haihu wazai raini wani itada ďan??, itama kanta ba'agama rainontaba bare tahaifi wanda zata raina.
   Dariya aunty bily tayi ta ce, "yaya kenan ai abun ba'anan yakeba, mudai kasan 'ya'ya muke bu'kata.
    Baice mata komaiba illa murmushi kawai dayayi, bayan yagama cin abincin yatafi sallar la'ar.

Haka rayuwa taci gaba datafiya, yauda gobe sai ALLAH inji masu iya magana, yau satinsu Nurr biyu da aure, shiririta awajenta sai abinda yay gaba, tun ya Mahmud yana mata magana harya tattaraeta ya watsar, saidai aunty bily tana 'ko'kari wajen bambance mata gabas da yamma.

Deena kuwa anacin amarci yanda yakamata, soyayya sosai akeyi agidan kamar babu gobe, idanma da rabo akusa tofa ansamu ciki kila, yauma suna falo itada mijin sunatashan sharafin siyayyarsu, ta kwantar da kanta ajikin kafaďar ya suraj, ta ce, "my D!, na'am babyna yafaďa yana shafa kumatunta.
   Dan ALLAH yaushe zaka kaini nagano Nurr??, wlhy duk kewarta ta isheni.
   Kumatunta ya sumbata, karki damu babyna insha ALLAHU weekend ďinnan zamuje saiki wuni acan, murmushi tayi tareda bashi kiss mai zafi awuya, ta ce, "ngd my D ALLAH yabarmu tare, amin babyna, nan suka cigaba da hirarrsu cikin nishaďi.

Agidan Nurr kam yau ta tashi batajin daďin jikinta, gashi itace da girki dukda ba kwana take da mijinba ma, gashi bata iya barci saboda ďan karen tsoro datakeji, aunty bily kuma duk ranar girkinta ďakin ya mahmud take kwana.
    Bayan ta idar da sallar isha'i ta rarrafa ta kwanta a kan gado.
    Acan kuma aunty bily tana can tana ro'kon ya Mahmud akan yarin'ka kwana ďakin Nurr tunda ita batason zuwa ďakinsa, gashi duk ranar girkinta bata barci saboda tsoro.
    Ďan tsaki yaja yana faďin bily bazaki ganebane, Yarinyar nan batada kunya, yanzuma yaya muka 'kare bare taga gadon barcina.
   Hummm yaya kenan, katuna Nurr tanada ha'kki akanka domin itama matarkace, yarinyar nan watarana zata bar duk abinda takeyi kuma zakace nina gaya maka, dan ALLAH kaje can ka kwana.
   Hummm bily kenan shike nan tunda kin matsa, ammafa gsky dole kicigaba da ďaukar nauyina zuwa wani lokaci.
   Murmushi tayi dan tagane inda yanufa, karka damu na yarda, to shike nan malama bilkisu.
    kai yaya yau kuma nice malamar??.
   eh mana gashi anzo an tsareni da wa'azi, mi'kewa tayi tana dariya to saida safe nidai.
      ALLAH yakaimu yafaďa yana binta da kallo harta 6acema ganinsa.
      Sai wajen 'karge goma yashiga ďakin Nurr, tana kwance zazza6i ya lullu6eta, ya'karasa gefen gadon ya zauna danshi azatonsa ta kwantane kawai, jiyayi tana fidda numfashi da 'kyar, "k lfy kuwa yafaďa yana yaye bargon data lullu6a dashi, ya salam bakida lafiya dama??.
    Ďagota yayi zuwa jikinsa, tabuďe ido ahanlali tana kallonsa, bakida lafiya amma shine baki faďaba??, ahankali ta ce, "naje zanfaďa ma aunty bily natarar bata ďaki, miyasa ni bazakije ki sanar minbane??, babu komai tafađa tana lumshe idanu.
    Goshinta yashafa ya ce, "sorry, tashi kisha magani, jinginata yayi ajikin gado yaje ya ďakko mata magani, dakansa yabata tasha, ita abin ma mamaki yake bata ammafa duk abinda yake mata baya burgeta dan ahushi yake batama, itafa ba sonsa takeyiba.
    Komawa tayi yakwanta, shikuma yaja bargo ya lullu6eta, barci yafara ďibarta taji ya nutsata ajikinsa, shiru tayi dan barci yafara cin "karfinta................








Luv u oll my fan's
©2017
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *