check your best novels here

Saturday 11 March 2017

SABON AL'AMAREE 31/33

[26/02 16:56] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMREE》》





NA BILKEESA IBRAHEEM 
       {♡Bilyn Abdul♡}


31

............munedai 'yan iska ko?, to kema yau zanyi iskancin dake, rigarta yashiga 'ko'karin cirewa, itako sai tureshi take tana kuka dakiran tashiga uku mama kizo ki ceceni, abubuwa yashiga yimata masu matu'kar tsoratar da bakonsu, yafara 'ko'karin cire dogon wandon dake jikinta, cizo ta galla masa a 'kirji, dukda yaji zafi amma ya daure yacigaba da abinda yake, kawai jiyayi tafara shiďewa dannan ta sassan 'kame awajen bayan tasaki wata razananniyar 'kara, ďagata yayi yakoma gefe yana kwafa tareda harararta, ya sakko daga saman gadon yafara neman magungunan daya kawo mata kwanaki, da'kyar yagansu batayi amfani da ko ďayaba, rintse idanu yayi yana faďin halinki saike maryam, abin turare yajona ajikin soket yazuba turaren maganin babu daďewa tafara tari, ta tashi arazane zata gudu dan ganinsa tsaye akanta, ya ce, "mu sa'anninkine???.
     Kai ta girgiza da sauri.
    Zaki 'kara cemana 'yan iska?.
  Nannma kai tagirgiza, ta ďora dafaďin yaya dan ALLAH kayi ha'kuri bazan sakeba dan ALLAH karkayi iskancin nan dani natuba wlhy bazan sakeba kaji na rantse, yanda ta ruďe sosai tabashi matu'kar dariya amma saiya gimtse ya ce, " ba nace karna sakejin kince iskanciba, hannu tasa tarufe bakinta tana hawaye, jikinta sai rawa yakeyi, ya watsa mata harara maza ďauki rigarki ki saka..........kafin yarufe baki ta rarumo rigar tana kare 'kirjinta saiyanzu talura yacire mata har bra ďinta, taja bargo ta lullu6e jikin, ya ce, "riga nace ki sakafa.
    Ta ce, "dan ALLAH to kajuya baya koka fita plzzzz.
   harararta yayi babu inda zanje, idan zaki saka ahaka ki saka, kitashi muje wajen break bily tana jiranmu, kuma wlhy ki daidaita nutsuwarki, idan kika bari tagane kina cikin wani yanayi zakisha mamaki.
    Wlhy bazan bariba barima kaga nawanke fuskata, rigarta bra ďin ta ďauka dagudu tashige bathroom, ya Mahmud ya tuntsure da dariya harda zama, kai matsoracima baiji daďin halinsaba, yarinya sai tsiwar tsiya amma tsoro fal cikinta, magungunan yagyara yamaidasu inda yaďakkosu, yakarasa gaban 'kofar yana bugawa kefa nake jira kina 6ata mini lokaci.
    Burum tabuďe tafito, ya ce, "maza jeki shafa fauda da kwalli, babu musu tayi abinda yace (nace o, su Nurr akwai tsoro), ya ce, "ki daidaita nutsuwarki sosai banason shirme, tayi kwal2 da idanu hawaye suka cika idon taf, ya ce, "o, kukan zaki 'kara???, da sauri ta maidasu tana girgixa kai, gaba yatasata har falo inda aunty bily take, takamo hannunta tana faďin haba Nurr ďin mama badai kuka kikayiba???.
    Saida takalli ya Mahmud sannan ta girgiza kai tana murmushin ya'ke, ya ce, "sakarta tazuba min abinci dan inada gurin zuwa, anty bily tasaki hannun Nurr, itakuma jiki asanyaye ta haďa masa dukkan kayan abincin agabansa, bai sake bi takansuba yashiga cin abincinsa, yana gani aunty bily tana ta lallashinta, yagama ya mi'ke samansa yakoma domin canjo kaya, wajen kokawa da Nurr duk kayansa sun yamutse gata shadda, yasakko cikin wata sabuwar shigar ta farin yadi mai shara2, saina dawo yafaďa yana ficewa batareda yajira amsar suba.
    Da 'kyar aunty bily ta lallasheta taďanci abincin, tana gamawa takoma ďaki tadasa sabon kuka.
  
 Da gudu deena tashigo gidan tana ihun kiran Nurr aunty bily!!!, ta ďane wuyan aunty bily tana murna, ohni deena haryanzu ba'ayi hankalinba??, dariya tayi ta ce, "aunty da sauran lokaci ina Nurr??, tana ďaki aunty bily tafaďa.
    Dagudu tanufi ďakin Nurr, tana shiga suka rungume juna, deena tana murna Nurr tana kuka, sunkai minti biyar ahaka sanan suka saki juna, deena tafara share ma Nurr hawaye haba sis......miya sakaki kuka haka??, da nazata na murnar ganinane??, miyake faruwa??.
     Nurr ta zauna tana share hawaye deena wlhy bazan iya zama da ya Mahmud ba, bana sonsa shi ďan iskane, wlhy bana sonsa.
    Deena ta ce, "ban gane ďan iskaba??, kin ta6a ganinsa da karuwane??, kai ta girgiza, to giya yakesha??, nanma kai ta girgiza.
    To miyayi miki???.
 Hawaye Nurr ta share ta zayyanama deena komai, dariya sosai deena takeyi harda kwallah,, saida taga Nurr ta sake fashewa da kuka sanan ta tsagaita da dariyar datakeyi tana faďin sorry my dear wasa nakemiki.
     Yanzu waye yayima gadonnan haka?? deena ta tambaya tana gimtse dariya, Nurr takalli gadon tana hawaye, shine yay masa haka yanzunnan kafin muyi breakfast, deena tami'ke tana dariyarta ciki2, gadon tagyara tsaf sannan tadawo tana lallashin Nurr, saida taga ta nutsu tafara sakinjikinta sanan ta ce, "Nurr abinda kikagafa ya Mahmud yanayi da aunty bily ba iskanci bane, matarshicefa yana da hakkin aikata hakan agareta, kuma kema ba iskanci yay mikiba tunda "k matarsace, aii yamayi 'ko'kari da har yau baiyimiki komaiba, wlhy ni randa aka kaini ya Suraj bai barniba, gashi ina cikin kukan rabuwa dake da iyayenmu amma ko kaďan bai saurara miniba, "k yanzu hakafa ciki gareni.
    Idanu Nurr tazaro saikuma ta bushe da dariya tana faďin kai deena ciki kuma??, ta 'kara tuntsurwa da dariya..  
   Deena ta ce, "bakuna nason iskanci malama, dan nace miki inada ciki shine zaki tasani gaba da dariya, Nurr takai hannunta kan cikin deena tana faďin sorry mai ciki, ashe nakusa zama momy babyna ykk??.
    Deena ta ce, "yar iska saura "k, tunda aka fara gwadaki yau aiko ana hanyar baki ciki, duka Nurr takaima deena deena takauce tana dariya.
    Aunty bily tashigo tana faďin lafiyarku kuwa??, Nurr ta tuntsure da dariya aunty wai kinji deena ciki gareta, hhhhhhh takuma kecewa da dariya, anty bily ta ce, "ALLAH yashiryaki Nurr kinji, cikin shine abin dariya saurake aii, ta gwalalo ido waje ALLAH yakiyaye aunty nayo ciki??? haba.
     Da'kyar ta daina dariyar suka zauna suna hira.
   Deena tami'ka mata wayarta Nurr ga phone ďinki.
   Lah dama tana wajenki??, inata tunanin kona yarda, a'a tana wajena, saidaga baya naganta acikin akwatina ashe nan muka sakasu, ALLAH sarki my phone i miss u, tafaďa tana summbatar wayar.
    Aunty bily tami'ke kunga kuci gaba da hirar bari naje na haďa mana abincin rana, yanzu zakiga yaya yadawo.
    Suna ďaki ya Mahmud yadawo, baiyi zaton aunty bily tana kicinba, yazata suna tare dan yaji hirar mutun biyu tunda baison deena tazoba.
    Yaturo 'kofar yashigo, deena ta ce, "yaya sannu dazuwa.
   A'a deena kece agidan namu?.
  Eh yaya nice nazo muku yini.
To lallai mungode dayawa, amma ba mijinki yace mini bakida lafiya ba??, eh yaya amma naji sau'ki aii.
   To ALLAH ya'kara sau'ki.
 Ameen yaya.
   Nurr tace sannu da zuwa, bayan taga ya watsa mata wata uwar harara, sai yanzu kika gani yafaďa yana fita.
    Baki ta murguďa ta ce, "mugu kawai.
  Deena ta zaro ido lallai yarinya wuyanki ya isa yanka, yaushe kika raina ya Mahmud haka?, yanzunan idan yajikifa??.
    To yaji mana, zai kashenine.......salamu ailaikum, sukaji sallamar ya Mahmud yadawo.....................





Luv u oll my fan's
©2017
[27/02 17:23] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》




NA BILKEESA IBRAHEEM 
       {♡bilyn Abdul♡}




32

.......A tsorace suka amsa masa azatonsu yaji, shima ya fahimci kamar sunďan razana da dawowarsa, ya ce, "k bani magungunan nan, Nurr ta 6ata fuska dan tanajin haushin ''k ďinnan saikace baisan sunantaba, ya ce, "ba'kya jinane??, mi'kewa tayi ta ďakko masa, ya kar6a yafice.
     Deena ta ce, "maganin miye Nurr?.
   Oh masa ranar yakawoshi tun ana kwana ďaya da kawoni, nikuma banyiba.
   To saboda mi??".
Babu komai wlhy nina ma mantane, ALLAH ya shiryeki Nurr, amin 'yar uwa Nurr tafaďa suna tafawa da deena.
   Haka sukaita hirarsu kamar karsu rabu, bayan aunty bily ta kammala abinci takirawosu, kusan tare sukafito da ya mahmud, suka 'karasa dani kowa yanemi gurin zama.
   Aunty bily batayi yin'kurin haďama ya Mahmud abinciba dan tasan girkin Nurr ne, itama tayi burus dashi, saida anty bily ta ce, "Nurr yayafa ''k yake jira, Nurr taďan zum6ura baki taďago tana kallonsa, ya harareta, tai saurin kauda idonta daga kallonsa, tashi tayi tana saving nasa, tako ta'ke filet da abinci kamar mutum uku zasuci, aunty bily tabuďe baki zatayi mata magana ya Mahmud yaďaga mata hannu alamar tayi shiru, itamadai deena kallon abin mamaki takeyi, tasan Nurr da iya tsokanar faďa kosanda suna makaranta itake fara jawo musu faďa, saikuma tsoro kamar farra kura, tasan kuma tabbas ya Mahmud ba 'kyaleta zaiyiba.
   Tajuya tazubama su aunty bily suma, amma su daidai cikinsu, yagane wato shine abokin wasanta, wani filet ďin taďakko dazummar zuba nata amma saiya dakatar da ita tahanyar faďin aibama saikin zuba waniba, tsayawa tayi tana kallonsa da mamaki, ya ce, "ďakko cokali kidawo nan yanauna mata kujerar kusadashi, ta zun6ura baki toni idan nadawo mizan maka anan??.
    Harara ya watsa mata ya ce, "bansaniba, zakiyi abinda nace kosaina 'kara ďaukar irin matakin ďazu da safe akanki??, kafin yarufe baki tazo ta zauna, oya sakahannu muci, ta zaro ido waje yaya nifa ba shinkafa zanciba taliya zanci, ya ce, "wannan kuma abinda yashafekine ba damuwata bace, ubanwaye yace kizuba wannan uban abincin anan??.
   Idonta yaciko da hawaye ta ce, "aii canike zaka iya cinyewa, ya ce, "kwarai zan iya tunda ga mahmud jaki, kina 6ata min lokacifa.
   Yaya dan ALLAH tunda anty bily shinkafa zataci tazo kuci tare, kokuma na rage tunda baka fara ciba? Nurr tafaďa cikin muryar tausayi, aiba ita tace kizubaba, kuma tunda kika fito dashi bazai komaba, daga nan yafara cin abincinsa batareda yasake bi takantaba, saida yakai lauma ta uku sannan ya ce, "kinsan ALLAH idan kika bari nagama cin abincinnan bakiciba yau zakisha mamaki, tunowa tayi da abinda yafaru ďazu da safe dan haka sauri tasaka cokali suka cigaba daci.
    Deena da aunty bily sai gimtse dariya suke amma bai kulaba.
   Baifi lauma goma shabiyarba ya ajiye cokalin damashi bacika cin abinci dayawaba, (nace ance maza sunada cin abinci amma banda ya Mahmud wata macenma tafishi cin abinci).
    Tunda ya ajiye cokalin itama Nurr saita ajiye, baice mata 'kalaba yaďauki ruwa yana sha, saida ya kammala yaďauki tishu yagoge bakinsa, sannan ya ďauki cokalin dayaci abincin dashi, ya kalli deena ya ce, "deena ďakkomin caja ďincan, deena tami'ke tana faďin to.
    Tuni cikin Nurr ya ďuri ruwa, ya ciko cokali da abinci yakai saitin bakinta, ta waro ido tana tamke baki, cajan yađaga kamar zai zura mata ya ce, "buďe bakin.......da sauri tabuďe yajuye mata abinci, kafin ta haďiye ya ďebo wani kuma saiya cika cokalin taf, datayi 'kokarin yin gardama saiya ďaga bulala saita amsa da sauri kunsandai Nurr da tsoron duka.
    Cikinta yayi bala'in cika jitake kamar zai fashe amma shi sai ďura mata yakeyi, tanaci tana hawaye, tunsu deena suna gimtse dariya harta fara fitowa fili, harararsu kawai yayi batareda yayi maganaba, suka saka hannu suna toshe baki, Nurr ta fashe da kuka saboda tayi bala'in 'koshi bana wasaba, ta marairaice yaya dan ALLAH ka tausaya min wlhy zan mutu, banza yay mata yacigaba da bata abincin, ina dataga babu ala aii saita shammacesa ta arce da gudu ďaki tasakam 'kofar key, su aunty bily suka kece da dariya dan bazasu iya ri'ketaba, shima mi'kewa yayi ya haye samansa dan dariyar neman kufce masa takeyi, dayaje falonsa saiya zube saman kujera yana she'ka dariya harda hawaye, walhy gudun yarinyar nan yayi bala'in bashi dariya saikace wadda tayo sata, saida yayi mai isarsa sannan yay shiru amma daya tuna saiya murmusa.
   A 6angaren su aunty ma haka saida sukayi dariya mai isarsu sanan suka shirya tsokanar Nurr, wadda tunda ta fece saita zube ajikin 'kofar bayan ta kulle, sai maida numfashi take da 'kyar, tunda tayi girma bata ta6a cin abinci mai yawan na yauba, jitake tayi nauyi ga cikinta tamkar zai fashe, aunty bily tayi bala'in iya muryar ya Mahmud danhaka suka nufi 'kofar Nurr da niyyar tsokanarta.
     'Kofar ďakin sukaje suna bugawa, Nurr tanaji tayi shiru dan tasan ya mahmud ne ya biyota aii wlhy kizasu kwana ahaka bazata buďeba, ya daketa abanza, anty bily ta ce, "wai bazaki buďe bane?, tafaďa cikin irin muryar ya mahmud..         daga can Nurr ta ce, "ai wlhy kozaka kasheni bazan buďeba, anty bily ta ce, "haka kikace ko?, Nurr ta ce, "eh haka nace, kuma wlhy kamatsamin yau agidan daddy zan kwana naje na haďaka da mama, anty bily ta ce, "to ki buďe 'kofar nace, aff zancen kakeso ashe zamu kwana ahaka yaya.
     Suka tuntsure da dariya dansun kasa riketa, data gane bashi bane su aunty bilyne suka tsokanarta saita buďe 'kofar, suka shiga suna mata dariya, deena ta ce, "o, ''k Nurr yaushe zakidaina wannan tsoron ga jan faďa kin iya amma sai tsoron tsiya.
    Zama tayi a'kasa tana dafe ciki ta ce, "wlhy ya Mahmud mugune original, not photo  start copy, dan ALLAH kugafa yanda yake neman kasheni da raina, gashi kukuma sai dariya kukemin, ALLAH yasoku bai sauke muku bala'in nasaba, waima yana inane??.
    Anty bily ta ce, "kina zurowa da gudu shikuma yatafi ďakinsa, kai Nurr kin iya gudu fijo!!!! Sunan wata mota.....suka tuntsure da dariya harda Nurr, tanayi tana dafe ciki ita adole kar cikinta yafashe, deena ta ce, "to bakiji tsoron sanda kaika arto yabiyokiba??.
    Nurr ta ce, "ainasan duk bala'insa idan ka gudu ka tsira, aunty bily ta ce, "ALLAH nurr kirage abinda kikeyi kinfison keda yaya kuyta wasan 6uya agidannan kamar 6era da mage, ALLAH anty ya mahmud ďinne yacika muguntar tsiya saikanayi kana ďan ramawa, hakadai sukata hirarsa suna dariya..................










Luv u oll my fan's
©2017
[01/03 13:57] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》








NA BILKEESA IBRAHEEM
      {♡Bilyn Abdul♡}




33

......Har yamma Nurr ta'ki fitowa, koda ya Suraj yazo ďaukar deena da 'kyar tafito suka gaisa, ya mahmud yana fitowa ta arce ďaki, har suka tafi bata fitoba sai deenace tazo tayi mata sallama.
    Da daddare bata fito cin abinciba, da aunty bily ta ce, "bari ta kirata sai ya mahmud ya ce, "ta 'kyaleta, wannan cikin nata bazata iya cin abinciba, idanma tayi wasa bazata iya barciba dan ba 'karamin abinci taciba, saidai ki haďa mata furut tasha, shine zai taimaka mata abinda taci yayi 'kasa.
   Anty bily ta ce, "kai yaya kasan dalon mugunta iri2 saikace wani soja, murmushi yayi ya ce, "wlhy bily Nurr batajin magana ko kaďan, du ha'kurinka saita 'kureka, saikuma taga za'a hukuntata duk saita ruďe saboda shegen tsoronta.
    Aini zangaya maka Nurr akwai tsoro ďazufa tsokanarta mukayi.......aunty bily tashiga zayyane masa yanda sukayi.
   Dariya sosai yakeyi ya ce, "aibatada kunya yarinyarnan wlhy ni nama rasa yanda zanyi da'ita, nema ma take ta rainani, anty bily ta ce, "kuruciyace kawai ke damunta bari kaga takai irin shekara ashirin ďinnan zata rage abinda takeyi.
    Ya ce, "ta6 ashe da sauran aiki wajen shekara ukufa nan gaba, kafin sanan aina gama jigata da halin Nurr, dariya anty bily tayi, kuma dayake tanajin tsoronka zata rage wasu abubuwan kafin sanan, to ALLAH yasa yafaďa yana ajiye cokalin hannunsa alamar ya 'koshi kenan.
    Bayan sun kammala aunty bily ta haďa kayan furut takaima Nurr, Nurr ta ce, "yauwa anty bily wlhy kin taimakeni dama cikina tun ďazu narasa yadda zanyi saboda ya cinkushe.
   To aiga furut nan saiki sha insha ALLAHU zai sauka yanzunnan.
   Acan kuwa Deena tunda suka koma take bama ya suraj labarin ya Mahmud da Nurr, sai tuntsura dariya yake, ya ce, "sukuma tasu salon soyayyar kenan??, deena ta ce, wlhy kuwa kaima ka faďa ai da gidan nake danaci dariya wlhy.
   Ya ce, "gsky kam saikace wasu tom & jerry, ai sunfima tom & jerry, haka taita bashi labari shikuma yana she"ka dariya.
      Da lokacin kwanciya yayi sai ya Mahmud yay kwanciyarsa a ďakinsa, dan yanaso yabar Nurr tasamu Nutsuwa tunda a tsorace take dashi, ga abinda yay mata da safe gakuma laifin datayi masa.
    Itakam addu'a taketayi ALLAH yasa kar ya mahmud yazo dan yau koma tsoron bataji, idanma tanajin tsoron saidai na haďuwarta da ya mahmud, tadaďe batayi barciba saboda fargabar kada yayi amafani dawani key ďin yashigo kamar yanda yakeyi, to hardai barci ya saceta bai shigoba.
   
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, yauda gobe sai ALLAH inji masu iya magana, Nurr tanata hidimarta dan yanzu ya Mahmud yadaina kwana ďakinta, iyakarta ranar girkinta tayi masa abinci, tana gyara masa ďakinsa amma ruwan wanka saidai ya haďa da kansa, haka fira bakoda yaushe take zama ayi da itaba, tafi maida hankali wajen karatun novel awa, duk lungu dasakon dazata tasamo novel tasani, dan haka tarage wanima shirmen dan tana ganin yanda ake wasa 'yammatan littafi ko matan aure, shiyyasa itama takeso ta koyi wasu abubuwan badan ta burgr mijintaba saidan itama aringa đaukarta a babba ba yarinya ba, har yanzu bata ta6a jin son ya Mahmud ko kwayar zarra azuciyartaba, hasalima komai yayi haushi yake bata, tana masa kallo na mugun mutum masifaffe, kullum burinta ALLAH yasa yasaketa takoma makaranta kamar yanda khairat taci gaba da karatunta, itama tana burin haka, koda yake deena ta ce, "mata suma ana nema musu makaranta to ALLAH yasa hakane.
  
Yauma dai aikin aunty bilyne suna gama breakfast ya mahmud yafice gidan dady, da sallama yashiga falon babu kowa dan haka kai tsaye yanufi ďakin mama tunda su dady basu dawoba shida mami, nanma da sallama yashiga, Saiff dake zaune saman kujerar ďakin yana break ya amasa tareda sakkowa 'kasa yabama ya Mahmud kujerar, saida ya zauna sanan saiff ya gaidashi, ya amsa yana tambayar ina maman??.
    Saiff ya ce, "tana bathroom amma yanzu zata fito, yaya Ina Nurr??, tana gida saiff tunda ka'ki zuwa, zanzo wlhy yaya makarantace take hanani wani motsi amma zanzo gaishesu itada aunty bilkee harma da deena da aunty ikileema, to shikenan sai munganka.........mama ta katse musu zancen saboda fitowarta daga bayi, ďan zamowa yayi daga kujerar yana gaisheta, ta amsa tana zama gefen gadon ta ce, "ya iyali??, lafiya lau suke suna gaidaku yafaďa yana sunkuyar da kai kamar mara gsky, mama batace komaiba dan tanajin nauyin yin doguwar magana dashi, tsawon minti biyar babu wanda yasake magana, saiff yami'ke yana faďin mama bari naje wajen su Farhan, to saiff adawo lafiya, yafice yana faďin yaya ka gaidamin Nurr, to zataji saiff.
    Bayan fitarsa ya Mahmud yadaure ya ce, "mama dama nazo akan maganar Nurr ne.
   Mama ta ce, "incedai lafiya?, ko Nurr ďin batada lafiyane??.
    A'a lafiyarta 'kyalao akandai son sanin maganar iyayentane.
          , har yanzu tana cikin damuwa kenan bata kwantar da hankalintaba?, mama ta tambaya tana kallonsa, eto dadai sau'ki amma wani sa'in takan zurfafa tunaninta.
   Mama taja numfashi aii wanan kuma laifinkane, kaikeda alhakin lallashinta da kwantar mata da hankali, nasanka da zarni amma kuma duk zarnin mutum yakamata ya sassautama iyalinsa tahakane zakasan matsalarsu harka iya maganinta, kasan Nurr har yanzu akwai kuruciya atare da ita, idan ka bita ahankali kana kwantar mata da hankali saikaga ahankali taringa rage damuwarta harma tacigaba da rayuwarta kamar da, kasan ba'ason tada zancenan a family saboda nemawa yarinyar nan daraja, iyayenku basa son aringa kallonta da laifin mahaifinta, dan haka kaima karna sakejin makamanciyar maganarnan abakinka.
   To mama insha ALLAHU ya wuce kenan ayi ha'kuri,, shiru tayi saikuma ta ce, "ya ciwonnata basadai matsa mata ko??, a'a da sau'ki tundama taje sau ďaya tayi, kuma dayake an kar6o mata magani.
    To shikenan ALLAH ya 'kara karewa, amin yafaďa akan la66ansa daganan shiru yabiyo baya, ya Mahmud yanaso yaga sun zauna da mama haka suna hira, amma ita bata sakar masa fuska saboda kunya da kawaici, yauma saboda mami bata nanne shiyyasa har firar tasu tayi tsawo haka, haka zai dage yayta cusa kansa harta fara sakewa dashi.
   Mamafa ko gidansa bata ta6a zuwaba saida bily tayi 6ari kusan na 'karshe sanan tadaure taje abisa tursasawar dady, yanzukam ai yasan dole taje kodan Nurr, yasan yanda take 'kaunar Nurr kosu 'ya'yanta bata musu haka, shiyyasa mutane dayawa suka gaza gane ba itace ta haifi Nurr ba........mama ta katse masa tunanin dafaďin akawo maka breakfast ne??, kai ya girgiza cike da jin daďi ya ce, "a'a mama saida nayi break nafito, to shikenan mama tafaďa.
    Haka  suka zauna tamkar surukai lokaci2 suďan ta6a hira saikuma ayi shiru na tsawon lokaci, yadaďe agidan daga baya yay mata sallama yataho gida.

Daga nan gidan ya fahad yashiga, suna falo shida iyalinsa suna hira, Abdul da rauda sukazo suka taresa suna faďin oyoyo dady, ďagasu yashiga yi yana faďin oyoyo yaran daddy, ya zauna saman kujera yana faďin school ya 6oyemin ku yarana, Rauda dake cinyarsa ta ce, "dady jiyama na iya alifun, ya ce, wow!! Babyna da gsk??, ta ďaga kai cikin farinciki, Abdul ya ce, "dady aini na'iya tuni uncle ma ya ce, "nafita 'kokali, ya mahmud yaja hancin abdul aikai dabanne babammu.
   Anty ikileema ta ce, "yaya ina kwana waďannan maganannun sun hanamu ko gaisuwa ayi, ya amsa yana dariya to aini dama danna gansu nazo badan kuba.
   Yaya fahad ya ce, "haba yaya wasa kakeyi.
   Babu wani wasa gsky ce nafaďa, okey ikileema to tashi mubar musu falon ya fahad yafaďa yana dariya, hanya ya mahmud yanuna musu ya ce, "kuyi maza ga hanya, dariya sosai sukeyi, yami'ke tareda sa6ar Rauda akafaďa yakama hanun Abdul suka fice.
    Suka bishi da kallo da addu'ar shima ALLAH ya azurtashi danasa 'ya'yan.
   Daga nan gida yanufa, Nurr kaďaice a falon, tana kwance saman doguwar kujera, jikinta sanye da wando pink iya gwuywa tasa farar best taďora pink ďin jaket mai mannewa ajiki, kanta ko ďankwali babu dama batacika sonshiba, kunnenta manne da iya fis, tanajin wanka, yashigo da sallama hannunsa ri'ke dasu abdul, kwata2 Nurr batasan da shigowarsuba dan idanunta alumshe suke da alama tanjin daďin wa'kar.................









Luv u oll my fan's
©2017
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *