check your best novels here

Wednesday 1 March 2017

NAWAFF!!! 55/58

[26/02 15:14] Abba Gana: ☆☆☆☆☆☆☆
 NAWAFF 
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM




Page55 & 56

.......A kwana atashi babu wuya gurin ubangiji, yaune sunan baby kuma taci sunan nana khadija, ubangiji ALLAH yaraya mana dukkan 'ya'yan da aka haifa ya albarkacesu.  
    Su yasmeen ansha shagali, kuma tanun bajinta itada habibinta, sunyima baby alkairi maiyawa harda iyeyen baby, mas'ud har yarasa bakin magana, yasan shida Nawaf sunruga sunzama 'yan uwa na jini, tamkar yanda mahaifansu suke tare, babu abinda suke iya 6oyema juna, ALLAH kuma ya dubesu ya azurtasu da mata 'kawen juna, masu kula dasu dason farincikinsu.
    Nawaf yayi hidimar da ko mas'ud bayi rabintaba awajen shagalin sunan,, duk da yasan Nawaf yafishi samun kuďi, dan gsky 'yan kwallo suna samun kuďi sosai, to amma ba kowa bane zai bigi jiki yayi maka hidimar kuďi a irin wannan lokaci da kowa yaďauki rayuwa dagashi sai 'ya'yansa.
   To mudai saimuce ALLAH ya sassaka da alkairi, yakuma maida kowa gida lafiya.
  Bayan kwana biyu da gama suna suka shirya tafiya saudia, amma harda su momcy da kowa da kowa,, papa ne kawai sai sun kusa dawo zaije su dawo tare.
     Nawaf dake kwance yana kallon yasmeen tana haďa musu kaya, ta ďakko manyan kaya wajen kala shidda zata zuba masa a akwatinsa,, ya ce, "fancy face waďan nan kayanfa, waye zai sakasu??, ta ce, "kai mana!!.
   Yatashi zaune yana faďin tab fancy face kina gani anan ma basakawa nakeba sai papa yayi magana bare acan,, tacigaba da zuba kayan tana faďin nikam ina son naga kasaka manyan kaya ba 'karamin 'kyau suke makaba, abinda manyan kayan nakama marabarsu da 'kananun kaďan ne, tunda ďinkunan sun cika fitat  kamar wani mace.
    Ya koma ya kwanta yana dariya, toni ahakamma ina sakawane kawai dan suna takurani wlhy,, hummm zamani yazo damuka ďauki Al'adar wasu muka yafama kammu, bayan kowa yasan kayan yarensa sunfiyimasa 'kyau.
     to nidai yanzu ni akema faďa kenan?, tokiyi ha'kuri kwananna zan koma saka manyan kaya sosai tunda kina so kinji.
    Yasmeen tayi murmushi aiko danafi kowa jin daďi, dan wlhy manyan kaya suna maka bala'in 'kyau, saidaifa kaine kake haskasu, ta'kare maganar da ďaga gira.
    Ya saki wani lallausan murmushi kina cikin aikina fancy face,, kinrigada kin gama mallakeni, nakula kofa aure na 'kara amarya baxata samu farincikina sosaiba.
   Dan danan yasmeen ta canja fuska, tamkar zata fasa ihu,, tabama Nawaf dariya amma saiya daure ya gimtse, ya ce, "yayadai naga kin 6ata rai, shiru tayi masa tana rufe akwatinsa dan tagama haďa kayan, ta saukeshi 'kasa tana hawaye,, Nawaf ya mi'ke ya sakko dan yasan shirun datayi ta sha'kane.
   Rungumota yayi tabaya dan ta juya masa baya, ya le'ko fuskarta saiyaga hawaye share2, cak ya ďauketa zuwa gado, ya kwantar da ita, shima yana gefenta,, yasa hannu yana share mata hawayen cikin kunnenta ya ce, "kinga nifa da wasa nake miki, plz kidaina bari hawaye suna 6ata mini 'kya'ky'kyawar fuskarnan tawa ni kaďai,, ta harareshi tana faďin maza ai dama kun iya daďin baki.
   Ya ce, "woow!! Ni na isa nayima fancy face ďina daďin baki, wlhy iya gsky ta nake gaya miki, kina kula dani, duk sanda nazo da bu'katata kina 'ko'karin biya mini, kina sakani farinciki, ba'kya barina da yunwa,, to idan na 'karo aure ita kuma mixata min??, bayan my xarah tana yimini komai,, ya sumbaci bakinta sorry dear kimin murmushi mana kozanji daďi.
   Yasmeen ta sake hararar sa, saiya rungumeta yana dariya, kinga bari na canja hanyar lallashin tunda sunada yawa, da sauri ta ce, "nikam naha'kura habibina,, yaďago fuskarta suna kallon juna ya ce, "ban yardaba,, ta ce, "to mizan maka ka yarda na ha'kura,, ya lashe la66ansa, tayi murmushi dan tasan abinda yake nufi, ta ce, "to rufe idonka, yarufe yana faďin sarkin kunya.
    Saida ta 'karema 'kya'ky'kyawar fuskarsa kallo, sannan takai bakinta kan nasa, wasu zafafan kissis take bashi, wanda shi kansa baisan zata iyaba, dan tamaso tafishi shi dayake malamin nata, da'kyar ta janye bakinta ta tashi tana dariya 'kasa2, dan ganin yanda jikinsa yay lakwas.
   Shikuma sai binta yake da idanunsa dasukayi jaa, gaba ďaya jikinsa yayi laushi, cikin dariya ta ce, "yakamata mutafi fa tunda kace bazaka barni na wuni acanba,, ALLAH inata zumuďin son ganin umma da abba da yaseer.
   Nawaf ya lumshe idanu tareda fitar da huci mai zafi daga bakinsa, ahankali ya furta to zokiji wani abu mana,, ta ce, "tab aina gane wayonka Alhaji, katashi kawai kayi wanka mu wuce kaga ni tunďazu nayi nawa,, yaďan cije le6e yana murmushin mugunta, ya ce, "to zomiyi wata shawara,, yanda yaďan haďe rai saita ďauka shawarar gsky ce, tanufi bakin gado ta zauna, ya ce, "karaso mana, A'a daga nanma ya isa..... kafin ta rufe baki yayi ciki da ita, na ce, "sai anjimanku,, dan naga soyayya za'a sha..

Ina zaune a waje suka fito Nawaf cikin manyan kaya hardasu hula, yasmeen kuma ta saka atamfa zani da riga ta ďora farin gyale, sunyi 'kyau sunata zabga 'kamshi abinsu, bayan sunyima su momcy sallama suka fito hardasu Abdallah za'aje, itada shi suna gaba su Abdallah suna baya.
   Yana cikin tu'ki saiya kamo hannunta, da sauri ta janye, yaďan kalleta, da ido ta nuna masa su Anwar,, ya ďan murmusa yana maida kansa saman titi, babu daďewa suka isa gidan.
   Da gudu yasmeen ta shige, da umma ta fara karo, tako rungumeta tana tsallen murna, umma ta ce, "ohni yasmeen wai sai yaushe hankali zai zomikine??, ta saketa tana turo baki gaba kai umma murnar ganinkufa nakeyi!!, to sannu da zuwa, yana ganki ke kaďai bayan kince tare kuke da mijin naki, lah umma suna 'kofar gida hardasu Anwar ma.
    Oh ni ALLAH ya shiryaki mamana shine kika barosu awaje, yaseer!!! umma ta kwala masa kira,, yafito da sauri yana amsawa, ganin yasmeen zaune saiya rungumeta suna murna,, umma ta ce, "kaje kashigo dasu Abdullahi........
    Bai bari umma ta 'karasaba yayi waje da gudu, acanma rungume juna sukayi da Anwar dan sunzama abokai tuni, ya gaida Abdallah da Nawaf, Nawaf ya ce, "o, yaseer kaima kayi girma wannan tsawo haka, yanzu wanda bai saniba saiyace ka girmi fancy face ďina.
    Dariya sukayi sosai yayinda yaseer yay musu jagora zuwa falon abba, yaja hannun Anwar suka fice,, dayake ansan da zuwansu an shirya musu abubuwan ciye2 afalon,, Abdallah ya hau cin abinsa dan dama abinci zaici Nawaf ya azalzalesa yafito.
    Nawaf ya ce, "ALLAH ya shiryaka Abdallah kaidai acicine ko??, Abdallah yay murmushi abii wlhy yunwa nakeji, kumafa ni gidannan kamar gidanmu nake ďaukarsa, duk abindazan iya yi aginamu zan iyayi anan, munzama ďaya da ablah aii..
   Nawaf yay murmushi danjin daďin maganar ďan 'kaninsa, ya ce, "hakane my dear bro's.
   Babu daďewa abba yadawo yazauna sukasha hirarsu dayake mutumne mai sau'kin kai, ga son jama'a.
   Umma maidai ta daure yau ta ajiye kunya ansha hira da ita,, yasmeen sai shagwa6a take zubama abba,, ya ce, "mamana har yanzu ba asan an girmaba ko??, ta shgwa6e fuska abba nafa daďe ban gankuba, kuma nasan yaseer yana nan yana ta6ara.
   Yaseer ya ce, "oh kina kishi danine aunty??, to aii yanzu lokacinane, ninake shanawa.
   Su Nawaf suka saka dariya, Anwar ya ce, "yaseer aii nima addu'a nake abii shima yayi aure abarni ni kaďai nasha shagwa6ata,, Abdallah ya hararesa ďan ba'kin ciki aiba yanzuba saina 'kara hutawa,, gaba ďaya suka saka dariya, duk sanda Nawaf da yasmeen suka haďa ido saiya ďaga mata gira, ita kuma tayi murmushi, hakadai sukasha hirarsu,, Nawaf ya ce, "yaseer yay 'ko'karin kar6o takardunsa zai nema musu makaranta shida Anwar a kasar Rasha, yaseer akaita murna da godiya, suma su umma sun masa godiya, suka ajiye musu alkairi maiyawa suka taho, yasmeen harda ďan kwallanta, tabama Nawaf tausayi,, amma sai ha'kuri duk macen duniya haka ta gada, bishiya agidanku, inuwa a gidan wasu.

Bayan sundawo gida sun gama duk abinda yake al'adar rayuwarsu suka kwanta dan dare mahuta bawa,, yasmeen tana kwance agefen hannun Nawaf ta ce, "shine zaka nemawa su yaseer makaranta amma ni ka lalata mini tawa ko??.
   Yashafa kanta yana murmushi to kina kishi da yaseer kenan dgsk??, babu wani kishi, to miye inba kishiba??, ke aii kingama karatunki,, keda kike cikin babbar makaranta mai cike da aikin lada.
   Ta 'kara gyara kwanciyar ta tareda rungumeshi, hakane habibina amma wlhy inason karatu sosai,, yajuyo ya rungumeta sosai karki damu my xarah zakicigaba da karatunki, harma saikince kin haji dan kanki, aikine kawai banyarda dashiba,, damun koma Spain zan nema miki makaranta.
    Ta 'kan'kameshi sosai tana murna, ta ce, "wlhy ni dama bana karatu dan na samu aiki, inasondai kawai nazama mai ilimi,, saura karatun islamiyya, kai yaka mata kazama malamina mijina.
   Yay murmushi waya gayamiki inada kwarewa anan?,, tab ai momcy tabani labainka tun kana yaro, da 'kiriniyar dakayi, ta ce, "min kai Anwar yagado shiyyasa ga yaronnan akwai ilimin addini, kumama kafishi,, dan haka kawai kabada kai..
   Ya ce, "shikenan tunda momcy ta fallasa ni insha ALLAHU zamu fara karki damu.
   Sunata 'yar hirarsu 'kasa2 har suka fara jin barci, sukayi addu'a suka lula duniyar barci.

Washe gari jirginsu ya ďaga zuwa 'kasa mai tsarki,, tarba akai musu ta mutunci, 'yan uwa cike da gida sunzo tararsu, aginda hajja  tsohuwa mai ran 'karfe suka sauka, yasmeen sai ware ido take yau gata a saudia, kasar da aka haifi (mafificin halitta ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) (TSIRA DA AMINCI SU 'KARA TABBATA GA SHUGABAN TALIKAI, MAI CETONMU AWATA RANA MAI CIKE DA HARGITSI DA RUĎANI,, ALLAH yasa muna cikin waďanda zai ceta, ameeeeen.)
    Lallai yasmeen ta yarda su momcy 'yan gatane, dan family nasu sunada kuďi da ala'ka mai 'karfi tsakaninsu da masarautar saudia,, abinci har rasa wanda zataci tayi, Nawaf sai dariya yake mata wai kartayi 'kauyanci,, itadai shiru tayi masa dan momcy da hajja suna kare mata,, bayan sunci sun 'koshi an gaggaisa da dangi, suka tafi dansu barsu su huta.
    Abin yabama yasmeen mamaki dataga an haďasu ďaki ďaya da Nawaf, itakam gsky tanajin kunya,, takira Abdallah ta ce, "yaje yasanar da momcy dan ALLAH araba musu ďaki, dariya Abdallah yayi, ya ce, "Ablah aiko bazasu raba muku ďakiba, dan momcy ma idan sukazo itada papa wlhy ďaki ďaya suke zama.
   Idanma na faďa momcy koroni zatayi, kiyi ha'kuri kawai kuyi zaman ku, dan shima Abii ba yarda zaiyiba,, yasmeen ta ce, "ALLAH inajin kunya Abdallah, Abdallah ya fice yana mata dariya.
    Bai daďe da fitaba Nawaf yashigo ita harma ta kwanta sannan,, ya shigo yana faďin sorry fancy face nabarki ke kaďaiko, ina wajensu isma'il muna shan hirar zuminci, bayi yashige yay wanka dan azatonsa tayi barci ne..
    Bayan ya fito yay shirin barci sannan tayi barcin gsky, sai kawai ya rungume matarsa suka hau barci.
       Da asuba tunda yatafi sallah bai dawoba, ta nanan zaune tana laximi saiga wata 'yar yarinya takawo mata dabino guda bakwai, ta ce, "taci, yarinyar ta burge yasmeen, ta zaunar da ita saman cinyarta tana tambayar ya sunanta, yarinya ta ce, sunanta fateema,, woow!! Yasmeen tafaďa, sunanmu ďaya kenan ko, yarinya ta ďaga kai,, duk suna magarne da turanci saikuma larabci ďai2 da yasmeen take sakawa wanda ta iya.
   Suna nan zaune Nawaf yashigo dagudu fateema taje ta tarosa ya ďauketa yaďaga sama, suna dariya, yazau bakin gadon yana yana tambayarta tasan yasmeen tace eh, nan sukaita hira shida ita da larabci, yasmeen ta ce, "o ni yar yarinya 'karama ta iya larabcun.
   Nawaf yay dariya kajifa xarah da wani zance, to itada yarenta , ke sanda kina 'karama baki iya hausaba, da yaren buzaye??.
   Yasmeen ta ce, "na'iya mana, sukai dariya gaba ďaya, ya ce, "fateema jeki amso min dabino nima, tako 'ki'kira da gudu amso dabino, Nawaf yasakko kusada yasmeen yaďan kwantar da kansa a bayanta, cikin taushin murya yace nifa da matsala nazo, yasmeen ta ce, "matsala kuma wace iri??, yay mata zobe da hannayensa cikin kunne ya gwar gwaďa mata suna cikin yin dariya fateema tadawo da dabino, da sauri yasaki yasmeen yana ďan sosa kai, tazo ta haye cinyarsa tana bashi dabinon abaki,, yasmeen ta ce, "kaganka kuwa kuna kama kamar kaika haifeta.
    Yay murmushi mai 'kayatarwa yana shafa kan fateema ya ce, "karki damu nima tawa tana nan zuwa,, yasmeen tai 'kasa dakai tana murmushi,, ta ce, "ďiyar waye??, Nawaf ya ce, "ďiyar uncle zaid ce, tunda mamansu tarasu wajen haihuwar 'kanin fateema aka kawosu nan wajen hajja.
   Ayya ALLAH yagafarta musu, wlhy harta bani tausayi, su nawane??, su ukune, akwai Nawaf mai sunana, sai muh'd Ariff,  sai fateema Wanda tarasu wajen haihuwarsa shima yarasu,, ALLAH  sairki ALLAH yaji'kansu.
    ameen fancy face.
      nansukaita hirarsu harsaida hajja ta aiko su fito suyi break sannan.
    Bayan sun kammala break suka ďau gayu, Nawaf yatafi zagawa da yasmeen gidajen dangi, gidansu ummuhabeeba ne na farko, antarbesu da mutunci, ummuhabeeba sai rawar kai ake anga masoyi, yayinda yasmeen ta cika tayi fam, Nawaf ne kawai ya gane halin datake ciki, dayaga zata fashe saiyace ta tashi su tafi,, ummuhabeeba kuma ta ce, "zata bisu itama tayo ziyara, tofa.
    Koda suka fito yasmeen saita shige baya, Nawaf ya ce, "k miye haka??, banza tayi masa bata amsaba,, itako ummuhabeeba ko a kwalar rigarta ta buďe gaban mota tashige abinta,, da hausa Nawaf ya ce, "fancy face wai miye haka kikeyi??, baki ta murguďa masa batareda ta tankaba.
   Ummuhabeeba ta ce, "my luv muje mana, wani haushi ya'kara turni'ke zuciyar yasmeen, wai agabanta akecema mijin ta my luv,, Nawaf yana kallonta tana hawaye ta madubu,, kai kawai ya girgiza dan baisan miya dace yayiba.
   Ummuhabeeba ta ce,, A'a yanaga kana nufar ka'aba damune?, muda zamu ziyara,, batareda ya kalletaba ya ce,, "aidama can zamuje nida fancy face, mungama ziyara sai kuma gobe idan ALLAH yakaimu.
     Ummuhabeeba taji haushi ta 'kara maimaita sunan wai fancy face, wani ďan 'karamin tsaki taja wanda Nawaf ne kawai yaji, itafa tabiyosune dan azatonta dangi zasu zaga tana kuma bu'katar dangi su tabbatar da soyayya takeyi da Nawaf, tasan dolene asakashi ya aureta.
   Amma shine dan wula'kanci yayo masallaci dasu.
    Yasamu guri ya tsaida motar, suduka suka fito fuska babu walwala, Nawaf ya ce, "lokacinma sallah yayi, saimushiga muyi sallah idan mun fito saina zagaya dake kiga guraren tarihi ko fancy face??,, bataso tabashi kunya agaban ummuhabeeba dan haka tayi far da idanu ta ce, "hakane habibina,, ummuhabeeba tayi gefe dakanta zuciyarta tana zafi,, yayinda yasmeen ta harari Nawaf,, yay mirmushi yana mata jinjin.
    Haka suka shiga sukayi sallar la'asar,, bayan sunfito yashiga nuna mata wajajen tarihi hannunsa yana ri'ke da nata,, daga baya ummuhabeeba ta ce, "tagaji ya maidata gida.
    Ya kalli agigon hannunsa yana murmushi, aii inaga mu bari muyi sallar magriba kawai dan ta gabato, zata iya riskarmu a hanya.
    Badan tasoba dole ta ha'kura sukayi sallar magriba accikin masallacin sannan ya maidata gida suma suka koma inda suka fito, yasmeen tanata wani zuzun6ura baki, ita adole kishi ya motsa.....................










©2017




bilyn Abdul
     Mrs Abdus'salam
          luv u oll my fan's
[26/02 15:14] Abba Gana: ☆☆☆☆☆☆☆
 NAWAFF 
☆☆☆☆☆☆☆







NA BILKISA IBRAHIM



Page57 & 58

.......Nawaf yanaso yay dariya amma saiya gimtse, idonsa na kan titi ya ce, "matar NAWAF SA'EED MODEBBO ya yadai??.
    Yasmeen taimasa banza kamar bata jishiba, yay murmushi tareda kamo hannunta ďaya ya rumtse anasa, yana tu'ki da ďaya, yaďan kalleta kaďan yanda taketa zum6uro baki saida ya dara,, ya ce, "waishin yazanyi da shagwa6ar fancy face ne yayinda yarana sukazo duniya??, sai asannan ta kalleshi ta murguďa masa baki, ya sake murmusawa dan yaganta ta madubi, antuna baya kenan yafaďa yana shiga kwanar dazata sadashi dagindansu hajja.
    Ta zame hannunta daga nasa tana cewa kadaiji dashi na ummuhabeeba,, tofa harkin sadakar dani fancy face, lallai kinason ummuhabeeba wannan irin 'kyauta da rana tsaka, aiiko muna sauka zan kirata na sanar mata kin barmatani tasamu miji a sanga.
   Yasmeen fa ta sha'ka da yawa danhaka tayi tsit, yanayin parking tafice batareda ta jirashiba, a'katon falon gidan ta tarar da ahalin gidan harma da ba'ki waďanda bata saniba,, tunda tashigo suke murmushi damata sannu da zuwa, itama saita daure take murmushin ya'ke, amma tuni momcy ta harbo jirginta, ta gaisheda  kowa dake falon, waďanda ta girma suka gaisheta, hajja ta mi'ka mata hannu alamar tataho wajenta, kusada ita taje ta zauna sai asannan Nawaf yashigo yana cilla makullin mota sama yana ca6ewa, kai kai lallai ashe yau munada manyan ba'ki, waďanda yakecema manyan ba'ki suka shiga dariya suna faďin kainedai babban ba'ko, shekararka nawa rabonka da saudia, shima ďayan gefen hajja yaje ya zauna suka sakata tsakki shida yasmeen, ya ce, "ablah kibari kawai wallahi sana'ar nan tamu itake hanamu wani motshi, amma waccan shekarar nazo saidai kwanana biyu naduba hajja na tsere, ya madina?.
   Ta ce, "madina lafiya lau, ya amarya tunda bansamu zuwa bikiba sannan jawad yana fama da rashin lafiya muna kwance a asibiti, ayya ablah karki damu aisu ummulkhairi sunje shima ya wadatar, su jawad suka gaisheshi ya amsa yana tambayarsu ya karatunsu, sukace lfy law,  yamaida kallonsa ga jawad ya ce, "zo na ganka my boy, jawad yazo suka gaisa lallai kayi girma sai aure ko? , gaba ďaya falon suka saka dari, ablah ta ce, "aure kam, Anwar fa ya girmi jawad jikinne kawai ALLAH yabashi haka.
   Koh ablah?, amma yanzu sai ace shine babba, ga Anwar ďan 'karami,, gsky kam, shima yanzu yagama tsokanarsa aii.
   Ablah tacanja maganarta zuwa larabci danda da turanci sukeyi,  ta ce, "Nawaf wannan matar taka kamar ba 'yar Najeria ba?, Nawaf ya kalli yasmeen ya ce, "ablah saboda mi kikace haka??, Ablah tayi dariya naganta 'kya'ky'kyawane,, lallai Ablah kin samemu mu 'yan Najeria bamuda 'kyaune??
   Kunada 'kyau mana amma dai ku ba'ka'kene, inkuwa 'yar Najeria ce ka iya za6e, nanma dariya sukayi, banda yasmeen dabatasan misuke cewaba, Nawaf ya ce, "kai ablah ammafa kin samemu mungode,, saidai yakamata ki shirya kije Najeria kigammu muma akwai kala.
   Ta maida maganar zuwa turanci, Karka damu zanzo Najeria da bikin Abdallah insha ALLAHU.
   tabďi bikin Abdallah kuma?, kice da sauran lokaci kenan??, kai haba wane sauran lokaci?, aii kamar yaune,, ablah yanzufa yake shekara ta biyu a school, yaushe aka gama aka samu aiki, yarinyarma dayakeso ko secondary bata gamaba.
    Hajja ta ce, "aiko Abdallah aure yakeso kaida kadage kanata kwaso masa shekaru, kallifa yanda yake haďe fuska yaji kace da sauran lokaci.
    Abdallah yay saurin cewa hajja karkisa yanzu abii ya hau kaina fa, momcy tai masa dakuwa kaci gidanku ai gsky hajja ta faďa nima ina kallonka.
   Dayaga za'a tasoshi gaba saiya tashi ya shige đaki yana kunkune, lallai abii kaika kama matarka ahannu kunata shan soyayya saini zaka ringa lodamin shekaru, wlhy halimatu tana gama secondary aure zamuyi, dannikam aure nakeso.
   Na ce, "da gsky ka Abdallah wlhy kayi aurenka kaima kasha soyayya.
   Afaloma hirarsu suketa sha, dayake da turanci akeyin hirar yasmeen tanajinsu saidai bata saka musu baki, iyakarta daria ko murmushi, dahaka aka kira sallar isha'i mazan suka fita masallaci sukuma matan sukayi agida, bayan sun dawo akaci abinci sannan su Ablah suka tafi gindan iyayenta dayake anan suka sauka.
   Momcy ta kalli yasmeen datayi shiru cikin kujera ta ce, "ďiyata zonan, yasmeen ta tashi ta nufi wajen momcy, harzata zauna 'kasa momcy ta ce, "A'a takamota ta zauna kusada ita, tajawo kan yasmeen gefen kafaďarta tana shafa bayanta ďiyata miyake damunki?, yasmeen ta ce, "momy babu komai.
   Momcy ta saka hannunta gefen wuyan yasmeen ta ce, "bakijin dađi yasmeen tun jiya ina kula dake bakisan faďane kawai komuje asibitine??, A'a momy bama sai munjeba, to faďamin mike damunki??, mom jikina ne kawai yakeyimin nauyi sai kuma wani lokacin inaďan ganin jiri, amma banajin zazza6i, saidai jikin yayi ďumi kawai.
   Momcy ta shafa kanta amma shine baki faďaba ďiyata, kuma mijinkima bai saniba ko?, eh yasmeen tafaďa,, humm ďiyata zurfin ciki ko??, ALLAH mom niban ďauki abin serious ba shiyyasa., aiko wannan serious ne ďiyata, gobe idan ALLAH ya kaimu ummuhabeeba saitazo ta dubaki kinji, dam gaban yasmeen ya faďi, badai wacan maikama da aljanarba ko tafaďa a zuciyarta.
   Nawaf dake gefe yana kallonsu ya ce, "momcy waimi ake tattaunawane haka?, sai kus2 kukeyi babu maiji.
   Tofa kaji wani sa ido ina ruwanka ko ka aikata wani abune dakake tsoron kar'afaďane??, Nawaf ya murmusa A'a A'a, nikam ban aikata komaiba, amma momcy wannan irin sirri haka miyasa ba'aso muji??, aiba saikunjiba shiyyasa, to shikenan idan tayi tsami maji, nikungama bari naje na kwanta, inaso mu fita da wuri gobe idan ALLAH yakaimu gara muyi ziyarar nan mugama kafin wuri ya 'kure.
   Yay musu sallama ya shige ďaki, momcy ta ce, "yasmeen tashi kema kije ki kwanta kinji ALLAH ya'kara sau'ki, tami'ke tana faďin ameen mom, itama sallamar tai musu ta shige, yayinda suma kowa ya mi'ke yanufi makwanci, dama Abdallah yana ďaki suna waya da halimatunsa.
    Yasmeen ta maida 'kofar tarufe, Nawaf dake zaune bakin gado yana tu6e kaya yajuyo yana kallonta ta ďauke kai daga kallonsa,, murmushi yayi yatashi yashige bayi danyin wanka,, yaudai ba'a daďeba aka fito, yana fitowa itama tashiga, sanda ta fito yana shafa'i da wutiri, itama saitayi harama dan dama batayiba.
   Bayan sun idar yazauna shan shayi itakuma ta haye gado tana mitar mutum kullun saiya sha shayi yake iya barci saikace wata kwaya, koni dana gada bana shansa haka,(karku manta yasmeen buzayene ), koda yake shima yagada awajen momcy.
   Tana nan tana sa'kawa da kwancewa Nawaf yagama ya hawo gadon yakwanta, shiru tayi kamar tayi barci, ya rungumota zuwa jikinsa yana faďin yarinya kokinyi barci saikin tashi, danyau bazan iya ha'kuriba, duk abinda yake mata tanajinsa tayi shiru.
   Dayaga haka saiya ďauki wayarsa ya haska mata fuska, dole taďan 'kyafta idanu sabida haske, yay dariya, oh da wasan 6urun2 akeyimini to aii na harbo jirginki, hannu tasa taďan tureshi tana faďin dakazo kana 'yar murya bagara kabiya sadaki aďaura muku aureba gobe kaida mai kama da aljana.
   Tabashi dariya sosai wai mai kama da aljana wato ummuhabeeba kenan,, cikin dariya ya ce, "A'a fancy face karfa ki faďa abakin mala'iku, surubuta gobe ya tabbata, dama ďazu kince kin barmata ni.
   Ta gallah masa harara tamkar yana ganinta, ta ce, "kaidai kasani.
   Yasake rungumota yana faďin kema zaki sanine, tunda zaki koma raba dai2 ďina da wata.
   Haushine ya 'kara turnu'ke zuciyar yasmeen saikawai tafara kwalla,, jiyayi laima tana bin 'kirjinsa da sauri ya haska danyasan 'kila kuka takeyi, ilai kuwa shitakeyi, yashiga share mata haba matana uwargidana kuma amaryata dagake aii babu 'kari, itafa mai kamada aljanar nan amatsayin 'kanwa na ďauketa, dan haka batada wani fili azuciyar habibinki, duk kinbi ki mamaye ko'ina, 'ya'yana kawai kika barma fili, plz banaso kibari kishi ya 6ata min ranki a banza, Nawaf nakine ke kaďai fancy face, ya 'kare maganar da sumbatar bakinta, daganandai ya cigaba da kwantar mata da hankali ta hanyar daya dace.

   Washe gari momcy ta aika Abdallah ya đakko ummuhabeeba danta duba yasmeen, sama2 suka gaisa kowa kishi yana cin zuciyarsa, Nawaf yay dariya wato sudai mata basuda wata damuwa saita kishi.
   Toshi wannan 'kaddara tasa ya haďasu aiyaga takansa.
   Ummuhabeeba tanama yasmeen tanbayoyi cikin wani yanayi, itama tana bata amsa cikin jin haushi, tun a tanbayoyin datake mata da amsar datake bata tagano yasmeen ciki gareta, amma tsabar kishi bazai barta tafaďa musu yasmeen nada cikiba, saita ce, "zataje asibiti tadawo.
   Momcy ta ce, "babu wani magani dazaki bata yanzu ummuhabeeba?, dan na kula batajin daďin jikinta, karki damu momcy yanzu zandawo insha ALLAHU da maganin zan dawo, to shikenan saikin dawo.
    Ta kalli Nawaf  abii zoka kaini muje mudawo plzzz, saida yaďan harareta sannan ya ce, "dawaya kawokine?,, ta shagwa6e fuska ALLAH mijin Ablah hidaya ne ya saukeni, toga key kije kidawo, ta zaro ido waje kamanta nanba 'kasarku bane, kasanfa mata basa tu'ki a saudia........
   Momcy ta 'katsemusu zancen da faďin kaje ka kaita mana modeebo, kaga yasmeen batajin daďin jikinta, zaku zauna gaddamar dakuka saba, saida yakalli yasmeen dake kwance ta haďe rai kamar zatayi kuka, ta harareshi, ya ďauke kai yana faďin to momcy.
    Suna fita ummuhabeeba ta kamo hannunsa, da sauri ya kwace yana harararta, ta ce, "sorry bazan sakeba, batareda ya ce, "komaiba ya buďe motar yashige, itama saita buďe ta shiga, tanaso tayi masa maganar aurensu amma tanajin tsoro dan ganin yanda ya haďe rai kamar bashiba.
   Har cikin asibitin ya kaita, tafito tana faďin kazo muje ciki mana, kai ya girgiza mata, A'a jeki fito ina nan ina jiranki,, asanyaye ta ce, "to, taso yashiga dan 'kawayenta su ganshi, suna shan labarinsa sosai awajenta.
   Bayan tafiyarta  ya kwantar da kujera ya kwanta, tuni tagama abinda takeyi amma tayi zamanta suna hira da 'kawayenta kamar babu wanda ke jiranta,, Nawaf yagaji da jira yafito, yasan matarsa tana bu'katar magani danyabaro jikinta da zazza6i, cikin asibitin yanufa, office ďinta yafara zuwa amma arufe, wanine yake gaya masa aii yau bata aiki tana hutu sai dare, ya ce, "ai tare sukazo,, mutum ya ce, "to inaga tana wajen 'kawayenta zomuje na rakaka 6angarensu, acan kuwa ya sameta tana ganinsa tafara wani kame2n binciken takardu,, ya 'karaso yana faďin ummuhabeeba wai har yanzu?,, ta mi'ke tana faďin abii yanzu na kammalane.
    'Kawayena ga abiina na 9ja sunansa Nawaf,, suka mi'ke suna faďin woow!! Nice guy, dama sun sansa a hotuna datake nuna musu, suka gaisheshi ya amsa yana tambayarsu ya aiki.
  Bayan sun gaggasa yayo waje, itakuma taimusu sigina da ido itama tafito tana dariya suma sunayi.
    Amota ta tarar dashi, harya tada, tashigo tana faďin albishirinka abii, batareda ya kalletaba ya ce, "goro, saida taďan cije le6e ta ce, "matarka tanada ciki wata biyu, da sauri ya tsaida motar yana kallonta, ya ce, "da gsk kikeyi ko wasa?, ta ce, "wlhy da gsk, aii baisan sanda ya rungumeta yana murna ALHAMDULILLAH yaketa faďi, yayinda itakuma ta kwanta luf ajikinsa, da sauri ya tureta yana faďin wa'iyazubillah, ALLAH ka nisantamu daga sharrin shaiđan.
   Shiru kawai ummu habiba tayi dan batada amsar bashi, haka suka 'karasa gida batareda ya kula dukkan maganganun datake masaba, yana zuwa ya rungume yasmeen babu ko kunyarsu momcy da hajja, ya ce, "fancy face albishirinki, da sauri ta tureshi dan kunyarsu momcy sai asannan ya kula dasu ya saketa da sauri yana sosa kai, yay 'kasa da kai yana faďin sorry mom & hajja.
    Momcy ta ce, "kaidai kasani mara kunyar banza, to Albishirďin mi zakai mata??, ya sosa kai ummuhabeeba faďa musu kawai.
   Ummuhabeeba dake tsaye kamar gunki tun ďazu, ta mi'kama momcy result ďin,   momcy ta amsa tana dubawa, cikin murmushi ta mi'kawa hajja itama, hajja ta rungume yasmeen tana murna suka shiga mi'ka addu'oin alkairi ga cikin dabai wuce wata biyuba, kowa yana cikin farinciki da murna bare uban ginsamin Nawaf, momcy tabata shayi dakanta ta sha dayake ALLAH yasa cikin bamai saka ami bane, tanashan magunguna ta 6ingire barci abinta.
   
Haka rayuwa tacigaba da tafiya da sauri, yasmeen tana samun kulawa wajen mijinta da iyayensa, yana zagayawa da ita ko'ina guraren tarihi da gidajen dangi, sunje har kabarin fiyayyen halitta (ANNABI MUHAMMAD ,,,S A W), Tanajin daďin rayuwar saudia, kusan kullum saitayi waya dasu yaseer da ameena tanajin labarin 9ja,     satinsu uku papa yazo, shima yay sati ďaya sannan suka tarkato komatsansu zuwa 9ja, yasmeen tayi wani shegen 'kyau kunsan mai yaron ciki akwai bada kala, har wata 'yar 'kiba tayi, sun dawo 9ja suna kewar mutanen saudia,, su mas'ud ne sukazo tarbarsu.
    Tun afilin jirgi ameena take mata tsiya wai kodai ta kamu?, dan taga tayi wani 'kyau na musamman, yasmeen ta harareta kedai kika sani 'yarsa ido,, to shima mas'ud ba'a barsa abayaba wajen tambaya, kusan amsa ďaya Nawaf yabashi data yasmeen, mas'ud ya ce, "mutumina karka faďa ainariga na gane kasandai ni likitane, Nawaf ya ce, "to sannu likita, ya faďa yana ďaga nanah dake hannunsa, ya ce, "Ameena mikike bama babyn mu tayi girma da 'kyau haka cikin wata ďaya??.
   Ameena tayi dariya, babu abinda akebata, sai abincinta,, kai amma ďiyata 'yar baiwace, wlhy kuwa habibina yasmeen dake baya kusada ameena ta tafaďa.

Hakadai akacigaba da gungurawa cikin yasmeen yana fitowa, sati biyu masu zuwa kuma zasu cane 'kasar Spain, saidaifa papa kamar yana shirin hana tafiya da yasmeen ya ce, "idan ta haihu tataho daga baya.
    Saidai nakula maganar bata shigi Nawaf ba sosai,, dan kamar baima yardaba, toko yaya za'ayi kenan kudai biyoni kawai.
   Suma su yaseer da Anwar wannan satin suka ďaga zuwa 'kasar Rasha domin fara karatu a6angaren likitanci.
    To abokan juna saimuce ALLAH ya taimaka, yasa adawo asa'a.......................










© 2017

bilyn Abdul
     Mrs Abdus'salam
          luv u oll my fan's
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *