check your best novels here

Saturday 11 March 2017

SABON AL'AMAREE 5/8

[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE








NA BILKISA IBRAHIM






               
                                       
                                               


5


.........Tunda suka shiga 6angaren kwanan ďaliban suke baza idanu, ďalibai sunata harkokinsu, wasu suna ďibar ruwa wasu kuma ri'ke da robobi irin na al'majirai suna nufar wani 'katon gini, wasu kuma wanki wasu kuwa suna zaune suna hira, sun wuce wasu ďakuna kamar uku sannan suka nufi wani dake gefe, an rubuta Hostel F, agaban ďakin,, wasu ďalibaine zaune agaban ďakin saman katifu, gawasu kuma suna kamun kunne agefe, wata farar budurwa tsaye kansu da manyan bulalai na dalbejiya.
    Badiyya ta 'karasa inda nakan katifar suke, wata acikinsu ta ce, badee waďannanfa??? tafaďa tana nuna su Nurr dake tsaye suna kallon ikon ALLAH, badiyya ta ce, " 'kannenane aka kawo, wata takuma faďin kai amma gasu 'kyawawa dama kiran da pc tayi miki kenan??, eh wlhy kiran kenan,, wata kuma ta ce, " badee kudai nakula duk danginku 'kyawawane, 'kannenmu kuzonan ku zauna.
    Su khairat suka 'karasa saman katifar suka zauna, batare dasunyi maganaba, badiyya ta ce, "kunga bari na canja kaya na dawo.
   Bayan shigewar badiyya suka tanbayi su Deena sunayensu, khairat ta ce, sunana Aysha Sadiq mutallaf sardauna (khairat),, Madeena Abdul'malik mutallaf sardauna (deena), Maryam Abdul'malik Mutallaf sardauna. (Nurr), wow!! Nice name, 'yammata aji nawa aka kawoku?, (S's 1).
   Masha ALLAHU, ku 'yan wane garine??, Kaduna, wata ta gwalalo idanu kai!!! Tundaga kaduna aka kawoku nan yanzu??, sukace eh, taf lalai sannunku da zuwa, suka ce yauwa.
   Wadda take tambayarsu ta ce, "to mukuma sunayenmu, Salma bashir tana faďa tana nunawa, shamsiyya kabeer, Ni'ima muh'd, Nazeefa sani, Sadiya sani, sai badiyya yayarku, munan 'kawayen junane komai namu ahaďe yake, muduka firifet ne, sai ahankali zaku ida fahimta.
    Badiyya tafito sanye da wando da riga matsatstsu, kai babu ďankwali, gsky tanada gashi sosai, tatsaya kan masu kamun kunne tana tambayar wai waďannan misukayine Nazee???, Nazee ta yatsine fuska waďanda basu bada ruwan wankin tolet bane jiya, badiyya ta ďirkama takusada ita dundu 'yan iska dukkutashi naganku,, 'yan kutumar uba, wlhy yau saikun kawo 2 boket2, suka tattashi tsaye wasuma kuka sukeyi, wata acikinsu ta ce, "wlhy aunty badiyya nidai botiki nane yafashe, kuma nafaďa miki tun shekaranjiya, nama gayama aunty salma, salma dake zaune kusada Nurr ta ce, "eh gsky ne wlhy na mantane, k tashi ki tafi kukuma ku koma kamun kunne.
   Bulalai badiyya taďiba tafara lafka musu abaya, duk wadda ta motsa tata tazube sai an sake, tayi musu uku2, suma sauran  duk saida suka yimusu uku2, kuma su biyarne.
   Bayan angama dukansu akace suje su kawo ruwan kuma,, sudai su deena suna zaune suna kallon ikon ALLAH, dama haka akeyi a makarantar kwana ďin??, suna nan zaune wasu gayya suka zo wajensu, suduka babu mai shigar arzi'ki acikinsu, wasu suka zauna kan katifun wasu kuma saman botikai, suka ce, "waďannan 'kyawawan fa??,, su salam sukace 'kannenmune,, ďaya cikin waďanda sukazo ta ce, "kai amma yau aka kawosu??, shamsiyya ta ce, "yanzuma,, ya sunansu?, Nurr khairat deena, kai amma sunayen sunyi daďi, niharma nasamu dota ta nuna Nurr.
   Badiyya ta ce, "k ni 'kannena ba haka sukeba, wadda tace tana son Nurr ďin ta ce, "kai badee tunda kema haka kike ai dole 'kannenki suma su zama haka,, badee ta haďe fuska kinsan ALLAH jamcy zamu hau jirgin durin uwa mu sakko na kutumar uba, jamcy ta ce, "A'a yi ha'kuri badee tsokanarki nakeyi.
   Ni'ima ta mi'ke tana kama hannun su Nurr kunga kutashi muje ku canja kaya kunji.
   Sai yanzu su deena suka shiga 'katon ďakin da aka layanta gadaje tamkar asibiti, gadajen farko suka shiga, anhaďa rukunin gadajen wajen guda shidda, salma ta ce, to kunga kwanarmu nan kunji, kuma nan zaku zauna, gama kayanku nan, suka kalli inda aka nuna musu harma an saka musu katifunsu saman gado, an tura akwatinansu 'kar'kashin gado,, jakarsu takaya suka buďe suka ďauki kaya na gida suka saka kamar yanda sukaga ďalibai sun saka,, to dama su Nurr ďin gwanayen saka 'kananun kayane, dan hakama yanzu su suka saka.
    Tunda suka fito aketa kallonsu dan ainahin 'kyawunsu ya 'kara fitowa fili, kusada auntys ďin nasu sukaje suka zauna,, anan sukai sallar magriba kamar yanda sukaga sunyi har isha'i,, daga nan suka tafi dasu wajen rabon abincin dare,, kai sudai yau sunata ganin abubuwan mamaki.
    Tofa saida akazo wajen kwanciya suka kasa barci saboda tsoro,, sukaita juye2, Nurr harda kukanta, ta tuna 'katon gadonsu na gida daga ita sai deena, afili ta furta ya Mahmud wlhy ka cucemu, sai wajen asuba barci ya ďaukesu.
    Dasafe akasa ďalibai suka kai musu ruwan wanka, saidai sunata 'kyan'kyamin bayin, haka suka daure sukayi suka fito,, shiri sukayi cikin kayan makaranta,, dawasu yara aka haďasu sukaje suka amso shayi da biredi, tunda suka kar6o suketa kallon shayin kamar ruwan wanke kai, Nurr ta ce, "kai 'yan uwa nifa 'kyan'kyamin shayinnan nikefa wlhy, kairat ta ce, "ashe bani kaďaiba, deena ta ce, "ai inagama ni zubarwa zanyi,, Fateema ibrahim da aka haďasu ta ce, "karku zubar, yanzu zuwa zakuyi ku 'kara madararku da sukari, saikuga yayi muku yanda kukeso.
   Khairat ta ce, "eto yanzu naji batu,, madara da sukari suka 'kara sannan suka iya sha, amma kasa cin biredin sukayi saboda basu sababa.
   Bayan sun gama aka tafi aji dasu,, 'yan ajin sun tarbesu da mutunci bare dasuka gansu 'kyawawa, aiko kujerun gaban aji aka basu suka zauna, 'yan ajin suka fara iyayi sunaso suyi 'kawance dasu, tosu dukma basu wani burgesuba, garama wata khadija umar, da safiyya hashim da muneera lukman, sukam sunďan burgesu dan sunga sune wayayyun ajin ma, kuma kamarma zasufi kowa 'ko'kari,, dama sune suka nema musu kujerun zama.
    Wannan kenana......................








Bilyn Abdul
    Mrs Abdus'salam
         Luv u oll my fan's





©2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE







NA BILKISA IBRAHIM
   {♡bilyn Abdul♡}







   6           
                                    
                                     
.........Su ya Mahmud kuwa tunda suka tafi kewar 'yan 'kannen nasu tafara gallabar zuciyarsu, musamman ma ya Fahad, jiyake kamar yakoma ya ďakkosu.
   Haka suka iso gida kowa yana sa'ka wasi'kar jakuna,, dayake dare yafarayi abinci kawai sukaci suka kwanta, gidan shiru yau babu sarakan 6arna, Saiff harda zazza6i yayi saboda kewa,, an ďauke masa abokan faďansa.
   Hakadai rayuwar taketa gudu da sauri,, gidan basuda labari sainasu Nurr,, komai akayi sai ace dasu deena nanan dayanzu kaza yafaru, kullum sai a ambaci sunansu samada sau talatin agidan,, itako mama idan kanaso kaga farincikinta kayi mata hirarsu Nurr, shi kansa daddy yayi kewar 'yan yaransa.
   Yaudai naga gidan antashi da yawan jama'a,, dukkan family ďin sardauna family manya sun taru agidan su Nurr,, araina na ce, "tokomi akeyi??, gashi 'kakwayena basa nan bare na tambayesu,, ina nan zaune aharabar gidan inata raba idanuwa dan nema hanyar dazan ďakko muku rahoto,, can na hango saiff xai shiga falonsu,, da sauri na kwala masa kira,, yajuyo yana neman mai kiransa,, ganina yasashi nufoni da sauri yana washe baki kamar gonar auduga.
    Ya 'karaso yana faďin aunty Bily dama kina nan?, tundasu deena suka tafi makaranta kika daina zuwa gidannan.
   Nayi murmushi ina faďin A'a saiff bahaka bane,, lamurane sukayi mini yawa wlhy, ga islamiyya ga hidimar my sweet Abdul ďina,, dariya yayi ya ce,, "to uncle Abdul yana lafiya kuwa??, na ce, "lafiyarsa 'kalao wlhy, ykk ya makaranta??, Alhmdllh Saiff yafaďa.
   Saiff mi akeyi agidan naku haka nagansa cike da mutane??, aunty bily ansaka ranar auren ya Mahmud ne da ya Fahad.
   Na zaro idanu waje kai dama aure zasuyi??, eh aure zasuyi dama su Nurr basu faďa mikiba,, na girgiza kai A'a wlhy bamu ta6a maganarba,, wazasu aura??, duk auntys ďinmune, suma 'yan cikin family ďinmune,, ya Mahmud zai auri aunty Bilkisu ďiyar daddy habeb, ya Fahad kuma aunty Ikileema ďiyar abba Umar.
   Na jinjina kai ina faďin ALLAH yasanya alkairi, yaushene bikin,, yay ďan shiru alamar tunani eh naji su mami suna cewa nanda wata huďu,, to ALLAH Yakaimu sannan su deena sunzo hutuma,, ya ce, "eh hakane suna gida.
 Munďan daďe muna hira da Saiff daga baya natashi na nufo gida abina.

D/ZABUWA.
      su Nurr ana ďan zabuwa,, zuwa yanzu sun gama fahimtar makarantar,, saidai su 'yan gatane, su aunty badee basa bari adokesu bare aike,, hasalima saka wasu akeyi suyi musu abu,, su badee suna shanawa a makarantar dan har 'yan aji shiddamma tsoronsu sukeyi, kai harma wasu malaman,, kwata2 basuda mutunci, group ďinsu yayi suna sosai,, 'yan iskane nafaďa aji,, idan suna zaune jiniyos basa son bi tawajensu dan zaka iya wucewa tsautsayi ya faďa kanka, kosu aikeka kosu saka aiki,, har tausa sakawa suke ayi musu,, to sudai su khairat sun shigo da 'kafar dama, dan 'yan gatansu badee ne, koda yaushe suna nane dasu.
     Suna kewar gida dan kullum sai Nurr tayi kuka saboda bata iya barci sosai.
    Yau takama 'karshen sati, tunda aka kaďa sallar asuba ďalibai basu samu damar komawa ďakinsu ba,, sunacan gaban ďakin hostel F zazzaune,, cikin sanyi,, saida su badee suka tashi daga barcin safe sannan sukaje inda yaran suke, su deena suna ďaki kwance, ta Window suke le'ken hidimar da akeyi agurin, wata ba'ka doguwa ta hau saman birandar kaidaka ganta saika ďauka namiji ne,, tana hawa ta ďanna uwar ashariya, kai dan kutumar ubanku kowa tayi 'kasa da kanta,, gaba ďaya yaran sukayi 'kasa da kai cikin tsoro,, wata dake gefe tace 'yan iska suyita gwalo mana idanu kamarna mujiya, duk wadda tasake ďagowa saidai uwarta ta haifi wata,, azuciyata nace rigiji gabji, anya kuwa hakan zata faru 'yammata??.
    Babu abinda kakeji asaman barandar sai ruwan zagi kala2 wanima bansansaba ni sai a yau,, sudai su deena sunadaga ďaki suna kallon SABON AL'AMAREE, haka 'yan aji shiddan nan sukaita bayani ďai ďai yawancin bayaninma dai duk babu ma'ana, bayan sun gama girgije2n su aka kira 'yan aji biyar saman baranda,, ALLAH sarki dukansu akaitayi kamar jakuna saboda dama ba'a shiri 'yan aji shida da biyar, bayan angama loda musu duka aka raba musu aiki, kowacce firifet taja zugarta.
   Haka rayuwar makarantar tacigaba da tafiya su khairat suna kallon SABABBUN AL'AMURA, tamkar al'amara, wasu subaka haushi wasu kuma dariya.

KADUNA
   Ya Mahmud ne yafito cikin kwalliya ta kasaita, sai zabga 'kamshi yake, araina na ce, "kai gsky guy ďinnan yahaďu wannan irin ďaukar wanka haka, ya Mahmud matashin saurayine 'kya'kya'kyawa dukda dai baza'a kirashi alayin masu tsananin 'kyawuba, ammafa ko makaho bazai kirashi mummunaba, shekarunsa bazasu wuce 30/31 ba, dogone babu laifi, kuma 'ka'k'karfane, ba'kine babu 'karya kuma ba'kinsa mai duhune, saidai kawai saboda jin daďi fatarsa a goge take kuma tana bada kalar she'ki,, yanada ďan jiki kaďan amma ba sosaiba, fuskarsa zagaye take da 'kasumba wadda take lashe nairorin kuđi wajen gyaranta, hakama kansa akwai yalwatacciyar suma irin wadda gayun zamani suke tarawa,, yanada wushirya mai 'kyayatarwa yayinda yayi murmushinsa mai ďaukar hankali, baza'a kira ya Mahmud muskiliba amma bashida yawan magana, saidai mutumne mai saurin fushi, kuma yanada faďa sosai dan fuskarsa tana nuwama,, bai cikayin dariyaba gsky, ko murmushi sai yagadama yakeyinsa kodan yaga yana masa 'kyaune idan yayi oho.
   Ya Mahmud baita6a yin budurwaba saboda jin kansa, sai akan bilkeesu, itama itace ta ce, "tana sonsa, aiko da'kyar ya kar6i soyayyarta, bilkeesu ďiyace ta 6 awajen Alh habibu yayan Alh Abdul'malik, yarinyace mai ha'kuri da hankali, gata 'kya'ky'kyawa dirarriya, komai nata yayi, 'kyawawan halayentane suka bata nasara wajen jawo hankalin ya Mahmud kanta,, tun yana basarwa har shima yafara bata kulawa irinta masoya masu matu'kar sha'kuwa, har gashi ALLAH yakaisu da nasarar yin aure yanzu, dan nanda wata huďu sun zama mallkin juna, lol.
       Babban falo yanufa, yashiga da sallamarsa, afalo ya iske Ya mubarak da ya mustapha, suka gaisheshi cikin girmamawa dan gidan ana girmama juna kamarba gidan 'yan bokoba, cikin tsokana mubarak ya ce, "ya Mahmud irin wannan ďaukar wanka haka kodai wajen auntyn mu zaka??.
   Murmushi ya Mahmud kawai yayi tareda kama kunnen ya Mubarak ya murďa, cikin muryarsa mai daďi ya ce, "mubarak karainani ko??, mubarak yari'ke hannun ya Mahmud yana faďin sorry babban yaya magajin daddy.
   Ya Mahmud yasaki kunnen yana dariya,, Mustapha dake zaune agefe ya tuntsure da dariyar mugunta, cikin dariya ya ce, "kai amma ya Mahmud ya iya mashar kunne,, ya Mahmud yashige ďakin mama yana faďin kaima zanzo kanka aii.
    Da sallam yashiga mama tana zaune itada mami suna hira, ya rissina yana gaishesu,, mami ta amsa cikin fara'a, yayinda mama ta kauda kai gefe,, mami ta ce, "yaya sai ina haka??, yay 'kasa dakai yana murmushi mami zanje gidan abba habeb ne,, okey kace za'aje wajen ďiyata bilkeesu.
   Yajinjina kai cikin jin kunya,, mami ta ce, "to agaida mana ita da 'kyau.
   Ya mi'ke yana faďin to zataji, mama najinsu amma ko tari batayiba,, bayan fitarsa mami ta ce, "kai mama ko addu'ar baza'ayimanaba??, mama ta yatsine fuska ta ce, "bakin yimasaba, ai ya wadatar.
    Mami tayi dariya,, kai mama mudai gsky abunnan dakike mana yafara isarmu.
   Mama tami'ke tana faďin kudai kuka sani, nikam badaniba.......................









bilyn Abdul
    Mrs Abdus'salam
        luv u oll my fan's




©2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE


 BILKISA IBRAHIM
      {♡Bilyn Abdul♡}



8
               
                                    
                                          
..........BAYAN WANI LOKACI. 
   yau muta nene gidansu Nurr sunata shirin zuwa D/Z bistin, shiri sukayi sosai domin zuwa ganin 'yan gata, harda daddy, tunda safe suka tafi, cikin amincin ubangiji suka isa da wuri, a office ďin pc akayi musu masauki, sannan aka aika kirasu Nurr,, aiko babu 6ata lokaci suka iso, wayyo zokaga murna wajen 'yan uku, harda kukan shagwa6a su sunga 'yan gida,, daddy ya ce, "yaran mama duk kun rame kunyi ba'ki, Nurr tafara hawaye daddy dan ALLAH kace da ya Mahmud mun shiryu ya taimaka ya maidamu school ďinmu nada, wlhy anan akwai wahala gashi abincin babu daďi.
   Dariya daddy yayi ya ce, "nikam babu ruwana kubari idan kunje hutu saiku bashi ha'kuri, deena ta zaro ido waje, tab daddy wlhy zai bibbigemu ne kawai garama mu ha'kura kawai,, mama ta ce, "karku damu, aiikoni bazan juri ganinku a wannan makarantar ba, dolensa yasan yanda zaiyi daku,, mami ta ce, "haba yara garama idan zaku zauna ku zauna, dan babban yaya babu abinda zaiyi muku, khairat ta langwa6e kai, mami plz kisa baki,, ALLAH ya Mahmud yana saurin jin maganarki,, mami tayi dariya, kukam kuncika raki, kofa hutu ďaya bakujeba.
   Hakadai sukaita hira, suna bama su daddy labarin makarantar, suka kira su aunty badee daddy yay musu al'kairi tareda godiyar ďawauniyar dasukeyi da 'ya'yansa,, dazasu tafi kuka su Nurr sukeyi sosai, da 'kyar su Nazee suka 6an6aresu daga jikin daddy da mama,, suma haka suka tafi cike da kewar 'ya'yansu, mama harda 'yan kwallanta.

BAYAN WATA BIYU.
   su deena suka sami hutu,, sunyi farincikin wannan hutu kamarsu tashi sama,, ya Mahmudne da ya Fahad sukazo ďaukarsu, babu kunya Nurr taje ta rungume ya Mahmud danshi tafara gani kuma ita tafara ganinsa, ďalibai sai kallonsu sukeyi, ya cirota daga jikinsa yana murmushi, Nurr haryanzu ba'a fara hankaliba KENAN??, ta rufe fuska tana dariya wlhy yaya munyi missing nakune, kai kaďai kazo??, da hannu ya nuna mata ya Fahad dake waya a bayan mota,, da gudu ta 'karasa shima ta rungumeshi sai asannan su deena sukaji labari, suma ya Fahad suka rungume dan sunsan ya Mahmud baya son wargi, ya Fahad ya rungumesu yana dariya, cikin sanyinsa ya ce, "i missing u autara's, suma sukace muma munyi kewarku yaya, ya Mahmud ya 'karaso shima, su deena suka daure suka rungunesa amamakinsu sai sukaga baiyi musu faďaba, saima shafa kansu dayayi yana musu musrmushi,, lallai sun yarda ya Mahmud yayi missing nasu shima,, dan saisuce sukan daďe basuga dariyarsaba amma gashi yau yana musu, kodan karya badasu gaban ďalibaine oho.
    Ya fahad ya ce, "ina wadda muka haďaku ďinnan??, khairat ta ce, "yaya bari nakirasu,, babu daďewa taje takirasu sanan su Nurr suna basu labarin al'kairin da su badee suke musu, su badee suka gaida su ya fahad,, sudukansu saida suka 'kyasa matasan samarin masu matu'kar kama da juna,, Nazee ta ce,, "inama ya ce, "yana sona, shamsiyya dake kusada ita ta ce, "wanne aciki??, da ido ta nuna ya Mahmud,, salma ta ce, "ai guys ďin duk sun haďu babu na yarwa, saidai wanda kika nuna yafi aji, daganinsa zaiyi girman kai,, Nazee ta ce, "ai wanan shine halin 'yan mazan,, ya fahad yay musu alkairi sanan yace suyi sallama dan garinsu da nisa, shikam ya mahmud tundaga gaisuwa bai sake kula inda sukeba,, Nurr tana kusadashi tana zuba masa surutu, amma iyakarsa murmushi dan tasanma ba amsata zaiyiba,, tama gode dayake saurarenta.
  Bayan sun gama sallama ya Fahad ya ce, "sushiga mota, deena ta ce, "ya fahad hardasu aunty Nazee da aunty sadiya zamu tafi saimu ajiyesu a malumfashi, ya fahad ya ce, "okey babu damuwa, ai wajen zai isheku, kokuma Nurr tadawo kusada ya Mahmud tunda itace 'yar 'karama,, Nurr taďan zare ido dan tsoro, ya mahmud ya harareta, kinafa 6ata mana lokaci,, jiki a sanyaye tashiga ta zauna kusadashi, dukma rabin jikinta yana jikinsa.
   Suma Mota suka shiga ya fahad yaja suka fice daga gate ďin su aunty badee suna ďaga musu hannu.
     Tunda suka fice daga cikin makarantar bakin kowa yay gum musamman ma Nurr dan batada damar yin surutu kusada saraki,, garama su deena suna hira 'kasa2 sudasu aunty Nazee.
   Nurr ta ce, "ya Fahad ALLAH yunwa nakeji sosai,, ya Mahmud ya harareta to acici saiki bari saimunje wani garin, ya fahad yay dariya, ya mahmud kasan 'yan bodin  kamar almajirai suke nasan yanzu dole a'kara mudun abinci agidannan sabida su autaras sun dawo,, khairat ta ce, "yaya ALLAH jinake kamar naci babu,, dariya sosai ya fahad yakeyi, ya ce, "lallai kuce ci kuka koyo a school ďin??, humm ALLAH ya fahad abincin makarantar babu daďi, tunda mukaje mun kasa ci, deena tafaďa tana hawaye.
   Tofa yanzunan kuna nufin tunda kukaje bakucin abincin school ďin??, eh wlhy yaya bamaci kuma katanbayi su aunty sadiya kaji, tabďi to mikukeci??, yo abincin akwatinmu dakuma kuďin dakuka bamu, saikuma wanda su daddy sukazo suka bamu.
   Ya mahmud da tun ďazu yanajinsu bai tankaba hasalima wayarsa yaketa dannawa,  ahankali ya furta lallai yara kuna tare da wahala kuwa,, ya fahad yay dariya ya ce, "gsky kam.
   Dahakadai suka iso gidan mutum ďaya, kasancewar safiyane babu wani abinci maiďan daďi, saidai 'yan kayan kwaďayi aka sai musu daganan suka 'kara ďaukar hanya,, ya mahmud yana lura da irin kallon da Nazee take masa, dan duk ďagowar dazaiyi saisun haďa ido ta madubi, aiko ya'kara tamke fuska tamau,, sanda suka isa marabar musawa Nurr tayi barci, ya Mahmud ya kwanto da ita jikinsa yana faďin raguwar banza hartayi barci.
   Khairat ta ce, yaya aidole tayi barci jiyafa batayi barciba saboda murna zataje gida,, ya Mahmud ya ce, "zaku iya tunda hankali bai gama isarkuba.
   A malunfashi har 'kofar gida suka kai su Aunty Naxee, daganan suka nufi kaduna,, cikin amincin ALLAH karfe shabiyu a akudana tayi musu................






luv u oll my fan's
2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul SABON AL'AMAREE



 BILKISA IBRAHIM
     {♡bilyn Abdul♡}





                
                                                                        
7


............koda ya Mahmud yafita gidansu bilkeesu yanufa, dayake babu nisa tsakaninsu akafa yaje,, zan iya cemuku yawancin gidajen anguwar duk na 'yan Sardauna family ne, shiyyasama ake kiran anguwar da suna Sardauna.
   Ya tura 'kofar gate ďin gidan yashiga, maigadi dake zaune agefe yanajin redio yay saurin mi'kewa ganin ya Mahmud saiya washe baki, ya rissina yana gaisheshi,, ya Mahmud ya amsa cikin fara'a yana faďin sarkin gate da cakake 6arayine??,, mai gadi yayi dariya, A'a yalla6ai kawai dai abinne yabani mamaki.
   Ya Mahmud yay 'yar dariya tareda zaro kuďi a aljihunsa ya mi'kawa mai gadi, jiki na rawa ya amsa yayita masa godiya da zuba masa addu'oi, ALLAH yabaka 'ya'aya nagari masu amfani yalla6ai, ALLAH yasa kagama da duniya lafiya, ALLAH yasa kagama da iyayenka lafiya......haka dai yayta suburbuďa masa addu'a.
   Ya Mahmud yashige ciki yana mai jin daďin addu'ar ta mai gadi,, yanason yara sosai harma baisan iya adadin dayake addu'a ALLAH yabashiba,, yana fatan ace Bilkeesu tana zuwa gudansa tasamu ciki, idan duk shekara zata haihu zayi farinciki,, akan la66ansa ya furta ya ALLAH kacika min burina na mallakar 'ya'ya masu tarin yawa,, nace amin ya Mahmud.
   Ya tura 'kofar falon yashiga da sallama,, ummy mahaifiyar bilkeesu ta amsa da fara'a, tareda faďin Mahmud kaine tafe??, ya'karasa gabanta yana faďin nine ummy ina yini yafaďa bayan ya durkusa, lfy lau ummy ta amsa, yasu mama dasu mami??, duk suna nan lafiya ummy suna gaisheki, ina amsawa yawajensu Nurr 'yan bodin??, yay ďan murmushi suna lfy wlhy,, to masha ALLAH ai haka akeso, tunda ka kwashema su mama autoci kakai su bodin.
  Ya mi'ke yana dariya, ummy ai gara haka, yaranne basa jin magana ko kaďan,, aii dama yara sai ha'kuri Mahmud, bakaji masu iya magana sunce 'kuruci dangin hauka ba, kumafa duk kunyi irin wanan rashinjin,, kansa ya sosa yana dariya, ummy tami'ke tana faďin bari na turo maka bilkeesun tana ďaki yanzu haka tana barci, aii kana da aiiki sosai a gabanka Mahmud, saikayi dagaske zaka iya control ďin yawan barcin bilkeesu ,, murmushi kawai yayi batareda yace komaiba.
   Bayan kamar minti biyar bilkeesu tafito, ya Mahmud yaďago yana kallonta fuskarsa cike da murmushi, itamadai murmushin takeyi,, harta nufoshi saikuma ta ce, "ina zuwa yaya, kichin takoma ta haďo abubuwan motsa baki, a gabansa ta dire, saida ta zuba masa lemo a kofi sanan ta gaishesa,, ya amsa yana kallonta ummy ta ce, "barci kikeyi??, hummm ummy kenan, itafa dataga nayi shiru aďaki saitace barci nakeyi, wlhy ina karatun novels ne a waya, yaďan murmusa, karki damu nasan kaďaici yana damunki, insha ALLAHU nanda wata huďu kina tareda mai ďebe miki kewa ya'kare maganar da kanne mata ido ďaya ,, hannu tasa ta rufe fuskarta saboda kunya, ya kur6i lemo yana murmushi,, ta ce,, "ya Mahmud wai dan ALLAH miyasa kakai su deena bodin ne??, saida ya haďiye lemon daya kur6a sannan ya ce, "saboda inaso a hora mini su, yaran basajin magana, idan aka cigaba da tafiya ahaka za'a haďa mazajensu da aikine kawai.
   Dariya bilkeesu tayi, ta ce, "humm yaya kenan, to aii daka barsu agidama sai'a hirasu, amma bodin akwai wahala ballesu ankaisu mai nisa kuma ya Fahad ya ce, "min school ďin 'kauyece, humm ai dama nakula bada sonsa aka kaisuba, tundafa muka kaisu muka taho baiyimin maganaba, dana kalleshi sainagama kamar zaiyi kuka, kinsan Fahad akwai tausayi,, bilkeesu tayi dariya, aini burgeni yakeyi saboda yanada matu'kar ha'kuri wlhy, ya Mahmud yaymata hararar wasa okey mukuma bamuda ha'kuri kenan??, cikin dariya ta ce, "A'a ni na isa na faďa, yayi dariya gashima kin faďa, hakadai sukaita hirarsu cikin so da 'kaunar juna, har saida akayi kiran sallar magriba sanan yataho gida.

D/Z.
   A D/Z.... kam su khairat anatashan karatu, saidai matsala ďaya suke fuskanta shine gatanda su Naxee suke musu, dankuwa kamar suna 'kara musu ba'kinjini agun ďalibai. musamman ma 'yan aji biyar, babu abinda yake haďasu da juna sai 'yar harara, wani lokacinma har zaginsu sukeyi, dayawa ana ďaukar su Nurr ne amatsayin 'kannensu badee, dan haka duk muguntar dasu badee keyi akaci burin ramawa akasu deena, matsala ta biyu kuwa itace basa iya cin abincin makarantar saidai kayan kwaďayi dasukazo dasu, saiko kuďin da'aka Basu suketa faman kashewa, damma su dukansu basuda yawan cin abinci.
    Yauma kamar kullum bayan an taso daga makaranta suka iso hostel agajiye dan akwai 'yar tazara tsakanin hostel ďin da classis ďinsu, suka yada zango akwanar su, suna zama su aunty sadiya suka dawo,, suka gaishesu, aunty shamsiyya ta ce, "kutashi kuyi wanka sanan saiku huta gaba ďaya dan yau an shiraya yin wani gagarumin tare, kuma wlhy babu sau'ki,, salma ta ce, "dakin barsu yau anďan ta6a lafiyar jikinsu, tunda tundasuka zo ba'a dakesuba,, Nurr ta ce, "kai aunty salma yanzunan kina fata adokemu wlhy inada tsoron duka sosai.
   Badee tayi murmushi ke 'kaleta kinji Nurr ďin yaya babu mai dukar minku indai ina makarantar nan, saidai idan munbar makarantar, suduka dariya sukayi tareda mi'kewa suna murna,, babu daďewa sukayi wanka suka fito, agurguje suka shirya,, kwanciya sukayi tunda dama basa zuwa kar6o abinci,, amma kullum saisu badee sun ďebo musu nama ko kifi da'ake rabawa.
   Aiiko maganarsu Nazee dutse tunkafin agama rabon abinci akaje gaban gate ďin hostel aka jibge manya2n bulalai,, ALLAH sarki sukam yaran sunsani, dan haka sukaita himmar tafiya wasuma ko abinci basu tsaya ciba suka tafi, 'karfe uku da rabi aka rufe gate, waďanda aka tare sunci duka musamman ma 'yan aji biyar, dama dansu aka shirya yin taren,, shiyyasa aka  'ki basu abinci da wuri,, awajen tarenma sunfi kowa yawa,, humm mugudai baji daďin halinsaba wlhy,, ALLAH ka shiryamu........................









luv u oll my fan's
©2017
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *