check your best novels here

Saturday 11 March 2017

SABON AL'AMAREE 1/4

[12/02 15:10] bilyn Abdul


  SABON AL'AMAREE
                                          




NA BILKISA IBRAHIM





Da sunan ALLAH mai rahma mai jin'kai, ya ALLAH kabani ikon faďin abinda zai amfanar da al'ummarka, ka tsare harshena daga faďar abinda zai cutar da al'ummarka.AMIN

Ina mai farin cikin sake haďuwa daku asabon littafina mai suna SABON AL'AMAREE, ALLAH yasa mu amfani abinda zaizo aciki. AMIN.

NA sadaukar da wannan littafi ga dukkan masoyana, aduk inda suke.
    Duk wanda yacanja mini wani abu aciki ban yafe masaba wlhy. 

YABO DA JINJINA
    Ga gareku writers gaba ďaya, musamman.

☆ Abba gana.     
☆ Ayusher muh'd.
☆ Rayfat yahaya.
☆ billy galadanci.
☆ leemcy.
☆ ummiee khaleel.
☆ ummiee jafar.
☆ xoxo
☆ safiyya galadanci
☆ Mrs JH
☆ cwtjiddah. 
   Dama sauran waďanda ban ambataba,  ALLAH ya'kara basira
                
                                 
                                           



Da gudu suka shigo ďakin kowa yana maida numfashi, mama dake zaune abakin gado tana ninke kaya tadaka musu tsawa, kai wai lafiyarku!!!!.???
     Bathroom suka shige batareda sunbawa mama amsaba.
   Mama ta maida kallonta ga 'kofa da ake 'ko'karin buďewa, tasan tabbas wani suka takalo daga cikin yayyensu, ilai kuwa hasashen mama gsky ne, wani 'kya'ky'kyawan saurayi ba'ki yashigo yana hura hanci, hannunsa ri'ke da belt .
   Ganin mama a tsaye yasa yay 'kasa da kai, ya rissina yana gaisheta, mama ta amsa tana kauda kai gefe, tashi yayi ya fice dan bazai iya cigaba da ďaukar matakin dayay niyyaba.
    Bayan kamar minti goma da fitarsa mama ta ce, "marasa kunya saiku fito!!.
   Saida suka ďan le'ko suka tabbatar yafita sannan suka fito kowa fuskarsa tana nuna alamun tsoro.
   Mama ta hararesu mikuka yimasa?? Marasa kunya!.
   Matasan 'yammatan biyu masu matu'kar kama da juna suka shiga kallon kallo, kowa bayaso yafaďi laifin dasukayi, mama tasake daka musu tsawa, wai badaku nakeyi bane??,.
   Cikin rawar baki Nurr ta ce, "mama dama yayane yasakamu gyaran...........saikuma tayi shiru tana sosa 'keya,, mama ta hararesu kunsan ALLAH zan aika akirashi yazo yaci ubanku.
   Da sauri deena ta ce, "gyaran ďaki yasakamu shine muka zauna duba wasu takardu daya ajiye, harya dawo bamu gyaraba, shine yabiyomu zai zanemu.
   Mama taja tsaki kudai kuka sani mara mutunci, kunfison kullum ayita dukanku kamar jakuna ko??, kune zakuyita shan wahala abanza, ni ku fice kubani waje masu kunnen 'kashi kawai.
     sum sum suka fice kamar munafukai, afalo sai la6e2 sukeyi, dan suna tsoron yin gamo dashi.
   Saif dake cin abinci afalon ya bushe da dariyar mugunta harda buga kai da kujera, ya ce, "matsoratan banza, aii wlhy dama na ri'ke masa ku........Nurr ta harareshi to ďan haďi basai ka ri'kemuba yanzuma aii baka makaraba mtsoooow.
   Saif ya harareta kwacika bakifa yanzu tunda kunga ya koma ďaki, wlhy yau daba ďakin mama kukajeba da kun daku, dan nasan da mami ce da badaku zatayi........, deena taja tsaki yanzuma kaje ka sanar dashi mun fito mana.
   A'a mikukeci nabaka na zuba, aii wlhy nasan ba 'kyaleku yayi ba............kafin yarufe baki wani saurayi mai tsananin kama dana ďazu yashigo falon, 'yammatan suka sake ranta ana kare zasu afka ďakin mama.
   Da sauri saurayin ya ce, "ku kuma lafiyarku????, sukaja birki danjin ba muryar na ďazu bane, Saif yasake tun tsurewa da dariyar mugunta, cikin dariya ya ce, "yaya Fahad sun zatafa yaya Mahmud ne, matsorata kawai.
    Yaya Fahad yazauna yana faďin hala laifi sukai masa?, eh mana laifi sukai masa yabiyosu zai lakaďa suka sha a ďakin mama, shine dasukaga ya koma ďaki suka fito zasuyi mana salo.
   Yaya fahad ya maida kallonsa ga matasan 'yammatan yana murmushi, ya ce, "autara's bakwajin magana ko kaďan wlhy, aii yaya Mahamud ďinne maganinku, saikuzo ku zauna tunda baya nan, danna haďu dashi a gate zai fita.
   Nurr ta ce, "dan ALLAH yaya Fahad da gsk kakeyi??, kar sai mun zauna ya shigo fa."
  Yaya Fahad yay dariya to kuce yau atsaye zaku wuni kenan?..........mami dake sakkowa daga saman daddy ta kalli su Nurr dake tsaye cirko2 kamar kaji, ta ce, "kukuma lafiya???.
    Saiff yashiga zayyano mata yanda akayi,, mami ta hararesu wlhy tun kafin na aika akira mishi ku wuce ku gyara masa ďakin, inkuwa ba hakaba zaku gane kurenku, aini mama bata 'kyauta miniba dabata bari ya jibgekuba, marasa kunya kawai, oya kuwuce mana tafaďa tana nuna musu hanyar fita...
    Jiki a sanyaye suka fice dan sunsan ba 'karamin aikin mami bane taďaukesu da kanta takai masa.
   Awaje suka tsaya suna kallon kalo, Nurr ta ce, "deena mun shiga uku wlhy tsoro nakeji, kinsan dai dukan yaya Mahamud sarai babu sau'ki, ta 'kare maganar da zubo da hawaye.
    Deena takamo hannunta kinga muje kafin yadawo mu gyara masa tunda yaya Fahad ya ce, "baya nan.
   ďakin suka nufa zuciyarsu tana dukan uku uku dan tsoro..................



Kubiyoni masoyana,, cikakken littafin yana nan tafe insha ALLAHU.  
    KUKAN KURCIYA MA yana nan zuwa gareku, muna wasu 'yan gyararrakine,, mungode da 'kaunarku garemu 
   Luv u oll.








   Bilyn Abdul
                                          
    luv u oll my fan's
                                           
[12/02 15:10] bilyn Abdul: ------------©2017--------------









  
------SABON AL'AMAREE----
    


NA BILKISA IBRAHIM 




BAN MANTA DAKUBA.
☆Ayusha ilyasu.
☆Ummiee Garkuwa.
☆Maman usseey.
☆Maryam G.
☆Rabi'atu sk/mash.
☆Abdul'azez AJJ. 
Kuma ALLAH ya'kara muku basira.



             
                                  
                                           
2



...........Atare suka shiga ďakin gsky ďakin ya haďu, tamkar da mace aciki, Nurr ta ce, "mu raba aikin wani yayi bedroom wani yayi falo, yanda zamuyi mu gama da wuri.
    Deena ta ce, "to jekiyi bedroom ďin, amma dan ALLAH karki zauna wasa, dan nasan kin iya shiririta, Nurr ta ce, "matsalarkice kuma wannan, tafaďa tana shiga cikin bedroom ďin daya 'kawatu da 'kyawu.
               Dagewa sukayi suna aiki cikin hanzari, burinsu suyi sugama kafin mai ďakin ya dawo, sunkuwa yi saurin gamawa, Nurr ce kawai bata 'karasa wanke bayiba, deena tashiga tana tayata dansu gama da wuri.
    Batareda sun saniba ya dawo, 'kofar yasakama key yadawo saman kujera ya zauna, 'kafa ya ďora ďaya kan ďaya yana jiran fitowarsu.
   Cikin hanzari suka fito Nurr ta kwalla 'kara dan ganin wanda suke tsoron haďuwa dashi a zaune, da gudu suka isa bakin 'kofar da zummar guduwa, amma sai sukaji 'kofar gam da key, yadaka musu tsawa data sakasu durkushewa awajen suna rawar jiki, tamkar wanďanda suke cikin dusar 'kan'kara.
   Belt ďin jikin wandonsa yaxare yanufi inda suke, tuni suka 'kara tsurewa, Nurr uwar 'yan tsoro harta fara fitsari awando, tuni hawaye sun wanke mata kumatu, dama akwaita da tsoron duka, saikuma rashin kunya fal cikinta, deena tafi Nurr dauriya sosai.
   Ya zazzare musu manyan idanunsa, cikin 'karaji ya ce, "ku bakwajin magana ko,, kun manta da gargaďin danayi muku wancan weekend ďin ko??, kun raina kowa agidan nan, saboda kunnen 'kashi.
  Nurr zata fara rantse2 ya zura mata ďaya a baya, ta kwala wani uban ihu kamar wadda aka kashe, itama deena aka bata ďaya, saida yay musu uku2 sanana yabarsu, zuwa lokacin sun cika gidan da ihu.
   Yaya fahad yazo yana bashi ha'kuri sannan yabuďe 'kofar yafito yana huci.  ALLAH sarki yaya Fahad sarkin tausayi, shigowa yayi yatadasu yana lallashi, yakamo hannunsu zuwa babban falon kowa yana kwasar kuka, suna shiga sukayi arangama dashi a babban falo zaune, da gudu suka shiga ďakin mama, tabisu da kallo rai a 6ace, baki kawai ta cije tafito falon.
    Cikin faďa ta ce, "kai yanzu nan saida kadoki yarannan akan abinda bai taka kara ya karyaba  ko??.
    Yay 'kasa da kai, ALLAH mama yaran nan basa jin magana kwata2, yanzu idan na 'kyalesu gobe zasu yimin abinda yafi haka, tunda kunnen 'kashi garesu.
   Mama ta ce, "ai ka 'kyauta, nakuma gode,, ayi ha'ku yafaďa yana 'kara rissinar da kai 'kasa, mami tafito daga ďaki tana faďin aini yaymin dai2 wlhy, suba sun raina kowaba agidannan??, gobema idan suka 'kara yaymusu wanda yafi haka.
    Mama ta ce, "ALLAH mami kibar zugashi, dan bazan yarda ya illata min yara abanzaba.
   Babu wani illatawa mama, kema kinsan halinsu sarai, inda basuyi masa laifinba ai bazai dakesu ba ko.
   Mama tajuya cikin đaki tana faďin ai dama mami kekike goya masa baya.
   Babu wani goya baya anan, gadai gsky sai a'kita, saboda shi babba an maidashi juji, kuma ba'kya son laifinsu deena agidan nan.
   Ya Mahmud ya ce, "ALLAH mami yaran nan basuda mutunci, kuma ita mama bataso a hukuntasu idan sunyi laifi, karka damu My son daga yanzu suka 'kara yimaka laifi ka zanesu karka ďaga musu 'kafa.
    Mama tana jinsu tayi shiru dan tasan harda halin yaran, yaya Mahmud yanada zafi sosai amma bashida saurin duka, dan bakomai yake saka musu bakiba saboda bashida yawan magana, idan kaga yayi duka to an kaisa ma'kura kenan.

ASALIN LABARIN.
    Sardauna family shine sunan da'ake kiran ahalin dangin.
    Dangine na 'yan boko kuma 'yan kasuwa, dan 'kalilanne acikinsu suke aikin gwamnati, kan mutanan family ďin  ahaďe yake babu wani bare daya isa yaji sirrinsu, ko auratayyama atsaka ninsu sukeyi, kusan family ďin duk auren dangine.
   Basa yarda ďansu ko 'yarsu ya auri bare saidai idan ALLAH ne ya 'kaddara hakan, ko kuma zaka ajiye matar data wuce ďaya, tofa wannan kanada damar auren bare idan kaso.
     Awannan familyne aka samar da Alhji Abdul'malik, wanda ďane na goma awaje Alhaji mutallaf Sardauna.
    Alh Abdul'malik yanada mata biyu da yara tara.
   Hajiya suwaiba itace uwar gidansa, suna kiranta da mama, itama tafito daga tsatson Sardauna family, dan ďiyace ga 'kanin Alh mutallaf, yaranta shidda dashi, Mahmud shine ďanta na fari, dan batama faďar sunansa, akwai kunya tsakaninta dashi, babu wata sha'kuwa mai yawa tsakaninsu, ko hira bata shiga tsaka ninsu saidai idan ya zama dole, bata shiga harkarsa ko kaďan, bama tafiya sakashi a al'amurantaba, wannan dalilin yasa yafi sha'kuwa da daddyn sa Alh Abdul'malik, dakuma mami.
    Ya kammala karatunsa tuni a fannin kasuwanci, yanzu haka yana kulada kamfanin fahaifinsa mai amsa sunan (SARDAUNA FAMILY CARPETS & RUGS NLM)...................

Kubiyoni a page nagaba danjin 'karshen tarihin.








bilyn Abdul
     Mrs Abdus'salam
          luv u my fan's
[12/02 15:10] bilyn Abdul: 
SABON AL'AMAREE
                        



NA BILKISA IBRAHIM

KUNA RAINA.
☆zarah bukar.
☆Manshat.
☆Deedo 'yar ficika.
☆online Hausa writer's.
☆Exquisite online writer's .
ALLAH ya'kara sibirbiďa muku basira.



   
               
                                                                                3





........Yaya Fahad shine ďa na biyu a wajen mama, shine ďan lelen mama dan shikam komai anayi dashi, shima ya kammala karatunsa a fannin kasuwancin, yana tareda yaya Mahmud a kafanin mahaifinsu, wanda yaya Mahmud yake shugabanta.
     Sai Ru'kayya itama tayi karatu yanzu haka tanada aure, tana auren wani muhseen acikin family nasu, yaransu biyu mace da namiji.
   Sai yaya Mustapha shine ke binta, shikan yanzu yake nasa karatun acikin (BUK) zai kammala a wannan shekarar.
    Sai 'yan biyu Saifullahi da maryam, waďanda suke kira Saiff da Nurr, sukam ko secondary basu gamaba, yanzu suna  (ss 1) dan yaya mustapha yabasu tazara sosai.

   Hajiya wasila itace amarya, wadda suke kira mami,  itama cikakkiyar 'yar family ďince, yaranta uku, Suhaila itace babba, sa'ar Rukayya ce, komai na rayuwarsu tare sukayi, itama tana auren ďan family ďin, yaranta biyu duk maza.
   Sai yaya mubarak shima sa'an mustapha ne, suna makaranta tare yanzu haka, dan komai nasu tarene, idanma baka saniba saikace tagwayene, sai auta madeena, wadda suke kira deena, itama sa'ar su Nurr ce, dan haka komai nasu tarene kamar 'yan uku.
    Nurr da deena ko kaďan basajin magana, akwaisu da jan faďa, dan haka kowa yasansu a makarantar su, tundaga malamai har ďalibai, kowa yasan 'yan biyu,, ba'a haďa sati biyu ba'akawo takardar laifinsuba daga makaranta,, tun malamai na dukansu harma suka ha'kura saidai a aiko gida,, suna tsoron yayyensu sosai dan basa ďaga musu 'kafa,, yaya Fahad ne kawai baya dukansu danshi yanada ha'kuri da tausayi sosai.
   Amma sunfi tsoron yaya Mahmud dan ko kaďan baya shiga harkarsu, yaya Mahmud bayida hayaniya sosai dan bai fiya yawan maganaba, dan ba komai yake saka musu bakiba, idan kaga yana hira sosai to daddyne ko yaya Fahad, saiko mami, dama ita mama 'yar kunya sukeyi da juna, daga gaisuwa babu abinda yake shiga tsakaninsu.
   Yaya fahad ne suke tsananin kama da yaya Mahmud amma muryarsu ta bammanta, hakama hali,, ya fahad yanada sau'kin kai, dan mutumne mai barkwanci, dan idan kaganshi cikin yaran yana hira bazaka ta6a ďaukar yayansu bane.
      Akwai sha'kuwa da zaman lafiya da girmama juna a gidan Alh Abdul'malik, ko kaďan ba'a kishi dan kuwa ana zama irin na yaya da 'kanwa, a gidan akwai fahimtar juna dayima juna uzuri, azukatan ahalin gidan akwai tsantsar soyayyar juna, baka isa ka bambanta yaran gidanba duk suna kama da juna, gaba ďaya a ďakin mama suke, ya Mahmud ne kawai ďan ďakin mami.
   Wannan kenan.

Mun dawo labari.
    Tun daga randa yaya Mahmud ya lakaďi su Nurr sukayi karatun tanutsu, duk rashinjinsu sai suka rage idan ya Mahmud yana nan,, gyaran ďakinsa kuwa aii basai ya sakasuba, kullum safiya kafin su tafi makaranta suke zuwa su gyara masa, dama sune suke gyara nasu mama da daddy, sauran gurare kuma 'yan aiki su gyara.
   Yau ta kasance juma'a da wuri aka taso daga makaranta, hakama su ya Mahmud masu aiki sun taso da wuri, harsu yaya Mubarak suna gida kowa yana shirin zuwa madallaci,, kasancewar da sauran lokaci duk suna family falo zaune.
  Tunda su Nurr suka sauka daga motar da ake kaisu makaranta 'kirjinsu ke dukan uku2 dan ganinin takalman yayyen nasu reras a 'kofar falon,, deena ta ce, "Saiff da ALLAH kayi ha'kuri karka nuna takardar nan, wlhy zamu baka kuďin makarantarmu na ranar monday.
   Saiff ya ce, "wlhy ban yardaba  ai dama kunsha yin laifi a makaranta dakunga an bani takardar laifinku saiku cikani da daďin baki da al'kawarin bani kuďin makarantarku, amma dakunga na yaga saiku hanani, to wlhy yau saina kai, kuma ya Mahmud zan bamawa ko ya Mubarak dan nasan kunfi jin tsoronsu.
    Nurr harda tsugunnawa tana bama Saiff ha'kuri da ro'konsa karya bayar.
   Ya ce, "wlhy dama kin tashi dan babu ďaga 'kafa wannan karon, ai bani nace kuje ku aikata laifinba,, yana gama faďa yashige falon da sauri, dan zasu iya murďesa su kwace, da sauri suka take masa baya.
   Da ya Mahmud ya fara cin karo a kujerar farko yana karatun jarida, yayinda sauran kowa ke harkar gabansa, Saiff ya mi'kawa ya Mahmud zungureriyar takardar.
   Ya Mahmud ya'kar6a yana tambayar Saiff tamicece???, saiff ya ce, "ta laifice su deena sukayi amakaranta, hakan yayi dai2 da shigowar su deena falon,, ya Mahmud ya ajiye jaridar hannunsa yana 'ko'karin buďe takardar, cikin tsoro su Nurr suke gaida yayyen nasu, ya Fahad ya ce, "autara's lafiya na ganku kamar marasa gsky???.
   Da sauri ya Mahmud ya ce, "inafa sukaga gsky 'yan iska kuzo nan,, jiki na 6ari sukazo suka durkusa gabansa,, ya Mubarak dayake tsaye yana naďe dutsen guga daya gama guga yanzu, yazo ya rankwashi kawunansu yana faďin muna fukai, aii ni tunda suka shigo nasan basu aikata alkairiba.
   Ya Mustapha ya hararesu aii waďan nan yaran su kaďaine suke bamu ciwon kai agidannan shima yabasu rankwashi ďai2.
  ALLAH sarki ya Fahad sarkin ha'kuri shine kawai ya ce, "to kuyi ha'ku dai, ya Mahmud misukayi???.
    Ya Mahmud ya mi'ka masa takardar yana faďin A'a 'yar wani suka lakaďa a makaranta kamar sune suka haifeta, shine akace ana neman daddy ranar monday, dan baban yarinyar ya ce, "bazai yardaba.
   Ya Mustapha ya ce, "marasa mutunci nida Mubarak zamuje, dama ranar bamuda lectures ďin safe,, wlhy agaban asambili zamusa a tu6eku a zane,  masu kunnen kashi kawai.
   Cikin rawar murya deena ta ce, "wlhy ita tajamu kuma harda kairat da farhan ďin gidan abba 'karami, wlhy bamu kaďai bane.
   Ya Mahmud ya daka mata tsawa dallah kiyima mutane shiru!!, idanma hardasu ai kune shugabanni, bari mu dawo masallaci jikinku saiya gaya muku, hardasu farhan ďin zan haďa na lallasaku, yana gama faďa ya ďauki jaridarsa ya fice, ya mubarak da ya mustapha ma suka fice suna harararsu.
   Ya fahad dayake zaune yadawo kujerar da ya Mahmud yatashi, cikin sau'kin murya ya ce, "wai miyasa ku bakwa jin maganane??, kun fison kullum ayita dukanku dayi muku faďa agidannan??, har kun manta da dukan da ya Mahmud yay muku ranar ko??.
   Cikin zubarda hawaye suka ce ALLAH ya Fahad yarinyarce ta jamu, kuma atanbayi 'yan class ďinmu.
   Ya Fahad ya ce, "A'a nikam yanzu babu ruwana tunda ku ba'a gaya muku magana sau ďaya kuji, kofa wata ďaya ba'ayi dakawo takardar laifinkuba a gidannan, naje nabada ha'kuri da al'kawarin bazaku sakeba, amma shine kuka baďa min 'kasa a ido kuka 'kara, kunga kuwa yanzu da kunya na koma, shima yatashi yafice daga falon.
    Deena da Nurr suka zauna suna kwasar kuka kashir6an, saida sukayi mai isarsu sannan suka tashi dan babu mai lallashi,, mama mai goya musu baya tana sama wajen daddy tana taimaka masa wajen shirin masallaci.
   Mami kuma tana kichin suna girki da 'yan aiki, dan dama haka sukeyi mara girki itace ke tsayawa akan 'yan aiki ayi girki, ke kuma mai girki kina tareda mijinki kina bashi kulawa.
   To dama sun san mami saidai ta zuga azanesu, dan haka idanma suka kwaso laifinsu bamasa tunkarar inda take ko kaďan.
   ďaki suka shige suka kulle kansu,, na ce, "haba 'yammata yunwama ta isheku aii......................







bilyn Abdul 
     Mrs Abdus'salam
          luv u oll my fan's


[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE






NA BILKISA IBRAHIM


4
             
           
                                         




..........Har aka sakko masallaci basu fitoba, saida daddy yafara cigiyarsu sannan, da'kar mama ta lallashesu suka fito, aiiko dagudu suka haye saman daddy dan yayyen nasu duk suna falo suna cin abinci, ya Mahmud ne kawai babu.
   Agaban daddy sukaja birki, yabisu da kallo yana murmushi, yarana sarakan tsoro, gaku da iya laifi gakuma tsoro kamar fararen kuraye.
   Suka gaidashi suna murmushi suma, ya ce, "to kuzo muci abinci kunji, dan naji ance saboda tsoro yau bakuci komaiba, gashi kuma wannan bazai hana ya Mahmud zanekuba, garama kuci kuyi ďan 'karfi,, Nurr tayi kwal2 da idanu kamar zatayi kuka,, daddy dan ALLAH kabashi ha'kuri karya dakemu, ALLAH bazamu 'karaba,, murmushi daddy yasakeyi,, to mamana bar kuka, kunga kuzo kuci abinci,, tare sukaci abinci da daddy dan dama wata sa'in haka yake musu, saiya sakasu gaba suci abinci tare harda Saiff.
   Bayan sun kammala sukayi zamansu afalon daddy har dare sunki sakkowa 'kasa, sabida tsoron gamo da ya Mahmud kosu ya mubarak.
    Saida suka tafi sallar isha'i sannan suka sakko, ďaki suka shige suka kulle kansu, har safiya basu fitoba,, suna kwance suna barcinsu bayan sun gama sallar asuba suka koma, kamar daga sama sukaji an daka musu tsawa,, afirgice suka farka, ya Mustapha suka gani tsaye akansu, ya ce, "'yan iska kutashi ku fito falo, wlhy minti 5 nabaku in kuwa ba hakaba jiki magayi kunne boka.
    Cikin hanzari suka tashi, hijjabai kaiwai suka xira suka fito, babban  falo suka nufa sunyu matu'kar razana daganin yayyen nasu gaba ďaya, gakuma farhan da khairat zaune A'kasa,, kusadasu kairat sukaje suka zauna,, cikin tsoro suka gaishesu ya Fahad ne kawai ya amsa musu.
   Ya Mahmud yay gyaran murya, tareda gyara zama, ya ce, "iskancinku ya ishemu, dan haka hukuncin laifin dakuka aikata jiya shine aikin gidannan gaba ďaya da gidan abba 'karami,, daga yau har monday kune zaku ringa yi, duk wani aikin da 'yan aiki sukeyi,, nasallami 'yan aikinmu suje su huta na kwana biyu,, cikin tsoro suke kallonjuna,, sukam sun shiga uku, aikingidannan aiba 'karamin aiki bane garama adakesu gurinya huce, Nurr tabuďe baki zatayimagana ya Mahmud ya daka mata tsawa, gam ta kulle bakinta.
   Ya mustapha ya ďora da faďin sannan hukunci nagaba shine da Khairat da deena da Nurr duk zaku koma bodin, kuma ranar talata za'a kaiku.
   Atare suka kwallah ihun kuka, yaya mubarak ya mi'ke da belt a hannunsa, wlhy kokuyimana shiru kokuma yanzu ku daku.
   Hannu kowa tasaka tana toshe baki, amma idanunsu yana zubar da hawaye, ya mustapha ya ce, "kaiko farhan dakake biye musu kaima hukuncinka yana nan zuwa,, kuma wlhy babu fashi saikunje bodin kuma ta 'kauye za'a kaiku, government school.
   Yanzu kutashi kufara aikinku, sannan muna jiran break daganan zuwa 'karfe 10 na safe.
   Tashisukayi suka fice suna kuka kamar waďanda aka aikoma sa'kon mutuwa, su biyu suka haďa break ďin gidan, danma iyayensu suna koya musu girki, tunda su aunty suhaila sukayi aure ake ďan basu girki suna jagulawa hargashi yanzu sun iya,  farhan da khairat ma suna gidansu suna cin aiki.
    Yaukam 'yammatan mama sun aikatu saikace 'ya'yan bayi,, gashi daddy ya hana mama magana, ya ce, "babu ruwanta ta saka musu ido.
    duk wanda ya kallesu yasan sunyi laushi, sune girkin rana, dare sharan kowane ďaki, wanke2, komai na gidan yau sune sukayi,, aifa dazasu kwanta dole suka gasa jikinsu da ruwan zafi sosai.
   Washe garima haka sukaci uban aiki kamar jakuna,, sun bani tausayi gsky.
   Ranar monday su ya Mubarak sukai musu rakkiya makaranta,, babu tausayi sukasa aka zanesu, suma suka kar6a suka yimusu uku2, daga nan sukayi shigi da fici aka basu taransifa zuwa (G,G,A,S,S DAN ZABUWA).
   ALLAH sarki sunsha kuka dan suna son nakarantarsu, suma malaman basu so hakaba, 'kawayensu sai kuka sukeyi na rabuwa dasu,, shima Saiff baiji daďin rabuwa da 'yan uwansaba, dukda kullum sai sunyi faďa amma yau saiyaji wani iri.

BAYAN KWANA BIYU.
   aka gama yimusu shirin tafiya bodin, babu irin ha'kurin dabasu bama yayyen nasuba amma sukayi burus dasu,, dama ya Fahad ne mai ďan raga musu, shima yau yayi kunnen uwar shegu dasu,, sunje wajen daddy domin neman ďauki, amma ya ce, "babu ruwansa, haka aka tarkata 'yammatan uku zuwa bodin dake ďan zabuwa,, mama harda 'yan hawayenta,, amma babu yanda zatayi tunda daddy ya saka mata gate, ya Mahmud da ya fahad ne zasu kaisu makarantar.
    Tunda suka shiga cikin garin ďan zabuwa su Nurr suketa yatsine fuska, dan ganin 'kauyen da'aka kawosu,, wai duk eriyar kaduna arasa makarantar daza a kawosu sai wannan 'kauyen, suna cikin zance zuci aka iso gate ďin makarantar mai fentin tutar Najeria, wasu tsofafin masu gadi guda biyu suka wangale gate ďin suna ďaga musu hannu.
   Ya mahmud ya danna kai cikin makarantar,, adaidai kuma wannan lokacinne ďalibai suke tururuwar zuwa karatun yamma cikin uniform mai gida2 amma kala2 ne, kowane aji da kalar nasu.
    Tunda suka fito ďalibai suke kallonsu, sumadai baza ido suke suna kallon ďaliban,, ya Fahad ya ce, "kumuje ko,, Nurr ta yatsine fuska ya Fahad yanzu nan awannan dajin zaku barmu,, ya Mahmud ya watso mata harara, da sauri ta kulle bakinta.
    Office ďin principal aka kaisu dan dama ansan da zuwansu, wani abokin yaya Mahmud ne yay musu hanya, akwai wani ďan uwansa dake aiki a makarantar.
   Bayan angama shiga da fita dakuma cike form daduk abinda yadace, aka kaisu aji huďu, (ss 1a) amma sai gobe zasu fara zuwa aji, an gaya musu dukkan dokokin makarantar.
    Principal da kanta tasa aka kira mata shugabar ďalibai ta dan'ka su Nurr ahannunta.
   Su ya Mahmud sunji daďi sosai, dan haka sukaita godiya..     bayan sun fito daga office ďin pc ya mahmud da ya fahad suka shiga yimusu nasiha, da nuna musu nanfa ba gida bane, dan haka su dage da karatu, banda rashin kunya, da rashin mutuncin dasuka sabayi agida,, nasiha sosai sukayi musu,, suka basu kuďin kashewa dubu biyar2, shugabar ďalibai mai amsa sunan  Badiyya yusif Ahmad ita tasaka ďalibai suka kwashi akwatina da katifu da botikai nasu deena zuwa hostel.
    Bayan su ya mahmud sunyimata alkairi suka tafi suka bar su khairat da kuka,, ALLAH sarku ya Fahad jiyayi kamar karya tafi yabarsu, gaba ďaya fuskarsa ta nuna alamun tausayi,, shiko ya Mahmud ko'a kwalar rigarsa.
   Badiyya tashiga lallashinsu taja hannuwansu suka nufi hostel.........................







Bilyn Abdul
     Mrs Abdus'salam 
           Luv u oll my fan's
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *