check your best novels here

Saturday 11 March 2017

SABON AL'AMAREE 9/13

[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE



BILKISA IBRAHIM
    {♡bilyn Abdul♡}


Kuyi ha'kuri da typing ďin danakeyi yanzu kaďan2, wlhy ayukane sukayimin yawa.
    Kucigaba da kasancewa dani A SABON AL'AMAREE, dan har yanzu shimfiďa mukeyi bamu shiga cikin Novel ba,, akwaifa SABON AL'AMAREE agaba mai ban mamaki da al'ajabi,, karna cikaku da surutu kudai kubiyoni.
    Ina mi'ko ďunbin gaisuwa da fatan al'kairi ga masiyana aduk inda kuke,, luv u oll.


              
    9                                  
                                              

........Tun kafin ya fahad yagama fakin su deena suka fice da gudu, sunaji ya Mahmud yana daka musu tsawa amma basu saurareshiba ko kaďan, ya fahad kam dariya suka bashi sosai,, a babban falo sukaci karo da mama suka cikuykyeta suna ihun murna, cikin farin ciki mama ta rungumesu tana mai jin daďin ganinsu,, Saiff yafito dagudu daga ďakinsa, shima cikin farinciki ya ringumesu, dan danan gidan yakacame da ihun murnar ganinsu, kowa kagani yana cikin walwalar ganin su auta.
    Bayan gama murna sukaje sukayi wanka, cikin 'kananun kayan nasu nafama sukayi kwalliya,, haďaďďen abincin da mama ta haďa musu dakanta sukaci suka 'koshi, daga nan akashiga bawa su mama labarin D/Z, har daddy saida yasha labari,, ranar kunnen kowa bai hutaba agidan saida dare yayi,, suna ďakimsu daniyar kwanciya, deena tahaďa uniform ďinsu tana ninkeke dasuka baza akan gadon, ta shinshina kayan Nurr ta lumshe idanu, Nurr tabita da kallon mama ki, kekuma lafiya??, batareda tayi maganaba ta mi'kawa Nurr kayan saitin hancinta, Nurr ma ta sha'ka, ta ce, "turaren ya Mahmud ne, inason turarennan wlhy, amma munnemesa mun rasa, narasa inda yake sayosa.
   Deena ta ce, "gsky turaren ya haďu jibafa kigani wai ďan zaman dakikayi kusadashine yasa turaren ya manne akayanki,, Nurr tayi dariya k 'yar uwa aina manta nabaki labari ďazufa a cinyar ya Mahmud nayi barci,, deena tayi dariya wlhy naganku nima nasha mamaki, ya Mahmud ďin dabaka isa ko kusadashi kazaunaba, amma harda kwantar dake ajikinsa.
   Nurr tayi far da idanu kinsan ni 'yar baiwace,, deena ta hawo gadon tana faďin to sannu 'yar baiwa, kedai kawai ya gadamane, kuma danyaga su aunty Naxee ne,, k kinga irin kallon da aunty Naxee takema ya Mahmud inagafa ta faďa tarkon so,, dariya sosai Nurr takeyi, aiiko ta ďakko dazafi dan batasan halinsa bane.
   Deena taja filo tana kwanciya, ai wlhy nasan koda mata sun 'kare ya mahmud bazai auri aunty Nazee ba, 'yar uwa ashe kingane Nurr tafaďa tana lullu6a da bargo,, kai ALLAH mungode maka gadon nan kaima kayi missing namu,, kwana nawa bamuyi kokawa akankaba,, deena ta ce, "kai bodin gidan bala'i jiya iyanzu munacan anayimana 'kunshi ko??, Nurr takalli agogo hakane kam,, yanzu ko khairat tayi barci??, 'kila tayi kinsanta dai kamar kasa take, haka sukaita hirarsu har barci ya ďaukesu.
     Washe gari dakansu suka haďa break ďin gidan gaba ďaya, su mama sunji daďi sosai lallai sun yarda yaransu sun fara hankali kam.
  Haka rayuwa tacigaba da gudu da sauri, Sardauna family sunata shirin bikin 'ya'yansu maza da mata, hakama su ya mahmud anata shirin ďaukar amare.
    Dahakadai aka shiga shagalin biki,, duk wata bidi'a za'ayita kafin aure da'an ďaura aure za'a kai amare ďakinsu shikenan biki yatashi, su Nurr anata iyayi, dama anyimusu ďunkunansu tunkafin su dawo,, gashi aunty rukayya da aunty suhaila suma sunyi musu, dadyma ya burgesu da nasa,, hakama mama da mami, kai autaras dai sunfito gari kam.
    Yaune akayi loncin gurin yayi matu'kar haďuwa dukkan amare da angwayen sun hallara awaje, kuma kowa yabada ma'ana, karkuga yanda ya Mahmud da ya fahad sukayi 'kyau abin saiwanda yagani,, hakama amarensu sunyi 'kyau bilkeesu da ikileema, sai she'kin amarci sukeyi,, yayinda autoci suka fito sai kallo ya koma sama domin kuwa yaran sunyi 'kyau,, sunci adonsu cikin jar doguwar riga ta matiriyal sun naďe kansu da blue ďin gwagwgwaro, sar'ka da 'yankunnesu da gale da takalmi duk blue yaran sun bada ma'ana dan sun ďau wanka mai 'kayatarwa,, su kansu su ya Mahmud sun birgesu, kai kowama sun birgesa,, yayinda akazo fagen rawa kuwa aisai kallo ya koma sama, sai suka ware suna bama jiki hakkinsa yaran sun iya taka kowacce irin salon rawa,, aituni li'ki yatashi daga kan angwaye da amare yakoma kansu Nurr, mawa'ka kuwa suka shiga koďasu,, 'yan uwansu sai hotina da bidiyo suke musu,, tuni wani abokin ya Mahmud ya 'kyasa Nurr amma shi ba ďan family ďin Sardauna bane,, yazone daga abuja, tare sukayi karatu da ya mahmud a jami'ar abuja.
    Hotuna sosai yaran sukayi, yanda suke rawa abin duk ya 6atawa ya Mahmud rai,, amma babu damar magana, dasun haďa ido dashi saiya sakar musu harara,, aiko ko a kwalar rigarsu, tunda sunsan bazai dakesuba cikin taron jama'a,, shikam ya fahad dasun haďa ido saiya jinjina musu tareda yimusu murmushi,, sunsha rawa kafin daga bisani taro yatashi.
     Washe gari kuma akayi kamu, nanma su Nurr sun cashe damma ya Mahmud baijeba,, amma ana gobe ďaurin aure da'akayi dina da daddare suna fara rawa ya mahmud yakirasu, da har sun'ki zuwa sai sukaga ya mi'ke da'alama wajensu zai nufo,  dasauri sukazo,, ya galla musu harara waiy ku bakuda hankaline?, kuzauna kuyita rawa kamar mazari,, wlhy duk wadda nasake gani afincan tana rawa acikinku sainaci 'kaniyarta,, kunemi waje ku zauna kamar yanda kowa yazauna,, Nurr ta ce, "yaya muna murnanefa,, ya sake hararar ta to shikenan kuci gaba zakuga murna ajikinku, marasa kunya ku 6ace min dagani,, jiki a sanyaye suka shige.
    Aunty bilkeesu ta ce, "yaya daka 'kyalesu daga yaufa shikenan,, ya girgiza kai bazaki ganeba my bily yanzu haka wani abokina saboda wannan iya shegen dasukeyi yaga Nurr wai yanaso nayi masa hanya wajen daddy, ni nama rasa mizan cemasa, saboda inajin kunyarsa,, nasan kuma family ďinmu ba'a bada aure ga bare saidai idan ALLAH ya 'kaddara.
   Kuma Nurr yarinya ce banaso ta lalace da soyayya tun yanzu, karatu nakeso suyi,, bily ta ce, " shikenan saimuyita mata addu'a ALLAH yaxa6a abinda yafi alkairi,, ya mahmud ya ce, "amin ya rabbi.
   dahaka taro yatashi,, washe gari aka ďaura aurensu ya mahmud da amarensu,, zokaga farinciki awanana family,, to ya Mahmud & ya fahad ALLAH yasanya alkairi,, yabaku zuri'a tagari,, ALLAH ya kore fitina acikin auren............................




luv u oll my fan's
©2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE








 BILKISA IBRAHIM
    {♡bilyn Abdul♡}


               
   10                                  
                                             
........Kowa ka kalla yana cikin farinciki, da daddare aka kai amare ďakinsu, suma anan anguwar zasu zauna amma daga can sama, jerin gidajen matasan family ďin,, ana kai amare kowa ya koma gidansa domin ya huta, shikenan kuma sai wani ya taso.
     Su Nurr suna zaune a harabar gidan suna hira itada deena dama basuje kai amaryaba, ya Mahmud ne yafito cikin kwalliya, farar shaddace ya ďora 'yar gaske sai mai'ko takeyi,, ďinkin ma ya amsa sunansa dan yazauna dai2 da tsarin halittarsa,, ya ďora farin gilas a idanunsa sai zabga 'kamshin turarensa yakeyi mai daďi 'kamshi da saka ma'abocin sha'karsa nishaďi, Nurr ta tunture da dariya tana kallon ya Mahmud,, cikin tuhuma deena take kallonta k wai lfyarki kuwa??, cikin dariya Nurr ta ce, "wlhy ya mahmud ne yabani dariya, kina ganin yanda ya kwama gilas a idonsa.
   Deena ta juyya tana kallonsa itama dariya tayi ta ce, "wlhy kuma yayi masa 'kyau sosai fa,, abokin ya Mahmud dayace yana son Nurr ya ta6a ya Mahmud, Mahmud kaga 'kannenka can tun đazu daka fito suke kalloka kodai kayi musu 'kyaune?.
   Ya Mahmud ya ďago dara2n idanunsa yana kallonsu deena dake ta dariyarsu, ya ce, waďancan yaran dakake ji da gani bafa mutuncine dasuba, bari kaga ina zuwa, batareda yajira amsar abokansaba ya nufi su Nurr, suna ganin yanufosu suka shiga gimtse dariyar dasukeyi, yana zuwa suka haďa baki wajen gai sheshi, bai amsasu ba saima tambaya daya jeho musu, kai mukukeyi anan wajen??, deena ta ce, "yaya muna shan iskane ciki hayaniya tayi yawa,, yaja ďan tsaki aransa ya ce, "wai har waďannan 'yan yaran sunsan wata hayaniya, afili kuma saiya ce, "to kallon mikuke mana kamar wasu ba'kinku???.
   Da sauri Nurr ta ce, "yaya wlhy kwalliyarka tayi 'kyau baka ta6a cin gayuba irinna yau ba, jibafa harda gilas,, yaji daďin kalaminnata amma saiya basar ya harareta Nurr kin rainani ko??, da sauri ta ce, "wlhy yaya A'a nidai nafaďane kawai saboda kamana 'kyau, dan ALLAH kayi ha'kuri bazan sakeba, juyawa yayi yatafi batareda ya sake maganaba, amma fuskarsa ďaukeda murmushi, afili ya furta matsoraciya.
   Ya 'karaso wajen abokan nasa yana faďin kumuje ko,, mai son Nurr ya ce,, "gsky Mahmud nidai 'kanwar can taka kullum 'kara shiga raina takeyi yakamata kayi wani abu,, ya Mahmud yaďan Ta6e baki kukam kuna bani haushi, kurasa dawa zakuyi soyayya sai yara 'kanana,, har nawa Nurr take daza awani sota, dan ALLAH kabar wanan zance, dan yarannan dama sun iya raini bare ace ana sonsu ai sai su ringa ganinmu dai dai dasu ma.
    Mujaheed yay dariya, Mahmud kana bani mamaki, har yanzu nagaza gane kai wane irin mutumne wlhy???, kacika son girma dayawa, miye abin raini danka auri yarinya 'karama ai sannannema zaka more sadakinka,, ya Mahmud yay ďan tsaki aidama duk jirgi ďaya ya kwasoku kaida kamal ďin, ni kunga kuna 'kara 6ata min lokaci, idan zaku rakani kumuje, idan kuma surutu mara amfani zaku tsaya nakama hanya.
   Dariya sukayi su duka, Sadam ya ce, "lallai ka nuna mana ka 'kagara, to guy adaiyi ahankali awajen harka karkaje kayi gagarumar 6arna, duka ya Mahmud ya kai masa yana faďin kaidai ďan iskane wlhy sadam, sadam ya kauce yana dariya babu wani iskanci alaramma gsky nafaďa ko 'yan uwa, suma sauran dariya sukeyi sosai, kaseem ya ce, "kunsan dai tuzuru idan yasamu dama sai ahankali, ya Mahmud yay gaba yana dariya, kudai kun bani 'yan iska kawai, niba ďan iska bane, kuma gasu Nurr can zaune sunajin duk iskancin dakukeyi, mota suka shishshiga suna dariya, sukatafi raka ya Mahmud gidansa.
     babu daďewa tawagar ya Fahad tafito, shimadai yaci gayu abinsa, Nurr ta ce, "lallai aure dabanne, zamuyi kewar ya fahad, amma wlhy murna nake da barin ya Mahmud gidanan, dan yanzu zamu shana sosai,, damma gasu ya mubarak nan, dan suma halinsu ďaya da ya Mahmud, ALLAH yasa suma daddy ya ce, "suna gama karatu sufito da matansu ai musu aure,, deena tabawa Nurr hannu suka tafa, kai 'yar uwa dakuwa mun shana awannan lokaci wlhy, dagamu saimu kenan.
  Araina na ce, "dayake kukuma agidan zaku dawwama.

Acan  kuwa su mujaheed sun raka ya Mahmud bayan nasiha da ďan barkwanci na abokai suka taho, akabar ango da amaryarsa,, lallai yau su ya Mahmud za'a shanakai babu ruwanalol.
   Shima ya fahad ya isa ga tashi amaryar, nanma nasan babu sau'ki, dan ajiye wannan ha'kurin nasa zaiyi agefe ya murji amarci, lol.

Washe gari mami tahaďa break mai rai da lafiya su deena suka shirya suka tafi kaiwa, gidan ya fahad suka fara shiga, afalo sukaci karo dashi, suka gaisheshi tareda tambayar aunty ikilee, ya ce, "autaras auntynku tana barcin gajiyar bikine, sukace to idan ta tashi ace muna gaisheta ga break nan inji mami, yauwa yaran mama sannunku kunji,, kuce munama mami sannu da 'ko'kari,, ALLAH ya 'kara musu tsawon rai,, su deena sukace amin tareda yimasa sallama suka fito, suna 'yar gulmarsu.
    Daganan sai gidan ya Mahmud,shikam sunkai minta 15 suna kwankwasa 'kofar falon ba'a buďeba,, Nurr ta ce, "deena kodai mu koma dan nikam nagaji da tsayuwa wlhy, kafin deena ta ce wani abu an buďe 'kofar,, ya Mahmud ne ya buďe musu,, yaja gefe suka shigo sannan ya rufe,, saman kujera suka zauna suna gaisheshi ya amsa yana zama saman hannun kujera shima, sukace yaya ina aunty bilkee, ya ce, "tana ďaki tana barci nima wanan buga 'kor nakune ya tasheni, kunata bugama mutane 'kofa kamar zaku cireta, bakusan idan kunyi ďaya biyuba ku hakura.
   Deena ta ce, "kai yaya break fa muka kawo maku, ya yatsine fuska shine kuma zakuyi mana tashin 'yan birsin,, shuru sukayi dan sunsan shidama ba'ayi masa gwaninta, suka mi'ke suna faďin yaya sai anjima, ka gaida mana da aunty bilkee idan ta tashi, binsu kawai yayi da ido batareda ya amsaba, suma basu jira amsarsaba suka fice.
   Nurr ta ce, "kai shidai ya Mahmud halinsa dabanne dana kowa agidanmu, kiga yanda ya fahad ya tarbemu amma shi sai wani cin magani yakeyi, yayi aurenma bai canjaba, ai aunty bilkee taga takanta wlhy, tayi za6en tumun dare.
   Deena ta ce, "k ai bakisan irinsu ya Mahmud sunfi kowa iya soyayyaba, wlhy saikiga ita baiyi mataba tunda yana sonta.
   Nurr ta ta6e baki to ALLAH yasa haka......... ...........








luv u oll my fan's
2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE




 BILKISA IBRAHIM
    {♡bilyn Abdul♡}


            
                                                              
                                              
11
.........Haka su Nurr sukayita shan hutu cikin farinciki, jisukeyi kamar karsu koma,, yauma suka ďau wanka cikin dogayen jallabiya ba'ka, suka naďe kansu da farin mayafi sunyi 'kyau sosai,, ďakin mama suka fara shiga sukace mata sai sun dawo,, ta ce, adawo lafiya 'yammatana, bayan sun fito sukaje ďakin mami sukayi mata sallama itama sannan suka nufo waje sai gidan aunty rukky.
   Suma anan anguwar suke basuda nisa dasu ya Mahmud, cikin farinciki ta tarbesu,, ma'aruf yaronta yazo ya rungumesu yana mai farin cikin ganinsu, suma cikin farinciki suke ďagashi sama,, deena ta ďauki khursum dake wasa cikin 'yar motarta, tashiga ďagata sama tana wangale baki.
   Aunty ruky ta ce, "autaras ďin mama kunyi 'kyau saidai bodin tasa kun rame kunyi ba'ki, deena ta ce, "himmm aunty badole mu rameba, kinga 'kyauyen kuwa da ya Mahmud yakaimu,, wlhy munsha wahala sosai, danma ALLAH yahaďamu da wasu 'yan aji shida sunata gatantamu.
   Ayya to ALLAH yabiyasu da mafificin al'kairi,, ai kune bakwajin magana ko kaďan, inda kun nutsu kundaina ďakko musu magana aida ba'a kaiku bodin ba,, Nurr  tayi dariya haba aunty kema haka zakice bama jin maganar??, eh mana ina kuke jinta, kune dukanyaran mutane kune barna kamar 6eraye,, dariya sosai sukeyi wai su aunty ruky takecema kamar 6eraye, sallamar mijin aunty rukyne ya katse musu dariyar, ya 'karaso yana murmushi kai lallai yau 'yan bodin ne agidanmu,, ina sauran 'kanzon da kwaki???
   Suka tuntsure da dariya,, yaya aimu bama cin 'kanzo da kwaki, ya ce, "kai haba kufaďi gsky dai?,ALLAH kuwa yaya mu  abincin makarantarma bamu ciba bare 'kanzo da kwaki, yay dariya to shikenan 'yan 'kannena, ya gajiyar biki?, kunsha rawa ko?,hannu sukasa suna rufe fuska waisu kunya, aunty ruky ta ce, "lalai sanda kuka cashe ai kun manta da kunyar ko, sai yanzu?, dady ma'aruf ya ce, "ato aisuna da gsky ranar murna sukeyi da farin cikin auresu ya Mahmud ko??, kai suka đaga suna dariya.
   Sun daďe agidan suna hira saida aka kira sallar azuhur sanan suka tafi gidan aunty suhaila,, nanma dai tayi farin cikin ganinsu, nanma hira sukai mata sosai sai gabda magriba suka tafi gida.

------------------------------------------------
                   Suna falo zaune suda Saiff wani American film suke kallo, gaba ďaya hankalinsu yana kan tv, saidai lokaci2 sukanyi ďan ihu saboda film ďin na faďane, ya mustapha da ya mubarak suka shigo falon da sallama, babu wanda ya amsa dan hankalinsu yana kan tv, ya mubarak ne yadaka musu tsawa, afirgice suka ďago suna kallonsa, ya ce, "wane irin iskancine kunaji ana sallama amma kunyima mutane shiru??, cikin rawar murya Nurr ta ce, "sorry yaya wlhy bamujiba, ya mustapha ya ce, "yaza'ayi kujimu bayan hankalinku yana kan tv ku idan kuna kallo film bakwa tunawa da kawa da komai.
   Sudai ha'kuri suke basu, suma zama sukayi, ya mustapha ya ce, "kai kubamu abinci, deena da Nurr suka mi'ke agaggauce suka kawo abincin dabasa so awucesu a film ďin.
         Rayuwa mai gudu da sauri yau gashi saura kwana biyar su deena su koma makaranta,, amma basu ta6a addu'ar komawaba, da yamma suka shirya sai gidan ya Fahad, sun daďe acan suna hira, aunty ikilee taji daďin zuwansu sosai dama kaďaici ya isheta sabida ya Fahad yana office bai dawoba, saida suka tayata tayi abinci suka gyara mata gidan fes sanan suka taho gidan ya Mahmud, itama aunty bilkee ita kaďai suka tarar harma tagama aikinta, ta tarbesu da murna itama, dan danan tacika musu gaba da abinci da abinsha,, kaďan sukaci dansunci abinci gidan ya fahad, daganan suka shiga hira abinsu da labarin shagalin biki, sai wajen 'karfe biyar da rabi ya mahmud yadawo, da sauri aunty bilkee ta tarosa, yaďan rungumota jikinsa yay mata kiss a kumatu, su Nurr suka kalli juna itada deena, hannunta yakamo suka 'karaso cikinfalon shi sai yanzuma ya gansu,, suka rissana suna gaisheshi, sau ďaya ya amsa ya ďora da faďin yasu mami, lfy lao suke suka amsa, yaja hannun matarsa yana faďin ina zuwa dama ina son ganinku,, to kawai sukace suna binsu da kallo suna hayewa saman bene, saida suka shige ďakin sa sannan su Nurr suka tuntsure da dariya suka haďa baki wajen faďin soyayya ruwan zuma. suka tafa, Nurr ta ce, " 'yar uwa kinga wani SABON AL'AMAREE???, deena ta gyara zama tana dariya, kai sis... dama haka ya mahmud yake??, Nurr ta ce, "ga dahir kin gani, kofa kunyarmu baijiba ya mannawa matarsa kiss.
   Deena ta ri'ke ha6a mumadai ALLAH yabamu masu yimana,, dama ance masu shiru2 sun iya soyayya.......
      Aďakin ya mahmud kuwa suna shiga yazube a kangado yana faďin wash ALLAH na nagaji,, aunty bilkee ta ce, "sannu my handsome nasan ka gaji dayawa, yaďan lumshe idanu wlhy kuwa kamar kin sani, yaushe yarannan sukazo??, zasukai awa ďaya da zuwa aunty bilkee tafaďa tana zame masa kayan jikinsa, baice komaiba saima ta6e baki dayayi, tagama tabarshi dagashi sai gajeren wando, ya mi'ke yana faďin bilyna saura  wankan mana, saida tayi ďan fari sannan ta ce, "sorry my handsome kaga bamu kaďai bane, kadaure kayi da kanka yau sai nikuma naje na haďa maka abinci ko??.
   Okey no wahala yafaďa yana nufar bayi, itakuma ta tattare kayan ta kaisu inda ya dace, falo tafito ta haďa masa abinci a dani, su Nurr suna zaune suna kallon ikon ALLAH.
   Bayan ta kammala saman ta koma itama, sanda ta dawo harya fito, dakanta ta shafa masa mai ta kawo masa kayan dazaisaka,, bayan yagama shiryawa suka sakko falon, dani ya wuce abinsa, itama ta take masa baya, ta haďa masa abinci sanan tadawo wajensu deena suka cigaba dayin hira.
    Yana gama cin abinci yatafi masallaci, suma dole suka mi'ke suka gabatar da tasu, saida akayi isha'i yadawo, su Nurr suka sake gaishe shi ya amsa yana zama, yaďan kallesu ince dai kuna lissafin hutunku??, gaba ďayansu saida gabansu yafaďi, murya na rawa suka ce, "ee, ya ce, "okey!!, tokuyi shiri dan ranar da'aka koma zaku koma.
    Tuni hawaye sun wanke fuskar Nurr ta ce, "yaya dan ALLAH kayi ha'ku ALLAH bamason makarantar nan, aďage yake kallonta, to idan bakwaso ina kukeso,, da sauri deena ta ce, "school ďinmu tada, ya Mahmud!!,  yaja tsaki ashe bakuda hankali, kunsandai magana ďaya nakeyi ko??, banason yawan gardama dan haka ku shirya ranar lahadi zaku koma, gobe idan ALLAH yakaimu zan haďo muku provision ďinku, idan kuna bu'katar wani abu daban saiku rubuto mini yanzu, ko idan kun koma gida, idan nazo gidan da safe saina kar6a.
   Shiru sukayi dan jisuke tamkar su kwala ihu, gashi babu damar gardama dan ya haďe girar sama data 'kasa,, yadaka musu tsawa wai bakwa jinane??, cikin tsoro su ka ce, "munaji, "o,! Da iskancin nakune ya motsa, idanma zaku kwantar da hankalinku ku kwanta dan wlhy makaranta babu fashi bare ďaga 'kafa, kuma daina tunanin wataran zaku barta, idan kunga kun barta tofa kun gama, kutashi ku tafi gida dare yafarayi.
   Jiki a sanyaye suka mi'ke,, sallama sukayi musu suka fice suna gunguni........................




Luv u oll my fan's
2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE



 BILKISA IBRAHIM
    {♡bilyn Abdul♡}

              
12                        
                                                                 
........Tunda suka fita basuyima juna maganaba kowa da abinda yake sa'kama zuciyarsa, gidansu khairat suka wuce suka kaimata labarin abin haushi,, itakam harda kuka, amma yazasuyi dolene su koma tunda oga ya 'karrafa, daga nan gida suka wuce, tunda mama tagansu tasan da akwai wani abu a'kasa, kiransu tayi tana tambayarsu cikin lallashi,, ganin ana lallashinsu sai suka saka kuka, suka gaya mata yanda sukayi da ya Mahmud, lallashinsu tashiga yi, ta ce, "suyi ha"kuri su koma tunda yariga ya kafe saisun koma.
   Haka suka ha'kura suna shiri tafiya cikin damuwa, Nurr har wata ramar wahala tayi cikin kwana biyu.
   Ana gobe zasu koma ya haďo musu duk abinda ya dace,, sayayya yay musu irinta 'ya'yan gata, ranar a ďakin mama suka kwana dayake itace da daddy yau,, har gari yafara haske basu tashiba, ya Mahmud yashigo falon da sallama, đakin mami yafara zuwa ya gaisheta sanan yanufi ďakin mama.
     Cikin takunsa na sarauta ya 'karasa gaban gadon, yaďora 'kafarsa ďaya saman gadon ďaya kuma tana 'kasa, hannu yasaka ya yaye bargon dasuka lilli6a dashi, ya cije le6ensa na 'kasa tareda kauda kai gefe dan dagasu sai vest da wandonta, bargon ya maida ya lilli6a musu tareda daka musu tsawa, a firgice suka farka, ganin ya Mahmud tsaye akansu yana huci suka tashi da sauri suna kudundune jikinsu da bargo.
   Fuskarsa a murtuke yake kallonsu,, ya ce, "yanzunan saboda rashin mutunci bama ku tashiba,, nidanake da mata tuni natashi na shirya hakama fahad, wlhy tunkafin na sakko daga gaida daddy natarar daku kun shirya inko ba hakaba wlhy jikinku zai gaya muku marasa mutunci, 'kafarsa ya sauke 'kasa yanufi hanyar fita, haryaje 'kofa yajuyo ya'kara daka musu tsawa wai bazaku tashiba saina lakaďeku!!!!!.
   Har rige2n sakkowa sukeyi daga gado, Nurr tafaďa bayin mama da sauri, ita kuma deena tanufi ďakinsu domin yin wankan.
   Daga nan saman daddy ya haye afalo ya iske daddy da mama daddy yana break mama tana gefensa,, ya tsugunna yana gaishesu daddyne kawai ya amsa amma mama ko motsi batayiba,, daddy ya ce, "Mahmud za'a amaida 'yan makaranta yau kenan??, eh wlhy daddy zasu koma tunda hutunsu ya 'kare, to shikenan ALLAH yay muku albarka gaba ďaya, amin daddy Ya Mahmud yafaďa, daddy ya ďora dafaďin yauwa idan kun dawo kuwa inason ganinka, akwai wani taro danakeso ka halarta a TURKI, an gayyace nine nikuma inada wasu uzuri sosai agabana, dan gobe idan ALLAH yakaimu zan wuce KORIA insha ALLAHU.
   to daddy ALLAH yakaimu,, idan muka dawo sainazo da daddare muyi maganar aii.
   Okey ALLAH yakaimu,, saikun dawo, ina Fahad ďin??, daddy bai kai ga 'karasowaba, amma inaga yana hanya.
  To shikenan ALLAH yakawoshi lafiya, amin ya Mahmud yafaďa yana mi'kewa, bayan yafito daddy yakalli mama datayi burus dasu,, murmushi yayi yana faďin nasan duk cikin 'ya'yanki kinfison Mahmud amma kike nuna ba'kyayi dashi,, mama ta kauda kai gefe tana faďin nikam Alhaji dan ALLAH kabar faďa karma wani yaji,, aini bani na haifeshiba ga uwarsa can mami.
   Daddy ya haďiye dankalin dake bakinsa yana dariya, waďannan halayen yasa yake matu'kar 'kaunar matan nasa sosai, ya ce, "shikenan maman fahad,, mama tayi murmushi to kaji nawa ďan kenan,, haka daddy yayta tsokanar mama suna dariya.
    Suko su Nurr sanin halin ya Mahmud yasasu saurin shiyawa cikin uniform blue da farin hijjabi kayan makarantar ďan zabuwa kenan, jiki asanyaye suka hau saman daddy, sukaje jikinsa suna zauna suna gaidashi, ya amsa yana shafa kansu, ya ce, "yarana yau sai makaranta ko??, suka ďaga kai suna hawaye,, daddy yashiga lallashinsu dayi musu nasiha saida ya Fahad ya iso sanan suka fito suka shiga mota sunata kuka, yau harda ya mubarak da ya mustapha harda Saiff sai sadiq da Nasir yayun khairat, haka suka ďaga zuwa ďanzabuwa.
   Tunda suka tafi babu mai magana, saida ya Fahad yaga shurun yayi yawa sanan yafara jansu da hira, tunsuna bashi amsa ďai2 harsuka fara sakin jikinsu suna hira, suma su saiff motarsu daban.
   Sun isa ďanzabuwa dayawan ďalibai sun dawo, saida aka dam'kasu hannun malaman su sanan su ka shiga yimusu nasiha, alkairi sukai musu mai yawa sanan suka taho suka barsu suna kukan.

Bayan wani lokaci,, matansu ya Mahmud suka fara kwaikwan ciki suduka,, wayyo zokaga murna wajen ya mahmud jiyake kamar ya ahaďiye matarsa bilkisu,, aiko tanashan tattali kamar jaririya, duk wani motsinta akan idonsa,, hakama matar ya Fahad itama tana rainon nata cikin cikin nasara, tana shan tattali itama wajen nata mijin.
   Su Nurr ana ďanzabuwa anashan gwagwarmaya, gata kuwa sai abinda yay gaba awajensu aunty badee, komai sukeso ana yimusu, bare yanzu dasu badee keson cusa kansu wajensu ya mahmud,, dansufa sunanan suna haukan sonsu batareda sunsaniba,, kuma kowa yana 6oyema ďan uwansa sirrinsa.
   Yaudai akai kora zuwa masallaci sallar isha'i su Nurr suna ďaki basu fitaba saboda su badee ne masu korar,, Nurr tafito daga ďaki zatayi fitsari saboda tana fashin sallah, gullewa tayi tafaďi tareda kwalla wata razananniya 'kara mai firgitarwa.....................






luv u oll my fan's
2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE



  BILKISA IBRAHIM
     {♡bilyn Abdul♡}

13
            
                             
      ......da gudu su khairat suka fito, yayinda 'yan aji shiddan dake gurin suka bata taimakon gaggawa, asan'kame suka ďauketa tamkar matatta, ďaki suka nufa da ita aka kwantar da ita saman katifa a'kasa, su deena sai kuka sukeyi, ruwa sadiya tashiga yayyafa mata amma ko motsi batayiba, babu dabarun dabasuyi mataba amma ta'ki ko motsawa,, aunty salma ta ce, "anya kuwa ba aljanu bane??, Naxee ta ce, "nima nafara tunanin haka,, inaga mufita daita gaban ďaki sai ayimata karatu,, haka suka 'kara ďaukarta asan'kare zuwa gaban ďaki zuwa sanan anfara dawowa daga masallaci, shamsiyya tafara karatun alkur'ani cikin suratul ba'kara,, takai minti goma tanayi sanan Nurr tafara fisge2 tana wata irin kuwwa,, su Nazee suka rirri'keta, anuty badee ta'karaso aruďe dan labari yajemata wai Nurr tafaďi babu rai.
 Shamsiyya ta ce, "wanene??.
      Cikin wata irin murya mara daďinji akace basai kinjiba.
  Shamsiyya takuma cewa shikenan tunda basai najiba, karatun tacigaba dayi, Nurr kafara harbe2 tana cewa zan faďa kidaina 'konani zan faďa,, banza shamsiyya tayi mata tacigaba da karatunta,, saida Nurr tafara kuka konace aljanin sanan shamsiyya ta tsaya.
   Ta ce, "to wanene",
    ya ce, "sunan jantile!!, 
   To jantile miyasa kashiga jikinta??.
   Ya kece da wata irin mahaukaciyar dariya, saida yayi kamar minti biyu yanayi sanan ya ce, "tana burgemune danba ni kaďai bane, tun ranar da'aka kawota makarantar nan muke binta, amma bamu samu damar shiga jikintaba sai yau,, har gida muka bita.
   Badee ta ce, "anya kuwa kai musulmine??.
  Nanma saida yayi dariya sanan ya ce, "niba musulmi bane, amma sauran musulmaine.
   To ina ro'konka dan girman ALLAH kafita daga jikin yarinyarnan tunkafin mufara kai ruwa rana,, kaga batayimuku laifin komaiba bare kuce, dan haka kawai ku fita daga jikinta.
   Ya 'kara kecewa da dariya, saikuma ya murtike fuska, k wlhy babu inda zamu domin minga gurin zama, dan jikinta yanada daďin zama gata mai'kyau da'ita 'yar falai2, dan hakama kidaina tunanin zamu fita........ kafin ya'karasa badee ta wanka masa mari, ya dafe kunci yana kallonta,, wlhy karku 'kara kuskuren dukana, idan ba hakaba zan kauce kiyita dukanta babu abinda ya dameni,, shamsiyya taja tsaki ai idan ba'a dokekaba za'a 'konaka wlhy,, batareda tajira amasarsaba tacigaba da karatunta,, ihu yayta kwaďawa yana bada ha'kuri amma sun'ki saurarensa saima 'yan karatun suka 'karu,, yara suna tsaitsaye suna kallo daga nesa,, yayinda 'yan aji shida suka cika wajen,, su khairat ne kawai 'kanana awajen,  suna gefe sunata kuka.
   Saida sukayima al'janinnan ligif da ayar ALLAH sanan suka sakeshi yafice.
   Nurr tabuďe ido tana yatsine fuska, ganin mutane akanta saita fara tambayar lafiya??, babu wanda yabata amsa saima Badee ce ta jeho mata tambaya,, Nurr inane yake miki ciwo ajikinki??"
  Nurr takalli kanta, aunty duk jikina ciwo yakeyi gashi inajin fitsari, sannu suka shiga yimata, aunty badee tarakata tayi fitsari sanan tazo ta kwanta sai barci.
  Wanan kenan

KADUNA.
   a kd kuwa matar ya Mahmud ce babu lafiya, tanata fama da ciwon mara, a gaggauce ya ďauketa suka tafi asibiti, suna zuwa aka shiga bata taimakon gaggawa dan jinine yafara zuba ta 'kasanta,, tunda aka shiga da'ita ďakin ya Mahmud yake safa da marwa a "kofar ďakin, gaba ďaya hankalinsa atashe yake, yana addu'ar ALLAH yabata lafiya ya kare masa jaririnsa.
    Bayan kamar awa ďaya doctor ya fito yana cire safar dake hannunsa wadda ta 6aci da jini, Nos ďin dake biye dashi ta mi'ka masa wata tasa ya jefa safar aciki, akiďime ya Mahmud yataresa da jerin tambayoyi, doctor yaya matata??, ya cikin jikinta??, incedai kun cetomin matata??........, da sauri dector ya katse ya Mahmud, karka damu Alhaji muje office muyi magana.
   Ya mahmud ya takema doctor baya suka nufi office ďinsa,, kujera ya nuna masa suka zauna,, saida yabashi hannu sukayi musabaha sannan ya ce, "kayi ha'kuri Alhaji mahmud munyi iyakar 'ko'karinmu domin ceto cikin jikin matarka amma hakan ya gagara, cikin dake jikinta yazube saidai mutayaku da Addu'a ALLAH yabaku wani mai amfani.
   Ya mahmud ya dafe kai yana jujuyawa ALLAH kaďai yasan irin burin daya ďauka akan cikinnan, amma babu komai ALLAH daya basu ya kar6a shine zai sake basu wani akaro na biyu,   ya ďago kai yana faďin doctor matatafa??".
   Doctor ya ce, "itakam alhmdullah munyi mata allurar barcine dan ta huta, zamaka iya shiga kaganta Dan yanzu nasan angama gyarata..........jiki asanyaye ya mi'ke yafice, ďakin da'aka kai Aunty bilkee yanufa,, itakaďaice aďakin, tana kwance agado idonta arufe, ansaka mata ledar 'karin ruwa a hannu đaya, ahankali ya dur'kusa gabanta yakamo ďayan hannunta daba'a saka 'karin ruwaba, ahankali yake murzashi yana magana 'kasa2 kamar mai raďa,, karki damu bilyna ubangiji yana sane damu insha ALLAHU zai bamu wani, kekuma ALLAH yabaki lafiya, ya 'kare maganar da sumbatar kumatunta, mi'kewa yayi yazaro wayarsa daga aljihu yashiga laluben mami, bugu ďaya ta ďauka.....saida yaďan rissina wajen gaisheta, ya ce, "mami muna asibiti.
   Arikice mami ta ce, "waye baida lfy mahmud!!, cikin sar'kewar murya ya ce, "bilkeesu ce tayi 6ari.
   Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un mami tashiga faďa ta ce, "ganinan zuwa yanzu,, wayar takatse tanufi đakin mama aruďe,, mama tana zaune tana lazumi dan ba'a daďe dagama sallar azuhurba, ta ce, "mami injidai lafiya??.
   Mami ta ce, "dadai sau'ki wlhy yanzu mahmud yakirani wai bilkeesu ce tayi 6ari sunama asibiti, mama ta ce, "Hasbinallahu wani'imal wakil,, ALLAH yabata lafiya,, amin mami tafađa tana mi'kewa mama bari naje asibitin naga halin da suke ciki dannaji kamar shi kaďainema.
   To saikin dawo ayi mata sannu, to mama saina dawo.

Mama na fita asibiti tanufa, sanda taje har yayar aunty bilkee ta je dan ya Mahmud yakirasu,, ta gaisheda mami sanan mami ta tambayeta yamai jikin,, aunty hajarah ta ce, "da sau'ki mami aitanama barcine.
   ďakin suka shiga, mami tanata jinjina abin da addu'ar samun sau'ki ga bilkeesun, ta ce, "ina Mahmud ďin??, aunty hajara ta ce, "yaje sallah yanzu zai dawo.
   Babu daďewa ya Mahmud yadawo, ya gaida mami,, itama tayi masa jaje,, sunďan daďe suna jajanta abin,, mami ta ce, "wai ya akayi haka tafaru Mahmud??.
   Wlhy mami tun jiya nake lura da'ita kamar batada lafiya,, na tambayeta ta ce, "lafiyarta 'kyalau, sabodama karna dameta da tambaya saita dunga dakewa tana nuna lafiyarta lao,, yau hakadai nafita aiki cikin zullumi, wajen shabiyu saina kirata jin muryarta asar'ke nashiga tambayarta lafiya dai kuwa??, ta ce, "babu komai cikintane keďan murďawa, na ce, "shikenan ALLAH yabata lafiya,, harna cigaba da aiki sai zuciyata takasa nutsuwa da yanda naji muryarta shine nabawa Fahad sauran aikin daban gamaba na nufi gida, a tsakiyyar falo na tarar da'ita tanata juye juye, shine na ďakkota muka taho asibiti, sanda muka iso har jini yafara zuba.
            Mami ta ce, "ALLAH sarki, to ubangiji ALLAH yabata lafiya,, amma zurfin cikin bilkeesu yayi yawa, kaida mijinka bazaka faďa masa bakada lafiya ba.
   Aunty Hajarah ta ce, "wlhy mami haka bilkeesu take ko'a gida bakowa yake saurin gane batada lafiya ba.
      kai amma wanan aisaita cutar dakanta gashi gida kai kaďai, hakadai sukaita ďan tattaunawa, kafin kace mi asibitin yacika da dangi sunata zuwa dubata.
   Anan mami ta kwana dan an kwantar dasu,, da daddare daddy da mama sukazo suka dubata, da 'kyar aka lalla6a ya mahmud yatafi gida,, da ya ce, "shifa anan zai kwana, to aunty bilkeesu ALLAH yabaki lafiya,, yakuma azurtaku da wani ďan mai amfani..

D/Z
  Amakaranta ma su Deena suncigaba da harkokinsu kamar yanda suka saba, saidai lokaci2 aljanun Nurr sukan ďan motsa kuma suna bata wahala, dan wataran 'kafa suke ri'kemata su hanata tafiya, wani lokacin kuma susakata ta zauna tayita kuka,, suma su khairat dasunga tana kuka saisu zauna suna tayata, to Nurr kema ALLAH yabaki lafiya.

Itama aunty bilkeesu an sallamota, tacigaba dayin dukkan harkokinta na rayuwa,, matar ya Fahad kuwa aunty ikilee tananan tana jan nata cikin dahar yafara fitowa masha ALLAHU.
   Dahakaidai lokacin bistin yayi, ya Mahmud ne da aunty bilkee sukaje musu,, sunkoyi murna da ganinsu,, ya Mahmud yashiga tuhumar Nurr akan ramar datakeyi, dasauri ta ce, "karatune yaya da tunanin gida amma lafiyata 'kalau,, su deena sunason faďar gsky amma tahanasu.
   Ya mahmud ya ce, "to ALLAH yataimaka, idan kunyi ha'kuri kamar yaune zakuga kun kammala,, aunty bilkee ta ce, "gsky ne.
    Sun daďe suna hira daga bisani suka taho,, kamar yanda suka saba idan sunga 'yan gida sai sunyi kuka yauma hakance ta kasance saida sukaďan matse hawaye....... .......  



luv u oll my fan's
2017
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *