check your best novels here

Saturday 11 March 2017

SABON AL'AMAREE 14/18

[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE



BILKISA IBRAHIM
   {♡bilyn Abdul♡}



           14
                            
                                              
.......Yauda gobe sai ALLAH,, akwana atashi bayida wahala su Nurr sunshiga aji biyar amakaranta, ranarda su aunty badee zasuyi candy kuwa sunsha kuka kamar ransu zai fita,, suma har kuka sukayi amma yazasuyi haka rayuwar makaranta tagada, wasu sutafi wasu su shigo,, hakadai suka dangana suka barma ALLAH komai,, yanzukam rayuwa ta canja musu domin basuda wani gata a makarantar kuma dama 'yan aji biyar haushinsu sukeji saboda dukanda su badee sukai musu sun ďau alwashin ramawa akansu deena, gakuma 'kiyayyar dake tsakanin 'yan ss 3 da ss 2,.
   Duk tsoron dukan Nurr saita dake yanzu domin idan ta nuna tsoro rainasu za'ayi, babu 'karya suna dakuwa kamar jakuna, komai aka yayo sai kansu,, kodukan 'yan ss 2 za'ayi sainasu khairat yafi yawa, ranar kuwa akayi musu wani duka wanda yay sanadi tashin aljanun Nurr.
   Nurr ta sha'ke wuyan 'yar aji shiddan dake dukansu taita jibga kamar ALLAH ya aikota,, 'yan ss 3 suka rufu akanta suna duka,, datai kukan kura saita zubar dasu 'kasa suduka, dukan kan mai uwa da wabi tashiga yimusu,, aiko sun lallasu da'yar su deena suka shawo kanta ta ha'kura,, aljanin ya ce, "wlhy duk ranar dasuka sake dukansu Nurr saiya koya musu hankali fiye da yanda basa zato.
   Wanan lamari har gaban pc yakaisu,, pc tabawa 'yan ss 3 rashin gsky takuma gaya musu su Nurr ba 'kannen su badee bane, itace dakanta ta haďasu dasu,, daga yau aka 'kara dukansu Nurr batareda sunyi laifiba to wlhy mutum saiya gane kurensa.
   Tundaga ranar su deena suka samu 'yancin kansu indai kaga an dokesu to za'a doki kowane, wanana ne yabasu damar tsula tsiyarsu suma amakatantar duk 'yan ss 2 babu masu ajinsu Nurr,, sune manya masu aji gakuma 'ko'kari, komai nasu na girmane, su kansu wasu 'yan aji shiddan tsoronsu sukeji musammanma na ďakinsu.
   Yaranfa suna shanawa wlhy.

KADUNA 
  A kd kuwa lamura sai ahankali,, ya Mahmud yana cikin damuwa dominkuwa har yanzu idan aunty bilkee tasamu ciki saiya zube dayakai wata uku,, kwata2 cikin ya'ki zama, har matar ya fahad ta haihu sargaďeďen đa namiji,, sunan daddy suka saka masa suna kiransa da Abdul.
   Tun ya Mahmud yana nuna rashin damuwa da lamarin har abin yafara caccakar zuciyarsa,, to ayanzu dai tana ďaukeda ciki na huďu muna kuma addu'ar ALLAH ya inganta.
   Wannan hutun su ya mubarak ne sukaje ďaukar su Khairat daga makaranta, sundawo sunsha hutunsu kamar yanda suka saba, sunyi ziyara gidajen dangi dahaka hutunsu ya 'kare suka koma dan yanzu sun dake harma wani son makarantar sukeyi.
         To awanan karonma bata canja zaniba domin aunty bilkee ta'kara yin 6ari harma na 'yan biyu,, ya Mahmud harda kuka yayi,, yabani tausayi kwarai da gsk amma yaza'ayi haka ALLAH ya 'kadarto masa,, yana matu'kar son 'ya'ya amma ALLAH bai hukunta su iso duniyaba bama sukai wata huđu aciki,, wanan karon doctor yabashi shawarar ayimata wankin ciki ko ALLAH zaisa adace,, ya Mahmud baiyi gardamaba yabada umarnin ayi mata, likitoci sunyi mata wankin ciki suka bata kuma maginguna.
   Haka ya Mahmud yacigaba da tattalinta batareda yarage ko kwayar zarra asontaba saima 'karuwa da sonnata yakeyi acikin zuciyarsa, itama tana son mijinta sosai shiyyasa take bashi nagartacciyar kulawa ta musamman, ya Mahmud yana 'ko'kari wajen danne damuwarsa ta rashin ďa dukda wani lokacin aunty bilkee tana harbo jirginsa saidai tayita kwantar masa da hankali da bashi labaru masu daďi dahaka harya saki jikinsa.
    Hakama mama tana damuwa da al'amarin na ďan nata, dan tasanshi da son yara tunyana 'karami,, takan ware dare guda wajen ro'ka masa ubangiji akan samun haihuwa, takanyi azumin alhamis da litinin domin yi masa addu'a da mi'ka 'ko'kon bararsu ga ubangiji,, tasan duk cikin 'ya'yanta tafison Ya Mahmud tanayin kawaicine kawai irinna al'ada.
   Awanan karon kusan tare suka 'kara samun ciki da aunty ikilee matar ya Fahad,, ya mahmud yayi murna dukda zuciyarsa tana rawa,, yayita addu'a ALLAH ya inganta masa wanan,, cikin amincin ALLAH tawuce wata uku harta shiga na huďu,, na huďuma ya shuďe aka shiga na biyar dangi sunata murna dan ganin wannan karon da alamar nasara.
   Wani daren juma'a ta tashi da matsananncin ciwon ciki,, arikice ya Mahmud yafarka,, tallafota yayi zuwa jikinsa yana mata sannu,, ya ce,, "bilyna miyake miki ciwone??, cikin kuka tanuna masa cikinta,, ya shiga ruďani sosai gashi dare yayi,, jiki na rawa yakira doctor ďinsu cikin sa'a yasameshi, cikin ruďewa yake masa bayanin damuwarsa, doctor ya ce, "karka damu ina zuwa.
   Minti kaďan doctor ya iso, sanda yazo har jini yafara zuba ajikin aunty bily,, taimakon gaggawa likita yashiga bata amma ina yauma antaki rashin sa'a domin cikin yazube,, ya Mahmud yadafe kai yana hawaye amma ya zaiyi,, likita yashiga lallashinsa da bashi baki,, da'kyar yayi shiru daga kukan dayakeyi,, ya taimakawa likita suka gyara aunty bily dabatasan inda kanta yakeba,, 'karin ruwa yasaka mata sanan doctor yanufi gida,, shikuma ya Mahmud yayo alwala yashiga mi'ka kukansa ga ALLAH subahanahu wata ala.

Awanan karonma su Nurr sunzo hutu saidai bashida yawa,, suka gama kwanakinsu suka koma, daga wanan hutun sune zasu shiga aji shida.
   Tafiyarsu babu daďewa matar ya Fahad ta haihu mace, aka saka mata sunan mama suna kiranta da Farha,, anyi shagalin suna babu laifi Alhamdllh.
   Ya mahmud yataka rawar gani awajen sunan,, kusan kullum Abdul yana gidansu, gata sosai ya Mahmud yakema yaron jiyake kamar shine ya haifeshi acikinsa,, shima yaron yasaba dasu sosai.
   Haka rayuwar take gudu, bayan cikin daya zube aunty bilkee tasake samunciki sau biyu yana zubewa zuwa sanan ya mahmud yama gama fidda rai.
    Lokacin dana takwas yazube sai likita yakirashi suka zauna,  doctor ya ce, "Alhaji mahmud gawata shawara mana.
   Ya mahmud ya ce, "inajinka doctor karkaji komai kasanar mini,, likita yacire gilas ďin idonsa yana kallon ya Mahmud,, Alh Mahmud kayi ha'kuri inaga yakamata mu ďaure mahaifar matarka ta huta,, bincike ya nuna mana mahaifarta batada 'karfin dazataa ri'ke ďa, shiyyasa da cikinta yafara girma saiya zube saboda yafara nauyi,, gashi kuma kana yawan takura mata a 6angaren auratayya.
   Shawarata kuwa itace yakamata ka 'kara aure, arikice ya mahmud yaďago yana kallon doctor, doctor ya jinjina kai haka nake nufi ka 'kara aure domin naga kana matu'kar son 'ya'ya,, kuma hakan zai taimakawa matarka wajan samun hutu,, kaima zai taimaka maka wajen samun mai biya maka bu'kata yanda yakamata, idan kanada mata biyu zaka ringa raba musu kwana kaga karage mata nauyi kenan,, kuma idan da rabo ita zatazo ta haihu maka, dan haka ina mai baka shawara dakayi nazarin maganganuna insha ALLAHU zakaga fa'idarsu,, itama  bamu fidda ran wataran zata haihuba amma gsky zamu barta tahuta sosai.
      nariga nayima mahaifinka bayanin komai ďazu, domin kai kana cikin ruďani sanan.
    Ya Mahmud ya zaro ido doctor miyasa ka gayawa daddyne??, doctor yay murmushi saboda hakan yadace aii.
   Shiru ya Mahmud yayi yana juya maganganun doctor shikam gsky babu maganar 'kara aure acikin tsarinsa,, baima ta6a mafarkin hakaba,, toshi idanma zai 'kara auren wazai aura?????????????.......................


luv u oll my fan's
2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE



BILKEESA IBRAHEEM
    {♡Bilyn Abdul♡}



WANAN page ďin nakune sweet sister's Reefat yahya & maman usseey, AL'KAIREEN ALLAH ya kaimuku har gadon barcinku, nagoda da 'kaunarku gareni ALLAH ya 'kara mumu baseeeeeera my darling's .


              1⃣5⃣
                
.....Tunda aka sallamosu daga asibiti suka dawo gida ya Mahmud yakasa nutsuwa da magamganun doctor,, abu ďayane yake sakashi fargaba shine daddy da doctor ya ce, "yafaďamawa,, dukda har yanzu daddy baita6a yimasa maganarba amma tabbas yasan yana sane kuma duk daren daďewa saiyayimasa,, yasan halin daddy sarai akwai basar da'abu,, saiyayi kamar basan kana cikin wani haliba sai ranaďaya yabaka umarni kuma dole kabishi, dan mutumne mai magana ďaya maikuma tsayawa akan ra'ayinsa.
   Aunty bilkee dake zaume tun ďazu agefen ya Mahmud amma bai saniba saboda yana cikin duniyar tunani,, ya ďago da sauri yana kallonta, ta ďan langwa6e kanta gefe itama tana kallonsa cikin taushin murya ta ce, "haba my handsome mikake tunani haka??, miye damuwarka??, saida yaja numfashi tareda juyowa yana fuskantar ta sosai, yaďanja hancinta yana murmushin ya'ke babu komai bilyna kawai dai ina tunanine akan office waniđan aikine yashamin kai shine nake tunanin mafita.
    Hannunsa takamo tana murzawa ahankali, ayya my handsome ka kwantar da hankalinka kaji,, nasan insha ALLAHU komai zai warware, kaifa gwarzone a 6angaren komai na rayuwa, dayawa ana alfahari dakai acikin family ďinmu saboda kwazonka da dauriya.
    Ya sumbaci hannunta data ri'ke nasa,, ngd my bily nagode da irin kulawar dakike bani ALLAH ya tsawaita rayuwarmu harmuga jininmu muma a duniya,, amin tafaďa tareda kwanciya saman cinyarsa, my handsome!!.
   Na'am bilyna yaya akayi ne??, dan ALLAH yaushe zamuje ganinsu Nurr makarantane?? Wlhy ina sha'awar sake zuwa school ďinnan dan tana burgeni, kanta yashafa tareda faďin nidai inson zuwa kano ranar litinin inaga dagacan zan biya nagansu tunda tafiyar mota zanyi,  kekuma kiyi ha'kuri sai wani hutun tunda kinga dasun dawo sai kuma candy kenan,, murmushi tayi ta ce, "ALLAH yakaimu darai da lfy,, kai gsky duniya tana gudu yanzunan harsu khairat sun shekara uku amakaranta, kenanfa aurenmu shekara uku kenan??, ya Mahmud ya ce, "hakane gashi har Fahad yanada yara biyu, ai abun kamar yaune.
   Hakane kam ALLAH dai yasa mucika da imani,, amin my bilyna ya mahmud yafaďa yana sumbatar kumatunta.

D/Z
     Su Deena ana makaranta yanzukam sune suke shanawa, Nurr itace shugabar ďalibai tayanzu, suma su khairat duk anbasu ďankwali,, sumafa suna tsula tsiyarsu gsky,, dan sun maye gurbin su badee nada,, su harma malaman shakkarsu sukeyi, gashi yawancinsu duk so sukeyi suyi soyayya dasu musamman ma Nurr dantafi su khairat 'kyau dukda suna matu'kar kama dajuna.
    Yau monday gaba ďaya Nurr sukuku ta tashi, ko wajen tare bata tsayaba, dan yau batajin  dukan kowa, tawuce aji ta kwanta,, malam Mahfuz 'kya'ky'kyawan saurayi mai kwarjini yadaďe yanason Nurr kuma bai 6oye mataba yafito fili yasanar mata, itakam ko kallo bai ishetaba dan haushima yake bata,, ya 'karaso gate ďin 'yan ss3 suka shiga gaisheshi wasukuma suna masa kwarkwasa kamar yanda suka saba,, ya kai dubansa ga khairat yana faďin yau banga shugabar ďalibaiba kota manta yau duti namune nida ita??, khairat ta ce, "malam bata mantaba dan tare muka fito inaga batajin daďi shiyyasa ta wuce aji,, amma karka damu zamu wakilceta.
   Okey babu damuwa amma kusanar da'ita ta daure tafito anjima dan bazaiyuwu ace ba'a ganin mai duti ba,, to malam za'a sanar mata deena tafaďa tana binsa da harara, dan sunsan shishshiginsa ne yasa aka haďashi duti da Nurr.
   Koda aka fito break Nurr bata fitoba tana zaune a aji abinta saidai daka kalleta kasan batada walwala, tana zaune saiga Sajeeda marwan,, Sajeeda marwan itama 'yar ss3 ce, tana bala'in son malam Mahfuz kamar ta kashe kanta, tun tana 6oyewa harta kasa, tafito fili ta nuna masa amma saiya nuna mata shifa Nurr yakeso,, wannan dalilin yasa take matu'kar jin haushin Nurr jitake kamar ta haďa wuta ta jefa Nurr,, tasan Nurr tafita komai 'kyau, ilimi, gata, gayi itace shugabar makarantar kuma pc da malamai suna matu'kar jida ita dan hazi'kar ďalibace mai hankali da Nutsuwa.
    Tayi tsaye kyam akan Nurr dake zaune takifa kanta akan desks,, amma ba barci takeyiba, jin kamar mutum akanta yasata ďago,, ganin sajeeda tsaye saita yatsine fuska tana faďin kekuma kafiya zakizo ki tsaya min akai kamar naci miki bashi???,, Sajeeda ta 'kara tamke fuska saikuma ta tsartar da yawu tana wani jijjige2n jiki kamar wadda take afilin gasar rawa,, Nurr ta ta6e baki tareda maida kanta takwanta,, dasauri Sajeeda ta finciko hijjabin Nurr,, Nurr tayi mata banza dan batajin yin hayaniya yau,  itama sajeedar tasan Nurr sarai ba kanwar lasa bace.
    Ganin Nurr ta'ki kulata saita dan'kara mata KULLI abaya (dundu)jikake tiiiimmmmm!!!!!!.
   Da sauri Nurr taďago idanunta da sukayi jajur saboda 6acinrai,, zuwa sanan 'yan ajin sun fara dawowa,, jikin Nurr yafara rawa, ita kanta Sajeeda ta tsorata kwarai da gske, su khairat suna gefe suna kallo dan suma shigowarsu kenan, tabbas sunsan aljanun Nurr sai suntashi dan tun ďazu ranta yake a6ace,, wata muguwar sha'ka tayima Sajeeda ta ďagata sama ta faďa da bangon class ďin, saman cikinta ta haye tashiga jibďa,, duk wanda yakalli Nurr yasan ba'ita take wanan aikin ba dan Sajeeda tafi Nurr girma sosai,, Nurr yar karamace kodayake ance faďa azuciya yake ba'a jikiba.
     Adai2  wanana lokacin kuma ya mahmud ya iso cikin makarantar,, sunata gaisawa da malamai dayake sun sanshi sosai saboda yawan zuwan dayakeyi, gashi kuma indai yazo saiya yimusu alkairi sosai.
   Dukanta take sosai kamar uwarta dama anfaďawa su Nurr iya dambe ne,, dagudu wasu 'yan ajin sukaje kiran malamai , dagudu suka 'karasa staffroom suna  hakki,, malamai suka fara tambayar lafiya,, cikin hakki Fadeela Ahmad ta ce, "malam Nurr ce suke faďa da sajeeda kuma da alama ba Nurr bace dan gatacan tasha'keta zata kashe...... .aii kafin su'karasa faďa malaman sun rufo da gudu sai ss3a.
    malam Mahfuz ne yashigo shida ya mahmud saikuma malam Faruq da malam shazali,, ya Mahmud yashiga 'ko'karin fincike Nurr daga kan sajeeda danta mata wata muguwar sha'ka sai kakarin mutuwa takeyi nakula tafarajin kamshin lahirama........................



luv u oll my fan's
2017
[12/02 15:10] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE



BILKEESA IBRAHEEM
     {♡bilyn Abdul♡}


16
           
                              
                                                
...........Duk 'karfi irin na namiji amma ya mahmud yakasa fincike Nurr daga kan Sajeeda,, ya daddage ya wanka mata mari, da sauri ta saki sajeedar takoma ta sassan'kame kamar gawa,, da hanzari ya mahmud yatarota tafaďo jikinsa, ya rungumeta yana girgizata ahankali yake ambara Nurr! Nurr!!!, amma Nurr ko motsi tagaza yi, malam Mahfuz ya ce, "inaga aďauketa zuwa staffroom kawai.
   Wasu daga cikin ďaliban sukazo zasu ďauki Nurr amma sai ya mahmud yaďaga musu hannu batareda yayi maganaba, cak yaďauketa kamar wata jaririya to dama Nurr ďin 'yar fit ce,, su khairat suka take musu baya,, itama sajeeda saita mi'ke jiki asanyaye tana shafa fuskarta data kumbura tayi dam saboda duka, malam shazali yadaka mata tsawa kiwuce akace mara mutunci kawai wlhy nasan ko rantsuwa nayi bazanyi kaffaraba kece kika jata, Sajeeda tawuce tana shar6ar hawaye.
   Barandar staffroom suka nufa,, tabarma aka shimfiďa ya mahmud yakwantar da ita sanan yanemi gefenta yazauna,, malam faruq ya ďakko alkur'ani yafara karatu, yadaďe yanayi kafin ta motsa, tafara fisge2 kamar yanda tasaba, ya mahmud yari'keta yana tofa mata addu'oi shima,, zuwacan tasaki wata 'kara tareda yin atshawa mai 'karfin gask, saikuma jikinta yayi sanyi tayi wani lagwaf, ya mahmud yasake jawota sosai zuwa jikinsa yacigaba dayimata addu'a,, bayan kamar minti 30 saita buďe idanu akan ya Mahmud,, da sauri ta rungumeshi tana rusar kuka mai tsuma rai,, shiru yayi yana kallonta batareda ya ce, "komaiba suma su deena suna tsaye suna hawaye, ya Mahmud yaďagota yana share mata hawaye to kukan ya isa hakako??, ahankali tashiga sassauta kukan, su deena sukazo suma suka zauna kusada ya mahmud suna gaisheshi,, ya amsa yana tambayarsu ya karatu sukace alhamdullah, ya kalli Nurr da fuskarta taďan kumbura anya Nurr kina amfani da magungunanki kuwa??, kai taďaga eh yaya ina amfani dashi wlhy, amma yaya yaushe kazone wai??,, yanzu nazo natarar kina jibgar 'yar mutane wato a bodin ďimma bakubar halinkuba ko??.
   Cikin rashin fahimta take kallonsa ta ce, "yaya aimu bama faďa dakowa  yanzu,, ya mahmud ya harareta bayanzu kika gama faďa da wataba,, kai ta girgiza masa wlhy yaya banyi faďa dakowa ba, nifa ina ajima ina barci saiyanzu nafarka naganni awajenka.
    Shiru yayi domin yagano bama da'ita akayi faďanba kenan, ALLAH dai yabama 'yar 'kanwar tasu lafiya kawai zaice, nan sukayi 'yar hira sanan yabasu abinda yakawo musu sukaita masa godiya danshidai baya zuwa wajensu hannu rabbana,, shiyyasa basu ta6a tashi basuda abunda zasuciba, abincin makaranta kuwa saisun gadama sukeci, idan aka kusa hutu har 'kyautar kayan abincinsu sukeyi.
   Yabasu kuďu masu yawa kuma sanan ya ce, "bari yatafi dan yanada mitin akano 'karfe uku,, yanafata karfe biyu da ravi tayi masa akano saiya huta na rabin awa kafin sushiga mitin ďin.
    Hannu suka shiga ďaga masa bayan yayima malaman sallama tareda yimasa fatan alkairi da sauka lafiya.

Bayan tafiyar ya Mahmud aka kira 'yan ajinsu Nurr suka faďi abinda suka sani,, har malamai suka gano laifin Sajeeda ne,, malam Mahfuz dakansa yayma sajeeda bulala goma,, tareda gaya mata maganganu masu zafi akan Nurr, daganan aka sallamesu suka dawo aji, dama ita sajida 'yar ss3b ce danhaka saita wuce ajinsu.

Haka akacigaba da damawa yau fari gobe tsumma har hutu yazo kowa yakama gabansa,, wanan karonma su ya Mustapha ne sukazo ďaukarsu, sunyi farinciki da ganinsu, bayan gaisuwa da murnar ganin juna suka ďauki hanyar Kaduna,, cikin nasara suka isa da wuri kuwa.

WASHE GARI.
     Tunda suka shiga gaida daddy yake binsu da kallo tabbas lokaci yayi dazai zartar da hukuncin dake zuciyarsa, saidai yana fargabar abinda zaije yadawo,, amma tabbas zai aikata umarnin marigayi mahaifinsu Alh mutallaf,, yasan akwai gagarumin tarna'ki dazai biyo baya amma yazaiyi dolene yacika al'kawarin daya ďauka kodan samun alkairi daga albarkar iyayensa,  yafitar da numfashi mai 'kargi daga hancinsa, insha ALLAHU zai zauna mitin da sauran 'yan uwansa guda goma sha uku danjin abinda yadace akan SABON AL'AMAREEn dake shirin faruwa a family ďin nasu,, yana fata ALLAH ya yayyafama abin ruwan sanyi kawai......
    Nurr ta katse masa tunani dafaďin daddy lafiya tunanin mikakeyine haka??, murmushin ya'ke daddy yayi, ya ce,, "ina tunanin yanda naga yarana sun girma, kamar basu bane aka kai makaranta suna kuka dafaďin basaso.
   Fuska suka rufe suna dariya , ahaka mama tashigo falon tasamesu, bayan sun gaisheda daddy itama suka gaisheta sanan suka mike suka fice, mama tabisu da kallo itama yana murmushi kamar yanda daddy yake binsu danasa kallon.
   Bayan shige warsu daddy yaja ajiyar zuciya tareda faďin hajiya lokaci yayifa da komai zai fito fili, "lokaci yayi da za'a buďe wani sirri a family ďinnan, lokaci yayi da SABON AL'AMAREE zai bayyana.
   Arazane mama take kallonsa, tuni hawaye sun wanke mata fuska cikin sanyin jiki tanemi guri tazauna,, taďago kai tana kallon daday idonta cike da kwalla, niko wlhy Alhaji saza'abar abunan danayi farinci mai yawan gsk,, banason tone2nan wlhy,, dan ALLAH kubar zancennan karku bari wani SABON AL'AMAREE ya 6ullo acikin family ďinana, tunda manyan 'ya'aynku ma basu san komaiba akai,, ta'kare maganar da sakin kuka mai tsuma rai.
   Rungumeta daddy yazo yayi yana share mata hawaye,  gsky kika faďa amma yazama dole sirrin 6oye yafito fili,, dolene SABON AL'AMAREE ya bayyana kodan cikar burin mahaifinmu danakeson yi,, ina son cika al'kawari nawasu shekaru abaya dana ďauka,, kedai kitayamu da addu"ar samun sau'ki akan 'kurara dazata tashi awanan family. Koni banason faruwar wani SABON AL'AMAREE amma hakan yazama dole kodan 'kyautata rayuwar waďanda abin yashafa.
    Faďawa jikinsa mama tayi tana cigaba da kukanta shikuma yana aikin lalashi.

Haka su Nurr suka gama hutunsu suka koma,, amma har yanzu babu abinda yafaru a family ďin dan daddy yakasa buďe sirrin komai,, yama kasa 'kir'kirar mitinďin dazaisa komai yafito fili, itama mama dayake bataso bata ta6a ďaga masa maganarba bare ta 'karfafa masa gwuywar fallasa SABON AL'AMAREE.
   dahaka rayuwa taci gaba da shurawa su deena suka fara zana jarabawar ssce ďinsu,, cikin hukuncin ubangiji suka gama cikin nasara,, ranar mota biyar dangi sukayi wajen ďakkosu domin kuwa daga kansu aka fara bodi, sadda suka iso gida kuma suka tarar da gagarumin farty da yayunsu suka haďa musu,, lalai gurin ya 'kayatar anci ansha ankuma 6ararraje dan 'yammatan uku sunci rawa sosai,, babu wanda ya hanasu domin ranar farin cikinsune da dukkan masoyansu.
      Saida sukai kwana biyu suna hutun gajiya kuwa,, daga baya suka warware suka cigaba da harkokinsu nayau da kullum tunda yanzu suna a free, zan iya cewa kusan har yazu akwai sauran rawar kai atareda su Nurr, amma sunďan sasaauta bakamar daba,, sunkoma islamiyyarsu tunda yanzu babu boko, komai yana tafiya normal saidai daddy abubuwa da dama sunacin zuciyarsa ga damuwar ya mahmud gakuma babban al'kawarin dake kansa na fallasa asirin dake 6oye, har wani ďan ciwo yayi na kwana bakwai dole yaje yaga likitansa dake 'kasar india.
       A6angaren ya Mahmud kuwa yana cikin damuwa tun yana 6oyewa har matarsa tagano shi,, itama tabbas abin yafara damunta dan haka taje tayi bincike agurin likitansu,, bai 6oye mata komaiba gameda bayanin dayayima ya mahmud ashekaru uku dasuka wuce,, tayi mamaki kwarai da gsk dan bai ta6a gaya mataba koma nuna mata bai ta6ayiba saidai talura yana cikin damuwar rashin samun haihuwa,, ashe angayamasa hanyar dazaibi yamagance matsalarsa yaki yabi,, tabbas yanzu zata koma gida saidai komai tafanjama fanjan dan bazata iya dawwama cikin 'kunci da damuwar rashin 'ya'yaba dolene yanema musu mafita tunkafin guru ya kure musu kowa yasan matsayinsa tofa akwai matsala kenan aunty bilkee kardai kiyi mana butulciiiiiiiii!!!!!!!!!!......................









luv u oll my fan's
©2017
[12/02 18:35] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE



 BILKEESA IBRAHEEM
     {♡bilyn Abdul♡}



WANAN page nakine dear manshat ALLAH ya inganta miki abin farincikin daya samemu, ALLAH yakaimu da rai musha shagali



17
           
                             
                                               
..........Tunda taturo 'kofar falon tashigo yake binta da kallo tamkar yau yafara ganinta,, itako ta 'kara ďaure fuska kamar wadda tahaďu da ma'kiyinta,, ko kallo bai ishetaba tawuce bedroom ďinta,, harta 6acema ganinsa yana binta da kallo ya tsurama 'kofar ido yana mai mamakin canjawar da bilkeesu tayi a yau, kodai wani abu akayimata??, ya mi'ke jiki a sanayaye ya rufa mata baya zuwa ďakin.
   Yatura 'kofar bedroom ďin yashiga tana tsaye tana cire kaya, bayanta yatsaya tana 'ko'karin cire brah ďinta, yaďora hannunsa akan nata ya cire mata,, bata cemasa komaiba taja zani ta ďaura ko kallon inda yake batayiba tashige bayi abinta tabarsa tsaye zororo.
    Bakin gado yazauna yana jiran fitowarta dukda lamarin nata yafara 6ata masa rai amma saiya danne tunda bata ta6a yimasa irin hakaba,, yanada tabbacin akwai abinda ya 6ata mata rai,, yazame yakwanta idonsa yana kallon fankar dake juyawa aďakin,, tafito daga wankan tahau shiri bataredata tuna akwai mutum aďakinba,, saida tagama shirinta sanan yatashi zaune yana kallonta, cikin muryarsa mai daďi ya ce, "bilyna minene matsalarki ne??, ta ďago daniyyar yimasa bore amma saitaga yayi mata wani kwarjini na musamman,, ya Mahmud yanada kwarjini fuskarsa tana nuna alamun tsoratarwa.
   Ta haďiye maganar datayi niyyar faďa, tasowa yayi ahankali ya kama hannunta suka nufi bakin gadon, batayi yun'kurin kwacewaba saima wasu 'yan kwalla dasuka taru mata a gefen idonta, ya juyo da'ita suna fuskantar juna, bilyna minene yake faruwa? kifaďamin kinsan banason irin waďannan halayen suna sauri fusatani cikin sigar lallashi yake wanan furucin.
   Ta matso hawayen dake idonta cikin rawar murya ta ce, "my handsome dama haka kukayi da doctor ashir amma shine ka 6oyemin, kafiso muyita rayuwa ahaka babu yara kenan??, nida kai duk munsan muna cikin damuwar rashin samun haihuwa amma kasan mafita ka 6oye min?, ya mahmud kana sona kuwa???.
        A tsanake yake kallonta dan yarasa gane inda maganganun nata suka dosa shin na amincewane??, kokuwa na bujirewane??, ta'kara jeho masa tambayar???? 
     baka sona ko???, 
da sauri yake girgiza kai alamar A'a, 
   Ta ce, "to miyasa ka 6oyemin sirrinka??.
   Yaďan gyara zamansa sanan ya ce, "ba 6oyemiki nakeyiba bily kawaidai bazan iya aikata abinda yace bane.
   Bily taďan murmisa to aiko indai kana bu'katar zama dani dolene ka 'kara aure.
  Cikin mamaki yake kollonta domin jin furicin bakinta, ya ďan cije le6ensa na 'kasa bily kinsan abinda kike faďa kuwa??,
     nasani my handsome kuma kaima kasan hakan shine dai2 kuma shine yadace.
  Shiru yayi yana kallonta, shiba wani abu bane yasa baya son 'kara aurennan ba, ila ita yake tausayi,, yaje ya auro wata ta haihu tazo tana mata wula 'kanci shikuma bazai juri hakaba.........ta katse masa tunani dafaďin mika yanke yanzu akan lamarin???
   Huci ya fidda daga bakinsa sanan ya ce, "toni bily idanma hakan ta kasance wazan aura??, kinsandai ba kula wata yarinya nakeyiba a family đinnan namu???.
         murmushi tasaki karka damu indai dan wanan ne mun gama magana da daddy nagidan ku, yasanar min yanada matar dazai baka ka aura!!, arazane yake kallonta ya ce, "bily yaushe kukayi wanan maganar da daddy??.
     taďan huro hanci tana faďin yauďinnan mana ganin dakayimin daga can gidan nake bayan naje wajen doctor saina wuce can, yafara girgiza kai yanaďan ja baya dajikinsa saikuma yay saurin dam'ke hannunta haba bilkeesu yazakiyi min haka danmi zakisaka daddy acikin wanan maganar?????!!!!!!,  ya'kare maganar cikin 'karaji tareda gitgiza hannunta da 'karfin tsiya, har saida ta rumtse idanu saboda zafi, ya wurga hannunta zuwa baya sanan yasake daka mata tsawa tunda kece zaki zaunamin da matar saikiyi saurin auromin ita aikin banza kawai!!!!!!!!.....yana kaiwa nan yafice afusace..
    Saman benen ya haura zuwa ďakinsa, saida yasakama 'kofar key sanan yafaďa saman gadon yana huci, (na ce, "lallai yau ran 'yan maza ya 6aci) kansa yadafe danjin yana shirin tsagewa wacece daddy yaza6a masa amatsayin mata??, shinwai mike damun bilkeesu ne??, ance mata suna gudun kishiya amma gatashi matar dakanta taje ta rakitoma kanta, yaja wani wawan tsaki jikake mtsoooow!!!!!!!!!,  yakula yarinyarnan batada hankali wlhy,, to inbanda hauka dakanki zakije kice asaka mijinki yayi miki kishiya wannan wane irin tunanine da ita????, (na ce, "tanada tawakkaline, sanan kuma kishiya aiba bala'i bace ga macen data gane).

Itako yana fita ta rushe da kuka dama kamar jira takeyi, saida tayi mai isarta sanan ta lallashi kanta tayi shiru,, mi'kewa tayi tanufi ďakinsa domin basa ha'kuri, tasan ya Mahmud yanada zafi sosai amma bai ta6a nuna mata 6acin ransa irin yauba, lallai yau tasan ta ta6oshi amma yazatayi hakan datayi shine dai2, shima wataran saiyayi alfahari da abinda ta aikata, idan ta ce, "bazai'kara aureba aita cutar dashi sosai,, domin shi mutumne maison yara, tunkafin suyi aure bashida hirar data wuce idan sunhaifi yara zayi musu kaza zai musu kaza,, hakama dasukayi aure,, to itako yazata tauye masa hakki tunda ALLAH bai bata nataba, ahankali ta 'karasa jikin 'kofar tashiga bugawa amma yayi burus da ita,, daga 'karshema saiya buga mata tsawa wai karta sake buga masa 'kofa idan bahakaba zai matu'kar bata mamaki.
   Zamewa tayi jikin 'kofar tana kuka, yanajinta, dayaga zata damesa saiya kunna tv yasa 'kara dayawa.
      Saida tayi kuka mai isarta sannan tami'ke takoma ďakin,, haka akacigaba da zaman doya da manja har kwana biyu, dayake weekend ne baya fita aiki,, babu abinda yake sakko dashi sai sallah,, baya cin abincinta baya shiga ďakinta, idan yashigo yaganta afalo saiya ďauke kai gefe,, itako harta sakko daga nata fushin,, fatantadai ALLAH yaganar da mijinta yafahimceta su daidaita da juna.
                   Nurr da deena suna ďakinsu Nurr tana kwance yayida deena ke gefenta tana karantamusu Novel mai suna "NAWAFF  NA bilyn Abdul" cikin waya,  deena tadasa aya ayayinda ta je 'karshen page, Nurr takalleta da sauri kai deena yakika tsaya kuma Novel ďinfa yafara sweet wlhy,, deena tayi dariya kai 'yammata maida wu'kar mana zan ďan sha ruwane, nikaina yanda nakejin daďin buk ďinan bazanso na tsayaba amma bani minti ďaya naje na ďakko mana fanta a firij, da sauri Nurr tami'ke tana faďin A'a yizamanki naje na ďakko mana.
   Kichin tanufa dan ita harma yunwa takeji, taduba babu abincin saita nufo saman daddy dantasan anan zata samu tabbas,, babu kowa a falon tagama waige2nta bataga kular abincin daddy ba, taďanja tsaki ita saima yanzu ta tuna baya 'kasar, da gudunta ta sakko,, jikake gafffff sunyi karo da mutum, taďago kai dasauri saitaga ya Mahmud fuskarsa tamkar baita6a dariyaba.....................




luv u oll my fan's
 2017
[12/02 21:54] bilyn Abdul: SABON AL'AMAREE



BILKEESA IBRAHEEM
    {♡bilyn Abdul♡}



18
            
                            
                                              
...........Tai saurin jabaya tana rawar jiki dan tsoro, cikin matu'kar ďaurewar fuska yake kallonta, ta dur'kusa tana bashi ha'kuri,, wani wawan tsaki yaja cikin faďa ya ce, "yaza'ayi kiganni tunda kina tafiya daka, useless kawai, kuma ban haku saka 'kananun kayaba anan gidan yafaďa yana zare belt ďin jikin wandosa,, tsale Nurr tafara tana yarfe hannu kamar wata yarinyar goye, yaya dan ALLAH kayi ha'kuri badan niba,, wlhy damuka saka bamu fitoba muna ďaki zaune,  yanzuma nazo đaukar abincine,, plzzzz karka dakeni dangirman ALLAH,, bai sauraretaba ya lafka mata ďaya a'kafafu, gashi wandon iyakarsa gwuywa saikuma 'yar mitsistiyar riga mai 'karamin hannu komai najikinta abayyane yake, ya 'kara lafka mata tabiyu saita ru'kun'kuneshi tana 'kara ihunta,, da sauri mama tafito dan da barci takeyi, ta 'karaso wajen tana daka masa tsawa,, "*k!!!!!! Mitayi maka zaka baro gidanka kazo kana dukar mini yarinya???, da sauri tabar jikinsa taje tafaďa jikin mama,, shiko du'kar da kai 'kasa yayi yana bawa mama ha'kuri.
   Ta kuma cewa wlhy ka kiyayeni dammi zaka tasamin yarinya gabane wai???, mitayi maka daga zuwanka gidan??, mama jibifa shigar dake jikinta,, kuma tuni na hanasu amma dan iskanci shine suka 'ki bari,, jibarta kamar ďiyar yahudawa..
    Toba ahankali akebiba, idan kana binsu da nasiha da lallashi aizasu bari ko??,, amma haka kawai da ranarnan tsaka kazo kana dukanta haba wace irin rayuwace wannan????.
    Har 'kasa ya rissina yana bata ha'kuri, yatashi yafice yana gallawa Nurr harara.
   Mama taja hannunta suka shige ďakinta tana mita.
   Su Nurr kam abin nema yasamu wai an cuci matar baqauye, tashiga rusa uban kuka mama tana lallashinta, daga lallashi barcin wahala yay gaba da'ita.
   Itako deena tana ďaki ta kulle kanta, tasan yana gamawa da Nurr kanta zai dawo, da sauri tashiga cire kayan jikinta itama ta canja da jallabiya ba'ka,, (na ce, "lallai wannandai badan ALLAH bane).
      Ya mahmud kam yana fita motarsa ya shige ya kifa kansa saman sitiyari, lallai yana cikin matsala, itadai Nurr ta taka sahun 6arawone kawai, ya huce haushinsane kawai akanta, motar yasakama key yabar anguwar. (Na ce, "ALLAH yatsare).
       Aunty bilkee zaune ta zabga uban tagumi itafa tagaji da fushin da ya mahmud yake da'ita, miyakamata tayine? dansu shirya tabashi ha'kuri amma ya'ki saurarenta, kozata koma tasanar da daddyne??, kai A'a wanan sirrinsune itada mijinta. 
      da sauri taďago danjin an ta6a 'kofar, ya mahmud ne ya shigo, fuskarsa ta fara kallo amamakinta saitaga fuskarsa asake take, ta taso da sauri ta kar6i ledar hannunsa, saida ya rungumota jikinsa ya manna mata kiss akumatu sanan ya ce, "i luv u my bily, ta ce, luv u too my handsome.
   Saman kujera suka 'karasa ta zaunar dashi sanan ta ajiye ledar tanufi firij, ruwa tabashi dan tasan bai cika shan kayan dreks ďinnanba, ya kar6a yana murmushi, saida ya shanye duka sanan ya dire kofin saman tebir ďin gabansa, jawo bily yayi saman cinyatsa yana faďin i miss u bilyna.
   Tai far da idanu tana faďin da gske handsome??, ya jinjina kai yana lumshe idanu, ta sumbaci 'kirjinsa ta ce, "ngd sosai handsome, kenan kadaina fushin dani??, murmushi yayi ya ce, "aii yanzu na fahimceki dan fitata 'kaddara tasani zuwa gida na sauke fushin akan Nurr.
   Ido ta zaro kai my handsome mitayi makane??, kibari kawai haushi tabani wlhy,, na hanasu saka 'kananun kaya amma sun'ki subari, to nikuma yau zuciyar akusa take shiyyasa na zaneta.
   Bily ta langwa6ar dakai gefe tana shafa sajen sa, ALLAH sarki Nurr ďin mama yau mijina ya ta6a lafiyar jikinki, amma mama bata nan ko??
  Tananan wlhy, aiko nasha masifa gashi mami bata nan bare ta karemini,, aikaima dai dabaka daketaba wlhy,, ya ďan ta6e baki kibari kawai gara dataji ajikinta gobe aii bazata sake sakawaba.
    Daga gurin aka fara soyayya (na ce, "bari nayi nan.).

Bayan kwana biyu daddy yadawo, daga tafiyar dayayi, awanan karon ya ďau alwashin fitar komai fili,, dan haka yabi dukkan dangi yasanar musu akan mitinďin dazasuyi sati mai zuwa.
      Su Nurr kam basu san hidimar da akeyiba.
   A 6angaren mama kuwa hankalinta atashe yake, nakula bata so a bayyana SABON AL'AMAREE da ake shirin fallasawa, amma babu yanda zatayi dolene gsky tafito kodan wasiyyar da ALH MUTALLAF yabari.

A yaune sati guda yacika,, gabaďaya manyan dangin sun hallara a tsohon gidan alh mutallaf inda yazauna sanda yanada rai,, duk shekara sai sun sake masa fenti dan anan suke mitin idan yataso kokuma wani taro .
     Falon yayi tsit kamar babu kowa,, Alh Usman ne yafara mi'kewa domin shine babba saida yayi musu addu'oi sanan yayma iyayensu da 'kannensu, ya'kara bin fukokin 'yan uwansa da kallo ďaya bayan ďaya suma shi suke lallo, yaja numfashi,, kuyi ha'kuri 'yan uwana domin yaune za'a taso da tsohuwar magana wadda tafaru abaya,, yaune SABON AL'AMAREE zai bayyana a zukatan 'ya'yanmu domin su basu san dashiba,, bakomai bane yasa hakan sai faruwar wani SABON AL'AMAREE dakuma son cika wasiyyar da mahaifinmu ya bari kafin yabar duniya,, bayyanar komai yanada amfani domin hakane zai bada ma'anar warware wasiyyar daya bari,, kowa yasan waye ALH MUSBAHU acikinmu? ???? Dan danan fuskokin kowa ya canja zuwa 6acin rai mai tsananin gsk...................tofa komiye dalilin hakan????,, kubiyoni kawai....... .................






luv u oll my fan's
2017
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *