check your best novels here

Saturday 11 March 2017

SABON AL'AMAREE 39/42

[06/03 19:32] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》


NA BILKEESA IBRAHEEM
    {♡Bilyn Abdul♡}


Kuyi ha'uri da 1page ďinnan wlhy nawuni kaina yana ciyo, da'yarma nayi wannan, luv u oll


40

.......Sai bayan la'asar sosai Nurr ta tashi, jinta take tamkar ba itaba, ta ja jiki zuwa bayi, saida ta haďa ruwa mai zafi sanan tashiga dan gabaďaya jikinta ciwo yakeyi damma tasha magani amma ďazu ai jitake kamar ba itaba, tadaďe kwance cikin ruwan zafin saida taďanji dama dama sannan taďauro alwala tafito, sallah tafara 'ko'karin gabatarwa dan batayi ko azuhur ba, bayan ta idar tazauna tana shafa mai.
    Tana cikin shafa mai ya Mahmud yashigo da sallama dawowarsa kenan daga aiki, sanin muhimmancin sallama kawai yasa ta amsa amma acan kasan ma'koshi, cigaba tayi da shafa manta batarda tabi takansaba.
    'Karasowa yayi inda take yazauna kusada ita, amma dukda haka batako kalleshiba, yaďanyi murmushi mai sauti Nurri na ya jikin??, nanma shiru tayi masa.
   Ru'ko hannunta yayi yana faďin autar mama wai fushi ake da yayan?, taďan ďago idanunta dasuka kumbura saboda kuka gashi sunďanyi jaa taimasa kallon kaikasani kuma, tamaida kanta 'kasa, yaďan lumshe idanunsa ya buďe, azuciyarsa ya ce, "yazanyi da wannan 'yar rigimarne??, wata dabara ta faďomasa ya ce, "kin fasa zuwa gidan maman kenen?, da sauri ta ce, "zanje mana", haba 'yan mata kinason zuwa amma kike shareni? bayan kuma nine mai kaiki, nama fasa kaki kuwa.
    Sorry yaya tafaďa tana hawaye, yaďan tsura mata idanu, bayason yaga tana kuka dan jin kukan nata yake har cikin zuciyarsa, yasa hannu yana share mata hawayen to kukan ya isa haka, banason gani hawayennan, haba maryam tun jiya da daddare kike kuka ba'kya tunanin hawayenki su 'karene? Kowani wuri yana miki ciwo??.
    "Kai ta girgiza masa".
   Ya ce, "to tsashi kisa kayan bari naje nima na watsa ruwa idan nadawo masallaci bayan naci abinci saimu tafi gidan dadyn.
   Nanma bata tankaba tadai kaďa kai kawai.
   Tashi yayi yafita yana mai mamakin shagwa6a irinta Nurr itafa yanzu idan akace gidan maman za aje yarda zatayi, toshi hauka yake dazai yarda taje wajen mama yanzu, salon taje tayi masa kato6ara, sarai zata iya juye musu yanda akayi, kissing nata kawai yayi kwanaki amma saida taje gida tafaďa bare yanzu dayayi mai gaba ďaya.....hakadai yayta tunane tunane har zuwa đakinsa, tararwa yayi aunty bily ta haďa masa ruwan wanka, yanason Bily kodan 'kyawawan halayenta, babu abinda zaice da ALLAH sai godiya shidai, wankan yashiga yayi, yafito ďaure da alwala, jallabiya kawai yazura ya sakko saboda masallaci.
   Saida yale'ka ďakin aunty bily tana tsaye itama alwala tayi, ta ce, "my handsome ashe kadawo, yaďan murmusa tareda sumbatar kumatunta, ta ce, "kai yaya karka karyamin alwala.
   Ya rungumeta ta baya yana faďin habadai "k saiki yarda alwalar ta karye, tayi  dariya to aikaine sumbarka bakayin 'karama saimai shiga jiki.
   Dariya sosai yakeyi, bilyna kenan akwaiki da abindariya wlhy, ashe akwai 'karamar sumba akwai babba??, ta ce, "oh da baka saniba?, ya jinjina kai gsky bansaniba.
   Ta ce, "to aigashi na sanar dakai, 'kofa yanufa saboda jin kiran sallah yana faďin baridai nadawo masallaci saiki sanar min sosai, ya kashe mata ido ďaya.......dariya tayi ALLAH yashiryaka my handsome, yafice yana faďin amin ya rabbi my bily.

Nurr kam tuni tagama shirin zuwa gidan dady ya Mahmud kawai take jira, ""batasan ya zurata bane kawai"", bayan ta idar da sallah tafara neman wayarta dan rabondata ganta tunjiya, duk inda yakamata taduba bata gantaba, saita ha'kura ta share dama deena takeson kira.
   Koda yadawo daga masallaci bai shigo ďakintaba sai aunty bilyce tazo takirata suci abinci, ta ce, "aunty anya zan iya cin abincinan kuwa??, wlhy bakina babu daďi ďacima yakemin ,, ayya sorry autar mama kinga zomuje kici ko kaďanne sai kisha maganinki tafaďa tana kama hannunta, bataso tayi mata musu dan haka tabita suka fito falo.
   A dinning suka iske ya Mahmud yana jiransu, suka zazzauna, aunty bily ta ce, "Nurr tashi ki haďama yaya abinci, to, tafaďa tana mi'kewa, shikam sai binta yake da kallo, mamaki take bashi saboda ganin tana komai anutse yau babu rawar kai kenan?, tagama haďa komai yanda ya kamata sanan ta ce, "aunty mizan zuba miki??, murmushi aunty bily tayi ta ce, "karki damu Nurr zanzuba da kaina zauna kici kedai kinji, itama ďan murmushi tayi taja kofi tana haďa shayi.
   Ya Mahmud ya ce, "mikuma zakiyi da shayi??, taďan kwa6e fuska zanshane tabashi amsa ata'kaice, amma Nurri banda abinki ga abinci miye kuma na shan shayi??, ki daure kici abincin idanma shayin zakisha saikisha daga baya, A'a ni shayin zansha saboda bakina ďaci yakemin ta 'kare maganar da hawaye.
   Ya girgiza kai, kekam kinzama ra6on kanya, yau duk maganar da akai miki sai kuka ko gajiya bakiyi?,.
    Batace masa komaiba tafara shan shayinta, aunty bily ta ce, "kabarta tasha yaya 'kilama zaifiyimata daďi, kasan idan mutum yana zazza6innan baya sha'awar komai.
  Idanu kawai ya lumshe batareda yayi maganaba, azuciyarsa ya ce, "ita wanan shagwa6ace kawai tayi mata yawa.
    Bayan sun kammala cin abinci suka dawo falo, itakam Nurr ďaki tanufa ta ďakko hijjab, ya Mahmud yabita da kallo, dan tazo ta tsaya masa akai, ya ce, "lfy?, ta gyara tsayuwarta bakai kace nashirya muje gidan dady ba, uhhm nina faďa amma yanzu an fasa, anfasa kuma?, Nurr tafaďa cikin raunin murya, hannunta yakamo ya zaunar da'ita kusadashi, aunty bily tana kallonsu, yaďan lankwashe muryarsa cikin sigar lallashi ya ce, "haba maryam yanzu idan kinje gidan dady mizakiyo??, kedama bakida lafiya kiyi ha'kuri idan kika warke saikije ki yini.
   Shiru tayi masa tana hawaye, ya ce, "ayya Nurr banason kukan nan dan ALLAH, kibar kukannan haka, wai yakikeso namikine dan ALLAH??.
    haushi ya 'kara kamata, azuciyarta ta ce, "kadawo min da budurcina daka kwata da karfi, wlhy indai kukane baka fara ganibama, tunda bakason kuka naringa 6ata maka rai kenan ta hanyar yinsa har sai ka sakeni dan bana sonka nama 'kara tsanarka tsakanin jiya da yau........
      jikinsa ya jawota dan ya kula bazata daina kukanba, ya rungumeta sosai ajikinsa yana lallashi.
   Aunty bily tayi 'kasa da kai danjin wani kishi yana neman tokare mata ma'koshi, sunayen ALLAH tafara ambata da sauri, cikin amincin ALLAH sai taji abin ya koma, tami'ke ahankali tadawo kusadasu yaya indai gidan dady takeson zuwa kabari saimuje yanzu taga mamar.
    Kai ya girgiza mata yana mata nuni datayi shiru....shirun kuwa tayi, shikuma yacigaba da shafa kan Nurr yana lallashi (nace kai Nurr 'yar latsin rainin wayoce tanata ikirarin bata son ya Mahmud amma daya rungumeta saita lafe ajikinsa, anya kuwa wannan kiyayyar ta gsky ce??)
    yaďan shafo kumatun aunty bily dan ganin kamar fuskarta ta ďan canja, taďago tana kallonsa da murmushi a fuskarta, gira ya ďaga mata shima yana murmushin (nace kai namiji akwai iya salon gulma) gawata ajikinsa amma yana basarwa agefe.
    Ita Nurr tunima  barci yayi gaba da ita, (wai ita bata gajiya da barcine? ).
   Ahankali yake jan aunty bily da hira harta ďan saki jikinta tana tayashi, saida aka gama labarai sanan suka mi'ke, ya Mahmud ya ďauki Nurr kamar wata jaririya yakaita ďaki, ahankali ya kwantar da ita sannan yafice.
    Dakinsa yatafi shima yayi wanka tareda shirin barci sanan ya sakko 'kasa, ďakin aunty bily yashiga, tana tsaye gaban madubi tana fesa turare yaďan rungumota tareda ďora kansa a kafaďarta suna kallon juna ta madubi, tayi masa murmushi my handsome baka kwantabane??.
    Yay mata harar wasa, yaza ayi nakwanta bayan baki gama sanar min banbancin karamar sumba da babba ba, tashafo sajen dake kwance akan kumatunsa my handsome kenan to in banda abinka ai kaine malamina, tunda kaine ka koya mini komai.
    Yayi murmushi tareda shafa cikinta my bilyna kenan to yanzu ai kin wuce malamin naki, tajuyo suna fuskantar juna, tasa hannu tana gyara masa kwalar rigarsa shikuma ya manneta sosai ajikinsa, yayana kaje ka kwanta haka nan kaga dare yayi kuma gobe idan ALLAH yakaimu zakaje office.
    Ya'kara manneta da jikinsa, koratama kikeyi??, A'a nina isa na kori maigida da gidansa, kawaidai nasan Nurrinka tana jiranka, yaďan lumshr ido yana murmushi, ya ce, "bilyna kishi ko?, ta girgiza kai tana murmushi no my handsome bana kishi da Nurr kawaidai nafaďane, Nurr 'kanwa tace 'yar uwatace tajini bazan yi kishi da itaba saidai abinda ba'a rasaba kasan rai da kishin abinda yakeso.
    Baice komaiba illa haďe bakinsa dayayi da nata, itama batayi yun'kurin hanashiba dan tana son mijinta sosai, saida yayi mai isarsa sanan yasaketa yana murmushi itama murmushin take masa.
    Tajuya ta haye gado tana faďin mu kwana lafiya, ya jinjina kai dan yakasa magana, yatura hannayensa a aljihu yana kallonta, saida taja bargo sanan ya ce, "saida safe.
    ALLAH yakaimu tafaďa.

Ďakin Nurr yashiga tana zaune abakin gado da alama ta tashine, yana shigowa tawani zabura tana zaro idanu waje, ya'karasa inda take yana binta da kallo, yana zama tana mi'kewa da sauri yaru'ko hannunta, Nurrina ina zuwa???.
   Cikin muryar kuka ta ce, "plzzz dan ALLAH katafi wlhy banason ganinka, nidai karkace zaka 'karamin abin jiya ALLAH mutuwa zanyi.
    Shiru yayi yana kallonta, yaďan lumshe idanunsa, kinga kwantar da hankalinki babu abunda zan miki, barci kawai zamuyi kinji.
    Tashiga girgiza kai A'a nidai bazan kwana ďaki ďaya dakaiba.....ta rushe da kuka, yami'ke da sauri indai har zaki daina kukan tozan tafi, tashiga share hawayenta tana faďin wlhy bazan sakeyiba.
   Yaďan ďaga kafaďa tareda ta6e baki okey saida safe....yafice abinsa, da sauri taje tasakam kofar key, (hhhhhhh Nurr kina burgeni wlhy, kina haďama ya mahmud zafi gsky, amma bari zan haďaki da ummiee jafar ).................





Luv u oll my fan's
©2017
[07/03 14:44] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》




NA BILKEESA IBRAHEEM
     {♡Bilyn Abdul♡}


Masoyana kuna 'karamin 'kaimi da 'karfin gwuywa ngd sosai, ALLAH yabarmu tare, ina muku gaisuwa da fatan alkaireee .
   Luv u oll

41

...........A falonsa ya zube saman kujera, ya fitar da huci mai zafi daga bakinsa, tabbas saiya cigaba da ha'kuri da Nurr, to amma miyasa take masa irin waďannan abubuwan haka?? (Zuciyarsa ta ce, "bata sonkane), ya runtse idanu yana girgiza kai, a fili yafurta ina banyardaba, inko hakane to tabbas zan koya mata yanda zata soni, bazan iya jure zama da macen dabata sonaba alhalin ni ina mata soyayya mai zafin gsk.....ya maida kallonsa ga wayarsa dake wringing tofa Ahmad kira da daddarennan??, ya ďauka tareda sallama, daga can aka amsa masa, ya ce, "mutumina ya dai kira da daddare?, sorry Sardauna wlhy nima nayi tunanin haka to amma matsalace ta tasomin kilama natada kaine daga barci?.
   A'a bamma kwantaba wlhy, miye matsalarka brother?, Ahmad yaja numfashi wlhy kuďi nakeso Sardauna, kuďi kuma? To har nawa?.
       Eh idan zansami kafar 50/millions daganan zuwa 'karshen wata zan dawo maka dasu, wata harkace tazomin wlhy gashi kuma kuďina basu kai yanda ake bu'kataba.
    Okey babu damuwa, idan naje office gobe idan ALLAH yakaimu zamuyi magana da Fahad komi kenan zakajini.
    Yauwa ngd sosai Sardauna, agaida iyali, zasuji insha ALLAHU nima ngd, yakashe wayar yana faďin Ahmad kenan sarkin rikita2 kayan wani kuma za'a rakito kenan, to ALLAH yafiddamu dan kar6ar bashinka sai ahankali bason biya kakeyiba.
     Mi'kewa yayi yatafi ďaki ya kwanta, yaja filo ya rungume wai kanada mata har biyu amma zaka kwana kai ďaya saikace gauro ( nace irinsu Safiyya galadanci kenan da ummiee khalil ).

Washe gari haka suka wuni yakasa gane kan Nurr, da anmata magana sai kuka, shi abinma yafara bashi haushi dan haka ya kuduri aniyar shareta gaba ďaya, yauma dayake ba ďakinta yakeba jitake tamkar anyi mata rahma.
   Sau biyu tana auna guduwa gidan daddy amma bata samu dama ba dan mai gadi yayi mugun saka mata idanu, idan taje fita saiyace bari akira oga sanan, haushi yakan kamata sosai gashi ya gar'kamawa gate kwaďo, saiya buďe za'a shigo saiya buďe za'a fita, komai ya dagule mata tanemi wayarta tarasa bare ta sanarma mama tanan, ita tama fara zargin ya Mahmud ne ya ďauki wayar (hhhhh hasashenki gsky ne Nurr, ya Mahmud ya ďauke wayar tun safiyar daya maidaki mace, yasan zaki iya kiran mama tawaya ki sanar mata shiyyasa yayi maganinki da wuri oohh).
    Tana zaune ta rabga uban tagumi jira take kawai atankata tafashe da kuka, ya Mahmud yashigo falon da sallama, bata amsa masaba bare sannu da zuwa, ya 'karaso cikin falon harzuwa inda take, hannun datayi tagumi dashi yacire amma baiyi maganaba ita kuma bata kalleshiba, aunty bily tafito daga kichin yaďago yana kallonta da baki yanuna mata Nurr, tayi ďan murmushi tareda girgiza kai dan shima ya iya takalar faďa, 'karasowa tayi ta kar6i jakkar aikinsa tana masa sannu da zuwa, ya amsa tareda kissing ďin kuma tunta, ta ajiye jakkar takoma ta kawo masa ruwa.
   Ya kar6a yana faďin godiya nake my bily, saida ya shanye ruwan sanan ya ce, "oh nanda kwana tara muna nan da azumi a bakinmu ko??, aunty bily ta ce, "wlhy kuwa yaya abin kamar wasa, kamar yau akayi babbar sallah amma gashi azumi harya zagayo.
    To rayuwar kenan wataranma haka zakiji bamu mun kaura, lallaikam ALLAH dai yasa mucika da imani, amin bilyna, Nurr dai tana jinsu amma ko kallon inda suke batayiba barema tasan da zamansu, shima mi'kewa yayi ya haye samansa aunty bily ta takemasa baya.
    Aďakinsa ya ce, "bily mi akayima 'yar shagwa6ane??,  hummm yaya kenan kudai kuka sani, dukda kun'ki gaya min abinda ya haďaku nasan kaine kajawo damuwar Nurr agidanan, kila kayi mata wani laifine wanda baka saniba tunda da bahaka takeyiba, yafara cire ma6allin rigarsa yana murmushi ni mizan mata??, kawaidai abubuwanne suka motsa, sotake taje gidan dady amma na hana nakuma toshe duk wata kofar zazuuu (guduwa), shiyyasa take wanan fushin.
    To kabarta taje mana, ni aganina bawani abu bane aii.
   Humm gara dakikace aganinki, kedai kalli Nurr kawai, waccan yarinyar da kike ganinta 'yarta 6arece, kishareta kawai kamar yanda na shareta, ina nan dake zata koma Normal.
   To shikenan ALLAH ya 'kyauta amma gsky bazan iya sharetaba.
   Yaďan ta6e baki, aii saikuyi ta bugawa ya shige bathroom abinsa.

Yau tsawon kwana takwas da faruwar SABON AL'AMAREE tsakanin ya Mahmud da Nurr, amma har yanzu komai bai canzaba, bata yarda yakwana ďakinta duk ranar girkinta, kwata2 ta daina dariya bare hira, garama idan bayanan aunty bily tana đan janta da hira danta rage mata damuwarta, amma daya dawo zatayi ďifff, dukta rame saboda tasaka kanta atunani, gashi kuma azumi yanata gabatomu.. 
     yau maigidan zai dawo daga yafiya dan baya 'kasar yana Chaina akan kasuwancinsu, yau kwanansa uku da tafiya.
    Kuma girkin Nurr ne amma batayi yun'kurin shirya masa komaiba har yamma, aunty bily ganin karsuji kunya yasa ta tashi ita tayi, tana kuwa gamawa babu daďewa yadawo, zuwa sanan Nurr tana ďaki kwance tana barci abinta.
   Aunty bily ta tareshi da murna, shima cikin farinciki ya rungumeta cikin kwana ukunnan haryayi missing nasu, bayan ya sumbaci wuyanta ya ce, "ina 'yarrigimar ki?.
   Tayi murmushi tana ďaki inagama barci takeyi, dan tunda tagama haďa maka abinci tashige ďaki, yayi murmushi lallai inaga anhuce kenan? tunda har gashi anyimini abinci?, 
      aunty bily tayi dariya tayi missing nakane.
    ya ce, " koh?".
         Yafaďa yana hawa saman matattakalar benen.
    emana aunty bily faďa tana dariya.

Saida yayi wanka sanan ya sakko, ďakin Nurr yanufa danson gainin kota tashi, yatura 'kofar yashiga da sallama, tana zaune abakin gado tana shafa mai da'alama daga wanka take, jikinta da ďan guntin tawul, jiyayi wani abu ya tsargashi daga kansa har tafin 'kafarsa, yaďan lashe la66ansa haďe da 'karasawa inda take.
   Batace masa 'kalaba dan yanzu ta maida kanta kurma agabansa, zama yayi daf da ita sosai dan har jikinsu yana gogar juna, tayi burus dashi, hannunsa ya sa'kalo ta bayanta, ya ri'ke kugunta sosai tareda ďora kansa gefen kafaďarta, Nurrina babu ko sannu dazuwa?, yau tsawon kwana uku bama tare amma ko kewata bakiyiba??, tasa hannu da zummar ture kansa saiya ri'ke hannun yana murzawa.
    Wai maryam kin koma kurmane??.
    ta ce, "kila hakane.
  Yanda tayi maganar tabashi dariya sosai, amma saiya gimtse yashiga yimata wani salo na musamman.
    Da sauri tayi 'ko'karin kwace jikinta amma saita kasa, saima tawul ďin jikinta daya zame, jikinta yafara rawa, yaya dan ALLAH kayi ha'kuri.
     Hakurin nan kam bazan iyaba, saboda nakula har yanzu bakiyi hankaliba Nurr?,."
  ::cikin muryar kuka ta ce, "wlhy nayi yaya..  
    Kai gsky banyardaba, inda kinyi aida kin fara kula da mijinki, dakindaina shareshi idan yana miki magana, dakin ringa yimasa duk abinda yakeso da wanda yasakaki, amma ina komaima sai 'kara ta6ar 6arewa yake atareda k.
  Dan haka bari na 'kara kaiki makarantar hankali kila ki sake canjawa..  
     Tashiga yimasa magiya, amma ina ya Mahmud ya rantse saiya kai inda yake kwaďayi.
   Babu abinda take fargaba irin tuna wahalar datasha a daren ranar, kuka take sosai amma ya'ki saurararta saima 'ko'karin aika sa'kwanni yake (nafito ina faďin baban soyayya asoye lafiya).
     Aiiko an soye ďin dan saida yakai ga gacci sanan yakoma lallashinta, dakansa yay mata sabon wanka, tayi wankan tsarki shima yayi, ya ďakkota yadire saman gado, ya shafeta da mai yaza6o mata kaya,(azuciyarsa yake tunanin yanda akayi yarinyarna ta tara kananun kaya haka, abinda yashafi atanfa less shadda kaďanne a durowarta sai tulin kananun kaya kamar akanti).
    Yasaka mata kayan tana wani kakkauda kai gefe ita adole batason kallonsa, (nace humm su Nurr 'yammata), da 'kyar tayarda suka zo falo cin abinci................






Luv u oll my fan's
©2017
[07/03 15:00] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》



NA BILKEESA IBRAHEEM 
     {♡bilyn Abdul♡}


42

.......Azumi yarage saura kwana uku, ya mahmud da ya fahad sun haďa kayan azumi na gani nafaďa sunkai gidan daddy, aiko sunsha albarka sosai ( kunsan duk kuďin mutum yanason aimasa alkairi, yakanji daďi komin kankantarsa).
    Agidansama yatanadi komai saidai abinda ba'a rasaba, wanda yakamata dole saida su aunty bily akusa tunda sune mata su sukasan abinda yadace asiya dan haka yabasu umarnin su shirya zai kaisu kasuwa suyo siyayyar azumi.
    To aunty bily dai ta amsa amma banda Nurr data dogare akan bazatajeba, har suka shirya suka fito batakoyi yunkurin tashiba daga kwanciyar datayi akan kujerar ďakintaba.
    Ya Mahmud yashigo ďakin ransa a 6ace dan aunty bily tazo tayi mata lallashin duniya amma ta ce, "babu inda zata.
   Zumbur tami'ke dan ganin ya Mahmud a ainahinsa na da, yadaka mata tsawa "k!!!! Tashi ki shirya mutafi, wai wane irin salon iskanci ne zaki ringa yima mutane??, shin wai ke kaďaice mace tafarko da aka fara kaiwa gidan muji, wlhy Nurr kishiga hankalinki dani banason iskancifa, yanda yake maganar tamkar zai daketa sai taketa shiri cikin hanzari da rawar jiki.
    Ya sake daka mata tsawa wai bazakimin sauri bane!!!, tasaka hijjabin da sauri tana hawaye, kinsan ALLAH idan baki daina min kukaba wlhy yanzu jikinki zai gaya miki aikin banza kawai, dan iskanci k da ammiki magana sai kuka saikace wadda muke yankar naman jikinki kullum,?, daga yau nasake miki magana kikaimin kuka agidannan saikin gane shayi ruwane dallah muje kina 6ata min lokaci.
   Da sauri tayi gaba, shikuma yajawo ďakin, ajikin mota suka iske aunty bily takama hannun Nurr tana murmushi o, ni autar mama sabuwar dai shagwa6a akeji kwanannan......karasowar ya mahmud ya hana Nurr sakin kuka, taje tabuďe baya tashiga, aunty bily ta ce, "kinga dawo gaba ki zauna.......ya Mahmud ya katse aunty bily da faďin barta ta zauna abayan.
    Nurr dake jinsu ta murguďa baki, aii kobaka ceba dama bazan zauna inda kakeba masifaffe kawai, yana kallonta tamudubi tana kunkuni amma baisan abinda take faďaba, yatada motar suka fice daga harabar gidan, yayinda direba ke binsu abaya awata motar dazasu zubo abinda suka siya .
    Tunda suka tafi suke hirarsu su biyu amma banda Nurr datayi shiru abaya, saidai data ďago ido zata kama ya Mahmud yana kallonta, dasun haďa ido saiya 'kara tamke fuska yana kauda kai (aranta ta ce, "kadaiji da guntuwar gulmarka).
    Akasuwa suka shiga suna siyen duk abinda yadace, amma Nurr sai daddogarewa abaya take, ganin kartayi wani wajen yasa ya Mahmud ri'ke mata hannu, idan kagansu saika ďauka 'karamar 'kanwarsuce kokuma 'yarsu tafari idan sunyi auren wuri, dama ga Nurr ďin 'yar karama babu kiba babu tsawo (kamar mara'kisiyya a gari)ga tsananin kamar dasuke gaba ďaya saboda family ďin duk suna kama da juna saidai wane fari wane ba'ki. Lol.
    Bayan sun gama siyayyar kasuwa sukafito zuwa wata haďaďďiyar  filaza, bazan faďi sunantaba saboda kar ubaida tace zata tunda agarinsune kd.
      Gurin ya burge Nurr sosai, nanma ya Mahmud yana ri'ke da hannunta duk inda zasuje, amma ya ce, "duk abinda tagani ta ďauka itama, (hhhhhh mutuniyarku banda kayan kwaďayi babu abinda take jida tama manta da siyayyar azumi sukazo yi, to ita inama ruwanta kanta kawai tasani,) babu wanda ya hanata tsakanin ya Mahmud da aunty bily saima dariya dasuke mata batareda tasaniba.
   Tana cikin duba wata chocolet wani guy ya'karaso wajen, tundaga nesa ya hango Nurr, yaja birki agabanta yana sakin murmushi, taďago da sauri danjin hucin mutum akusa da ita ita tazatama ya Mahmud ne, ta ce, "lfy kuwa malam??.
    guy ďin yasaki murmushi mai 'kayatarwa, lfyar kenan gimbiya, daga nesa na hango tauraruwa mai matu'kar haske shiyyasa nazo gareta taďan sammini hasken nata.
    Nurr ta ta6e baki lallaikam inaga yakamata kafara rubuta novels zaka samu fan's da yawa gsky dan ka iya tsara magana, tana faďa tafara 'ko'karin barin wajen, da sauri guy ďin yasha gabanta.......karaf akan idon ya Mahmud dayajuyo dan kiran Nurr.
    Afusace ya 'karaso wajen ya wanka ma guy ďin mari, yako dafe kunci da sauri haba alhaji minayi maka??, harar sa ya Mahmud yayi ya nunasa da ďan yatsa daga yau idan kaga matar mutane kasake yimata magana shashasha kawai sakari, wlhy kaci sa'a dasai na tsiyayar maka da idanu yanda zaka ringa tantance irin matan dazaka kalla anan gaba.
   Kai malam nufinka wanan matarkace?, aini wlhy kaďan yarage nace ko 'yarkace?.
   Jikatace ya Mahmud yafaďa yana sake kaimasa duka, dasauri guy ďin ya durkushe ya Mahmud yadaki iska, ya dakama Nurr tsawa dallah kekuma muje 'yar rainin hankali kawai!.
   Yanda yarikice sai abin yabama Nurr dariya dan haka taďan murmusa, yatasa 'keyarta sukai gaba zuwa cikin mota, kuďinma sai aunty bily ce taje ta kar6o ATM ďinsa aka cire, sai yayyafama Nurr ruwan bala'i yake kamar zai cinyeta ďanya, tafara hawaye ya ce, "wlhy idan baki maidasuba zan zaneki amotarnan idan kinji 'karya kuma kici gaba, koda aunty bily tashigo motar bayan anzuba kayan a ďayar motar da direba yake ya Mahmud bai daina masifava.
    Itama shiru tayi dan yanda yaďauki zafinnan zai iya sauke bala'in itama akanta, har sukaje gida yana masifa, ko kashe motar baiyiba yafice sai aunty bilyce takashe ta zare key ďin, sanan tafito da Nurr tana mata faďa.
    Nurr ta ce, "wlhy aunty niba sauraren mutumin nan nayiba kinjifa abinda yacemin........nikuma na ce masa.......shikenanfa zanbar gurin yasha gabana shine yazo ya maresa amma wlhy niba abinda nace masa ta 'kare maganar da kuka.
     Aunty bily tafara lallashinta to kinga bar kukan na fahimceki, amma kije kibasa ha'kuri idan anjima sanan ya huce, yaya yana da kishi Nurr sosai dan haka ki kiyaye abinda zai motsa kishinsa, idan yana cikin mayen kishi komai zai iyayi kikadai ganin marin dayayma mutumin ďazu to kaďanma kenan, dan haka kije kibasa hakuri nasan zai ha'kura.
   Kai Nurr taďaga tana faďin zanje nabashi aunty in ALLAH ya yarda.
    Yauwa Nurr ďin mama, ki kwantar da hankalinki kinji, nibanaso naga kina yawan kukannan ko shiga damuwa, ga azumi yana tahowa gawata rama da ba'ki dakikeyi saboda damuwar dakika saka kanki, plzz kisaki jikinki kamarda Nurr kinji.
    Nanma kai ta jinjina mata.
  Suka kwashi wasu kayan dazasu iya dama tuni direba yanata jida yana kaiwa cikin gidan, afalo suka iske mai gidan kwance a doguwar kujera idanunsa alumshe da alama har yanzu yana cikin fushi kenan?, basu yimasa maganaba dan yanzu a wuya yake, jira yake wani ya tankashi ya sauke bala'in akansaba.
   Kiran sallahne ya tadashi daga kwanciyar dayayi, ko kallo basu isheshiba ya haye samansa, babu daďewa yasakko ya fice, suma zuwa sanan suna ďakunansu domin yin sallah.
     Bai dawoba sai isha'i, sanan sun fito falon, yashigo da sallama ciki2, suka amsa, sharesu yayi yawuce harya fara taka matattakalar benen aunty bily tayi 'karfin halin faďi yaya!!!, juyowa yayi yana kallonta batareda yayi maganaba fuskarsa amatu'kar ďaure kamar bai ta6a dariyaba.....cikin in ina ta ce, "abincifa??.
   Cigaba yayi da tafiyarsa ya ce, "na'koshi.
     Shiru kawai tayi dan tasan yau akwai matsala, bazai saurari kowaba agidan.
   Nurr ta ce, "aunty yazamuyi to??.
    Hummm Nurr yafa zamuyi haka yake kindai san halinsa tunda gida ďaya kuka tashi, idan har yay fushi saiya shafi kowa, yanzu ko munje bazai sauraremuba garama kawai mu 'kyalesa.
    Nurr tayi shiru dan itafa ba fushinsa bane ya dameta kawaidai tana tsoron karya faďama daddyne, bakuma koda yaushe tacika son 6atama mutum raiba.
    Haka suka ci abincin su biyu, daganan kowa tanufi ďakinta, har safiya baiko le'ko wajeba yana ďakinsa zuciyarsa cike da haushi musamman idan yatuna sanda saurayin yasha gaban Nurr tamkar zai rungumeta ya runtse ido da 'karfi tareda cije la6e (na ce, "humm su ya Mahmud akwai ďankaren kishi kamar Abdul ďina agari).

Dasafe ma sanda yafito sun gama shirya break, cikin shirin office yafito, babu ďakin wadda yay tunanin shiga, kai tsaye yanufi hanyar fita, da sauri aunty bily tasha gabansa haba yayanmu har yanzu fushi  ake damune??, yakamata ayafe mana hakanan ayi mana uzuri, harara yasakar mata ya ce, "kinga inajin kunyarki bilkeesu dan haka tashimun a hanya, yanda yayi maganar babu wasa akuma matu'kar ďaure fuska sai abin yabata tsoro ta matsa gefe ya fice.
   Ta window take le'kensa ya shige mota yafece fuuu, aunty bily taja ajiyar zuciya, tasan ya Mahmud akwai kishi kuma yasha nunawa akanta, amma awanan karon yafiya ďaukar zafi komi yasa (na ce, "auntynmu saboda yana matu'kar son Nurrin sane, shiyyasa ya tsananta kishinsa akanta...................




Luv u oll my fan's
©2017
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *