check your best novels here

Thursday 13 April 2017

BAN SAKETA BA!!! 7 to 9

*________________________________*
      *BAN SAKETA BA!!!* 
*________________________________*
                        *NA*
        *BILKEESA IBRAHEEM*
              *{Bilyn Abdul}*
*________________________________*
https://mrsbilkisa.blogspot.com




_Sadaukarwa_~*ya Abdul {city phone's}*



*MIYAKAMATA NAYI???.*
     _gyara kayanka bazai zama sauke murababa, idan wani yayima ďanka gyara karka zargesa, kojin haushinsa, gode masa domin kuwa jihadi yatayaka, tarbiyyar 'ya'ya jihadine ga kowace uwa ko uba, bakasan miya aikata aka tsawatar masaba, dan haka kada kazama mai fifita son 'ya'yanka akan gsky._
    *"Kaso naka duniya tak'isa."*
 *"Kak'i naka duniya tasosa."*
   *ALLAH yasa mu gane.*

_Page....._7.

           ..........iman tayi shiru tareda k'ok'arin mik'ewa, da sauri xoxo ta rik'eta, wai inakuma zakije?, dariya tayi haba my hafsy shikenan kuma bazamuyi barciba?, kofa sallar isha'i bamuyiba, karku manta kumafa gobefa idan ALLAH yakaimu monday, munakuma da luctures ďin safe.......
   Reefat tai saurin tareta, amma dai aii k'ya k'arasa mana koda nan gurinne, tunda nasan dai saiya biki har bedroom ďin.
   Iman taja numfashi mai nuna alamun gajiya, please my sisters kuyi hak'uri sai gobe idan ALLAH ya kaimu, ALLAH bakina zafi yakeyi kaina har wani ciwo yake.
    Xoxo ta kalli Reefat suka tuntsure da dariya, yayinda iman tayi galala tana kallonsu dan batasan inda dariyar tasu tadosaba.
   Ta ce, "incedai lafiya??."
  K'alau Reefat tafaďa cikin dariya.
    Xoxo ta ce, "iman kinsan miya bamu dariya?.
  ''A'a..
  Iman tafaďa.
     Gudunkine yabamu matuk'ar dariya, wato dakika samu damar ku6ta saikika arce, suka sake kwashewa da dariya.
   Itama batasan lokacin data shiga tayasuba, saboda hangen gudun datayi take tamkar a yanzu yake faruwa, tashige bayi tana dariya domin ďauro alwala.
                      *♡☆♡*

Washe gari da wuri suka tashi kasancewa sunada lucture ďin safe, suduka gayu suka ďauka na birgewa, dan 'yan matan akwai kala, kowa ta iya ďaukar wanka na birgewa, a tsaitsaye sukasha shayi suka fito.
    'Yar tafiya kaďan takaisu aji (class), amma dayake akwai sauran lokaci saisuka samu k'ark'ashin wata bishiya suka zauna suna jiran lokaci yacika.
    Kamar wadda aka zirkuďawa allura tafara waige2, xoxo da Reefat suka bita da kallon mamaki, ta mik'e zumbur tana fidda numfashi da sauri da sauri tamkar wadda tayi gudun fanfalak'e a sahara.
     Inda tadasawa idanu ko k'yaftawa batayi suma su Reefat suke kallo, wani matashine fari atsaye jikin mota, dogone sosai da 'yar k'iba, saidai ba'a kirashi k'yak'yk'yawa sosai ba, amma babu laifi yanada nasadaidai k'yawun.
   Hannayensa aharďe kan k'irjinsa, hakama k'afafunsa suna harďe dajuna, idanunsa k'ur akan iman daketa rawar jiki kamar taga mala'ikan mutuwa.
    Murya k'asa2 xoxo ta ce, "da Reefat inagafa wanan iman takema wanan ruďin, ki lura da k'yau yana kama da musayeef.
    Reefat ta ce, "gskyar ki xoxo, toko shine Dr Isma'il ďin?......
    Kafin Reefat ta rufe baki iman tabar wajen cikin sauri da da sassarfa gamida rawar jiki, binta yayi da wani mayen kallo tamkar zai cinyeta, dayawan ďalibai kallonsu sukeyi suma.
   Saida ta 6acema ganinsa sanan yaja ajiyar zuciya tareda ďan matse ido wasu k'ananan hawaye suka zubo kaďan a idonsa , hankacif ďin hannunsa yasa ya gige yanaďan murmushi k'arfin hali.
   Ahankali yafurta *My SAUDAT* yaushe zaki dawo gareni?, yaushe zaki yarda *BAN SAKEKI BA!!.*
  wlhy *BAN SAKEKI BA*, ki yarda dani, karki bari ciwon haukan sonki  yacigaba damin illah, na tabbata babu wani likita dazai iya shawo kan matsalata saike kaďai.
   "Kece cikon farincikina."
 "Kice uwar ďana."
         Akanki kawai nake tanadin rayuwata, miyasa zakimin haka?, waye yay min wanan kullin?.
  *waye!?.*
            *Waye!!?.*
                     *Waye!!!......?.*
    dasauri yafaďa motar danjin juwa zata juyeshi ak'asa, ya kwantar da kujerara motar da sauri ya kwanta, sai fidda numfashi yake sama2....
   Cikin k'ank'anin lokaci yafara fita hayyacinsa, dauriya da jarumta tabashi damar jawo wayarsa, batareda yasan wayake kiraba ya kara akunne.
      Murya a sark'e ya ce, plz waye?.
   Cikin rikicewa nacan ya ce, "Isma'il kana cikin k'oshin lafiya kuwa??.
    Da k'yar ya iya faďin Nabil kazo katafi dani.
   Arikice Nabil ďin ya ce, "kana inane?..
   Ina makarantar su Iman!.
Hazbinallahu wani'imal wakil, Nabil yaketa ambata, yayinda tuni Dr Isma'il yasaki wayar k'asa dan numfashinsa yafara gagarar fita yanda yadace.
    Su xoxo dai suna tsaye suna shawarar zuwa inda motar doctor Isma'il yake, dan sunga kamar amawuyacin hali yashiga motar.
    Har ciki mai mashin yashigo da Nabil, yazaro ďari biyar yamik'ama mai mashin ďin, batareda yajira canjinba yay gaba.
     Tundaga nesa yashaida motar Dr Isma'il, yak'arasa da sauri yabuďe motar akuma daidai wanan lokacin su Reefat suka iso wajen.
    Tuni Dr Isma'il yafita hayyacinsa da alama ma numfashinsa shirin ďaukewa yake gaba ďaya.
    Nabil yay k'ok'arin matsar dashi kujerar gefen direba, ya maye gurbin inda Dr Isma'il yake da.
   Xoxo tayi k'arfin halin faďin lafiya kuwa?.
  Nabil ya kalleta arikice dadai sauk'i 'yammata, baijira amsartaba yatada motar yafice daga makarantar aguje.
     Kowadai kallon mamaki yabi motar dashi, wasuma har suna faďin mahaukaci.
  Jiki a sanyaye xoxo da Reefat suka k'arasa aji, saikuma suka tarar da iman zaune tanata rusar kuka, kamar zata k'arar da kwallar idonta.
   Tsakiya suka sakata suna lallashi, Reefat ta ce, "iman wai waye wannan mutumin??.
     Kasa magana iman tayi saima wani sabon kuka daya taho mata.....
   Shigowar malamin tahanasu cigaba da neman ba'asi.
  Itama iman tashiga hidimar share hawayen idonta dan fiskantar malamin.
                  
                Acan kuwa Nabil ya isa da Dr Isma'il asibitine arikice, taimakon gaggawa suka shiga bashi shida abokan aikinsa, dan shima Nabil ďin likitane, da taimakon oksajin Dr Isma'il yafara fidda numfashi.
     A6angare ďaya kuma an manna masa k'arin ruwa da aka juye alurai har biyar aciki.
   Bayan lafawar komai Dr Nabil yakira yayansa yasanar masa.
   Cikin rikicewa yaya mansur ya ce, "Nabil badai ciwonsa bane ko??, ya akayima haka tafaru?.
     Wlhy yaya bansan Isma'il yatafi makarantar su iman ba, na barsa agida dan ya ce min zaiyi barci, nikuma nanufi wani uzuri daya ďan tasomin.
     Inama awajen yakirani ya ce, "nazo nafi dashi yana makarantar su iman.
    Yaya yaja wani gwauron numfashi, to yanzu yajikinsa.?.
  Da sauk'ima aii, yana barcine.
     To Alhmdllh.
Dr Nabil yafaďi hakane kawai dan kar hankalin yaya yatashi, amma duk wanda yakalli Isma'il yasan yana cikin mawuyacin hali.........
    Yaya yakatsema Dr Nabil tunani dafaďi, to yaga iman ďin?.
   Wlhy yaya ban saniba, dan lokacin danajedai bata wajen, kodayake bawani saninta nayiba sosai.
   ALLAH yak'yauta yaya yafaďa cikin sauke numfashi.
   Amin dai".
Amma yaya bama saikazoba insha ALLAHU zuwa anjima komai zai dai2ta.
   To shikenan Nabil, kaima ALLAH yasaka maka da alkairi kaji, samun aboki irinka sai antona.
    Babu komai yaya aii yiwa kaine, nida Isma'il munzama ďaya.
     To mungode saina kira anjima.
   To yaya agaishemin dasu deexerh.
   Zasuji insha ALLAHU.

Dr Nabil ya yanke wayar tareda maida kallonsa akan Isma'il.
   Cikin lokaci k'ank'ane harya zabge, sai wani haske daya k'ara.
   Yana tausayama abokinsa, saboda yanda soyayya take masa juyin waina, ALLAH ka warware mana wanan kulli dake tsakanin abokina da matarsa.
   ya ALLAH ka bayyana gskyar lamari, kakuma maidasu amatsayin ma'aurata indai sunada rabon sake zama tare.
   (Na ce, "ameen Dr Nabeel).

Itamadai iman zaune kawai take tana sauraren malamin, amma bata fahimtar abinda yake faďa; gaba ďaya tunaninta nakan Dr Isma'il *SANYIN IDANIYAR TA.*
     Yau tsawon shekara huďu bata gansaba, ashe akwai lokacin dazaizo suga juna, taga yak'ara k'yau da girma, gawata kamala da nutsuwa sun sake riskarsa, uwa uba kwarjinin data hango a fuskarsa da annuri na musamman.
    Ta share hawayen dasuka gangaro mata tareda ďan jan hancinta, lallai tayi dana sanin zuwan wanan rana.
    Yau Doctor yatada mata tsohon ciwon dake cin *ZUCIYARTA* tsawon shekara huďu.
      Tabbas da amafarki wanana ranar tazo mata da idan tatashi bazata sake komawa barcinba.
    Haka tayita sak'e2, har malamin yafice batareda tasaniba, bare tayi ik'irarin fahimtar abinda yakoyar dasu.
            Haryanzu hawayenta sun kasa tsayawa, dan haka k'awayenta sukaja hannunta domin fita susha iska, amma saita kakare dan bataso tafita waje tak'ara tozali da mugun mutuminnan mayaudari.
     Murya asark'e ta ce, "kubarni anan kawai."
   Saboda mi xoxo? tafaďa aďan raunane;.
     Iman tayi murmushi k'arfin hali, babu komai banason fitane kawai.
      Shikenan muma saimu zauna aii.
    Reefat ta ce, "iman wai waye wanan mutumin naďazu?.
  Iman ta cije le6enta na k'asa, muryarta da karsashi ta ce, "Isma'il!!.
       Xoxo da Reefat suka kalli juna, wai Doctor kike nufi?.
     "Kai kawai taďaga musu batareda ta iya maganaba.
    Suma shiru sukayi, kowa yana sak'e2n abin aransa, da mamakin abinda yaraba iman da doctor Isma'il, domin alamomi sun nuna suduka suna matuk'ar son junansu, da begen kasancewa a fada ďaya.
    Amma saigashi sun kasanance amabanbanta gurare, kuma cikin matuk'ar ruďani da nuna damuwa.
        *"Komiye dalili!!!!!!!!???"..........*

                            *♡☆♡*

_Page........._8.

             ................Har suka gama kar6ar luctures nasu duka iman bata cikin walwala, zata iya kuma rantsewa yau bata tsinci komaiba a darissan da aka koyar dasu.
    Sukansu k'awayennata sun kasa gane kanta.
  Tak'i ci tak'i sha bare walwala".
Ahaka suka dawo ďaki tanata basarwa, suna kuma zuwa ta kwanta batareda tasake shiga harkar kowaba.
      Suma k'awayennata saisuka ďaga mata k'afa domin bata hutu na wucin gadi, tasamu damar cuďaya jiyanta da yau.
                                */^/*
     To shimadai a 6angaren doctor hakane, sai wajen gab da la'asar numfashinsa ya daidaita, zuwa wani kuma k'ank'anin lokaci yafarka.
      Dr Nabeel dake gefensa yafara yimasa sannu.
   Ya amsa cikin ďaga kai domin bakinsa yay masa nauyin dabazai iya maganaba.
   Da hannu yay masa nuni da ruwa alamar abashi.
   Dr Nabeel yamik'e da sauri yaďaukko gorar ruwa ya 6alle murfin ya tsiyaya akofi.
    Ya taimakama Dr Isma'il yatashi zaune ya jingina da gado, sanan ya kafa masa kofin ruwan abaki.
    Saida yasha kusan rabi sanan ya janye bakinsa alamar ya k'oshi.
    Dr Nabeel ya ajiye kofin yana k'ara yimasa sananu, ya haďa masa shayi mai kauri wanda yasan sai sunyi dagama kafin yashashi, dan bayason cin abinci yanzu sosai.
      Aii ko dak'yar yasha shayinnan, sanan yasha maganinsa yakoma ya kwanta.
     Har tsawon kwana uku Dr Isma'il yana jinyar jiki data zuciya, sosai yay jinya akwana ukunnan.
      Hakama gimbiyar tasa iman dukda bata kwanta ta ce, "batada lafiyaba jikinta da ayyukanta suna nuna alamar ciwo, danma tanada k'arfin hali da k'ok'arin 6oye damuwa, shiyyasa bakowane  yake saurin gane matsalartaba kai tsaye.
   Amma k'awayenta suna kula da ita suna kuma tayata addu'ar samun sauk'i a al'amuranta na jiya dayau, da gobenta.

    Dr Nabeel yanason tanbayarsa miya faru amma yanajin tsoron dawo da hannun agogo baya dan haka saiya share kawai.
    Bayan kamar minti talatain Dr Isma'il ya ce, "zaiyi sallah.
   Abokina kabari zuwa anjima mana lokacin kak'ara samun k'arfin jikinka.
    Zan iya Nabeel kaidai kaini bayi kawai.
    Da taimakon Dr Nabeel yay alwala tareda rama dukkan sallolin da'ake binsa tundaga azuhur.

       Reefat ta kalli xoxo dake zaune iman kuma tana kwance agefenta, ta ce, "kutashi ga abincin.
    Xoxo ta ce, "sannunki da k'ok'ari, ALLAH bakiji irin yunwar danakejiba, iman tashi.
   Iman taďago jajayen idanunta dasuka kumbura saboda kuka, tunda takwanta kuka take awajen tanayine ahankali kawai saboda kar k'awayenta suji hankalinsu yatashi.
   Ahankali tafurta nak'oshi".
Daga xoxo har Reefat galala sukai suna kallonta, dan ayak'ininsu babu wadda tafi cancanta da cin abinci kamar iman, tun tee ďin safe bata sake cin komaiba sai ruwa.
    Xoxo ta karyar da muraya cikin sigar lallashi ta ce, "haba iman, yakamata kiyi hak'uri hakanan, ki maida komai ba komai ba, kada kiyima ALLAH Butulci gameda ďunbin alkairai da ni'imomin daya azurtaki dasu.
    Kiyarda da k'addara akan abinda yasamu rayuwar aurenki, dukda bamusan abinda yarabaki da Dr Isma'il ba, munada yak'inin *K'ADDARACE,* duk wani mahaluki yakalli kallon da Dr Isma'il yaki miki aranar  yasan akwai tsantsar *SO* da k'aunarki kwance azuciyar sa.
       Wlhy agaban idonmu aka tafi da doctor cikin mawuyacin hali, nasan kuma duk akankine yashiga wanan halin.
    Ki daure kitashi ga abinci muci, insha *ALLAHU* munyi alk'awarin taimaka miki da iliminmu da k'arfinmu.
   Ahankali iman ta tashi zaune domin maganganun xoxo sunyi tasiri azuciyarta, saidai kalmar shigar doctor cikin mawuyacin hali yak'ara sakata cikin ruďani da firgici.
   Jitake tamkar tayi tsuntsuwa taje inda yake dan ganin halin dayake ciki, to amma babu dama.
    Su sukaita tursasata hartaci abincin kaďan sanan ta lalla6a tayi wanka tayi salloli ta kwanta 
     Su xoxo suna son acigaba damusu labari amma suna tausayin k'awar tasu da halin datake ciki a kwana kinnan.
   Dole sukai mata uzuri kasancewarta 'yar adam azija, suma suka kwanta badan sunajin barciba, saidan taya k'awar tasu jimami da tunanin jiyanta da yau, dan gobenta gaibuce.

  Dr Isma'il
        Doctor ya tsura ma abokin nasa idanu, cikin karsashi da dadishewar murya ya ce, "Nabeel wai saiyaushe ne iman zata amince *BAN SAKETA BA?.*
     shin haka zata cigaba da kasancewa da nauyin aurena akanta??, haka zata cigaba da barina kullum cikin *AZUMI* da bagenta?, tanisanta kanta dani, ta nisanta *MUSAYEEF* dani, alhalin yanzune nafi buk'atarsu akusadani.......
    Wasu 'yan kwalla suka mak'ale masa akan gashin idonsa na k'asa.....yacigaba da faďin, Nabeel inaga lokaci kaďan yaragemin a *DUNIYA,* domin *SON iman* yakusa hana numfashina aiki cikin kwarewa.
    Lokaci yayi dazanbarma IMAN duniya gaba ďaya k'ila bayan raina ta sanar daku *BAN SAKETA BA..........*
      hanunsa Nabeel ya damk'e cikin sigar lalashi ya ce, "haba abokina kadaina faďar waďannan kalaman, kaifa *MUSULMINE* kuma mai ilimin addini dana zamani.
     Nasan kasan k'addara da wanzuwarta da shuďewarta, to inaso kaďauki wannan lamarin amatsayin *JARABAWAR RAYUWARKU,* na tabbata akwai wani k'ulli dabamu saniba.
     Nayi imanai *IMAN* bazatace kasaketaba alhalin *BAKA SAKETA BA,* bazata nuna takardar nanba abisa k'arya koson rabuwa dakai.
     Saidai abinda yake bani mamaki da ďaure kai waye yayi irin rubutunka? wajen rubuta sakin iman, indai har yanda kake bani labari hakane tafaru to tabbas akwai ruďi da wanzuwar *SABON AL'AMAREE* a lamarinku.
      Saidai babu abinda yagagari ubangijin al'arshi, dan haka mucigaba da tsananta addu'a insha *ALLAHU* komai yana daf dazu k'arshe, kuma ko waye asirinsa yana gab da tonuwa wlhy.
        Dan haka inaso ka kwantar da hankalinka kodan gudun tashin ciwonka da wanzuwarsa, Nida kai duk munga *JIYAN MU,* *MUNGA YAU,* amma bamusan *GOBENMU BA* domin kasancewarta *GAIBUNMU.*
       Musayeef kuwa kana zuwa ganinsa kana waya dashi aduk lokacin dakaso dan haka ka kwantar da hankalinka insha *ALLAHU SAUDAT* tana gab da dawowa *FADARKA* amatsayin *SARAUNIYAR KA..*
        Dr Isma'il yasaki wani sassanyar murmushi tareda sauke ajiyar zuciya ahankali, to ALLAH ya tabbatar Nabeel, amma lamarin yana k'ara bani tsoro, atunanina nisanta kaina da iman zaisa randa tagani ta ďokantu.
   Amma kash ganina saiya sakata acikin ruďani da shiga uku, Nabeel inason Saudat wlhy sosai, zan iya cewa babu wani mahaluki daya ta6a son wata kamar ni.
     Asanadin iman nakamu da ciwon *ZUCIYA* da *hawan jini,* amma kash takasa fahimtata, takasa yimin uzuri, kodayake batada laifi itama tana cikin ruďanine kawai.
     Hakane abokina, iman tana cikin ruďani wlhy.
    Saidai kawai mucigaba da barma ''UBANGIJI "komai dominshi yanasane da shiga da fitar kowa, kuma shine masanin gaibu.
     Hakane, ALLAH yasa mu dace to.
     Haka Nabeel yayta kwantarma Isma'il da hankali harya samu 'yar nutsuwa, yakira yayansa suka gaisa harda Deexerh da marwan, dakuma mama da maman su deexerh, da aunty.
     
        *WASHE GARI.*
   duka 6angarorin biyu sun tashi sukuku, gakuma kowa yatashi da uziri, iman tatashi da uzirin text.
     Isma'il yatashi da uzirin aiki, an turasu kwantar dawata tarzoma a *RIVERS STATE,* dan kawai bashida ikon k'in zuwane amma daba inda zaije, sauk'insama harda Nabeel a tawagar tasu dan haka damuwar tasa tayi sauk'i.
      
Babu laifi iman ma taďan saki jikinta dan yau harta iya rubuta wani abu a text ďin.
   Su Reefat sunji daďin sakin jikinta sosai, harma a fuskarsu sun nuna.
    Iman tana k'aunar k'awayen nata, dan duk wanda yadace da k'awaye irin xoxo da Reefat yagama dacewa, bakuma zai ta6a yima k'awa kallon baibaiba.
   Dahaka suka rarrafa zuwa ďaki agjiye.
   Amma wanan bai hanasu sonjin labariba kasancewar yau iman adaidai take sa6anin jiya da shekaran jiya data shiga cikin ruďin zuciya dana jiki.
     To itamadai yau harga ALLAH tayi niyyar cigaba dabasu kabarin dan haka suna gama komai suka zauna.

           *LABAREE.*
   .......Nakai tsawon minti talatin dashiga ďakin banji motsin kowaba, sai zuwa wani ďan lokaci naji ana buga k'ofar ahnkali, tuni jikina yahau 6ari da 6aran6arama, cikin rawar murya na ce, "waye......?   
    Doctor ya ce, "kibuďe kinyi ba k'i.
    Da farko ban yardaba, dan azatona wayau zayimin, amma saina rink'ajin maganar mutane sama2, jiki babu k'wari na sakko daga gadon nabuďe k'ofa.
     Babu doctor awajen dan haka na k'arfafa jikina dankarsu zargi wani abu.
    Nazo na gaidasu, suka amsa cikin fara'a da bina da kallo.
   Matane dayawa yara da dattija da 'yammata, da alamadai danginsu doctorne.
    Babu daďewa doctor yafito daga ďakinsa, ya zauna kan hannun kujera kusada wata tsohuwa amma ba tukuf ba.
    Ya ce, "Saudat 'yan sakoto ne dangin mahaifinmu yanzu zasu tafi shine sukazo miki sallama.
   Kaina a k'asa na ce, "sanunuku, suka ce yauwa amaryarmu.
    Daganan ban sake furta komaiba kasancewar inajin kunyarsu dashi kansa doctor ďin.
   Sunďan ta6a hira da doctor sanan suka mik'e, tareda yimin sallama da fatan dawowarsu suna wata shekarar.
   Nidai bance komaiba sai doctor daya ce, "ALLAH ya tabbatar.
     Bayan tafiyar 'yan sokoto saiga deexerh da Marwan waďanda dama can nasansu ahoto, saidai yauce rana ta farko damuka haďu.
    Na tarbesu da murna dan deexerh sa'a tace, shikuma marwan nagirmesa, suma sai fariciki suke daganina, saidai bansan daliliba.
    Na kawo musu cincin muka zauna muna hira.
    Ahaka doctor yashigo yasamemu, cikin farinciki suka tarbosa suna faďin oyoyo uncle.
    Shima yataresu da murna, yarana ina kuka shigane haka??, muna nan uncle, kawaidai gajiyar bikice.
    Yay dariya kokuma ganin bak'iba.
   Suma dariyar sukayi suna faďin dama wanan ďin.
    Nakula doctor yana matuk'ar son deexerh da marwan, sunkuma shak'u sosai dan kusan a 6angarena suka wuni ranar sai nan nan yake dasu kamar wasu yaran goye.
   Washe gari 'yan jalingo suka tafi suma bayan sun shigo har 6angarena suma, tundaga randa aka kawoni bansake zuwa 6angaren mamaba bamma gantaba.
    Wanan yasa nayima doctor tsogumi, ya ce, "nayi hakuri saboda akwai bak'i a 6angarentane amma insha ALLAHU yau zanje.
      ''Na ce, "to shikenan..........

                            *♡☆♡*

_Page ......_9.

             .............Yau 6angaren mama mukaje cin abinci sa6anin da damukeci a 6angaren yayansa.
    Muka shiga da sallama.
 Tana zaune akujera mai zaman mutum biyu, k'yak'yk'yawace itama fara tas, tana matuk'ar kama dasu doctor, idan bama kasaniba saikace itace ta haifesu.
   cikin fara'a taďago tana amsa mana sallamar, ta ďora dafaďin lale da ďiyata, zonan kinji.
   Cikin jin kunya nak'arasa wajenta, kusada k'afafunta nazauna, na ce, "ina yini?.
    Ta amsa da lafiya lauw ďiyata ya bak'unta?".
   Nayi murmushi batareda na amsaba, suma sauran suka gaisheta.
    Bayan an gama gaishe gaishe muka ci abincin rana anan, sanan muka dawo falon aka sake zama.
      Doctor ya ce, "Saudat".
   Na ce, "Na'am".
  Ya gyara murya to kinga family ďina kamar yanda na sanar dake abaya, kuma kema yanzu kinzama 'yar cikin wannan family ďin.
   Da farkodai ga mahaifiyarmu wadda muke kiranta mama, ya nunan yayansa wanan kuma shine yayana Mansur, muna kiransa yaya, wanan itace matarsa ina kiranta aunty, yanuna matarnan dabatiminba.
    Yacigaba waďanan kuma sune yaranmu Hadeeza da Marwan.
    Dan haka ina rok'onki ki girmama family ďina kamar yanda kike girmama naki, gaba ďaya family ďina suna sonki suna farincikin kasancewarki acikinmu.
     Kaina yana k'asa na ce, "insha ALLAHU zaka sameni yanda kake buk'ata, kuma nima inason family ďina nabiyu, nayi alk'awarin zan zauna da kowa lafiya, kuma ina matuk'ar farincikin kasancewa daku nima.
    Ya ce, "to Alhmdllh".
 Nakula dukansu maganata ta burgesu, musamman dasukemin kallon k'aramar yarinya mara wayau, amma sai sukaji zance raďam kamar wata babar mace.
      Mama ta ce, "mungode ďiyata ALLAH yay miki albarka kinji, yakuma bamu zaman lafiya da zuri'a ďayyiba.
   " Duk suka amsa da amin".
Amma bandani.
     Yaya ya ce, "to aini duk abinda zance kunriga kun faďa, saidai na ce, "ALLAH yabamu zaman lafiya.
   Nanma akace amin".
   Aunty kam batace komaiba, da doctor ya ce, "auntynafa mizakice??.
    Ta ce, "a'a ni banida abin faďa, wanda kuka faďa yawadatar.
    Nakula kamar maganar bataima kowa daďiba, musamman yaya, deexerh ma baki naga ta ta6e tareda gallama aunty harara.
    Daganan hira aka cigaba dayi, wadda sukaďai suke abinsu bandani, itama auntyn saita gadama take saka baki.
     Munďan daďe muna hira daga baya suka tafi sallar la'asar, nima muka tafi 6angarena nida deexerh.
       Inason deexerh kasancewarta k'yak'yk'ya nutsatstsiya, gata alamunta suna nuna mai hak'urice da kawauci.
     Muna idar da sallah muka dawo falo domin yin kallo, muna nan zaune doctor yadawo, yashigo da sallama muka amsa.
    Kusadani ya zauna yana faďin kundaiyi sallar ko?.
   Atare muka amsa da eh munyi.
   Ya ce, "masha ALLHU".
  Namik'e nakawo masa ruwansha, cikin murmushi yakar6a yana faďin ALLAH yay miki albarka.
   Na ce, "amin ngd".
Deexerh ta shagwa6e fuska, uncle anbamu aikifa tun wancan satin, kuma gobe idan ALLAH yakaimu za'a amsa, nikam nakasa yin nawa.
    Dictor ya ce, "haba my daughter keďin aiba abinda zai gagareki saboda nasan kwakwalwarki akwai jaa.
      ALLAH uncle bawasa nakeba.
  Okey, tojeki ďakko nagani.
Da gudu tafice daga falon, yayinda shikuma yadawo kujerar dana koma, yazauna kusadani tareda rungumoni zuwa jikinsa.
    Ina masifar son turaren doctor dan haka nak'ara kwantar da kaina ajikinsa ina shak'a.
     Shikuma yasake nutsani sosai a jikinsa, ahankali yafurta my iman ina k'yaunarki dayawa wlhy.
   Nima na ce, "ina k'yaunarka doctor.
    Da sauri yaďago fuskata yana kallo, yak'ara k'ank'ance idanunsa yana k'aremin kallo kasa2, da gsky Imaniiii!!!??.
    Yanda yaja sunan nawa saida tsigar jikina tatashi.
   Na ďaga kai ahankali".
Yasaki k'ayataccen murmushi, ashe yau zaki amince mukwana gado ďaya kenan?, saboda na nuna miki tsantsar k'aunarki dake kwance acikin jinina da zuciyata.
    Kaďan naďago ina kallonsa, na maida kaina da sauri dan ganin ya kafamamin idanunsa......ahankali ya matso da fuskarsa kusada tawa danufin bani sumba sai deexerh tashigo ďakin.
    Yay saurin janye fuskarsa yana 'yan kame2 narashin gsky, yabani dariya amma saina gimtse nima nayi saurin tashi daga kujerar na canja wata.
    Deexerh tak'araso kusada shi ta zauna ta bashi littafin nata.
    Kar6a yayi yana satar kallona, nikam kaina yana k'asa.
   Bayan yagama dubawa ya ce, "my dee....bari nagaya miki kiringa rubutawa, babu musu deexerh tayarda dan kwakwalwar tata tanaja yanda yakamata.
      Ina zaune ina kallonsu yana faďa mata tana rubutawa har suka gama, yakar6a yagyara mata inda batayi daidaiba.
    Ya ce, "wai ina Marwan?."
Deexerh ta ce, "yana ďakin mama uncle barci yakeyi.
   Barci da yammarnan haka?.
Ta ďaga kai alamar eh.
    Baice komaiba yamik'e yashige ďakinsa, mukuma muka cigaba da kallo.

Haka rayuwar take tafiya, ina gidansu doctor amatsayin amarya amma ta nesa, dan babu wata alak'a dake tsakanina dashi.
      Har yanzu bana shiga kicin aunty take mana girkin gidan itada 'yan aiki.
    Komai na rayuwar gidan yana tafiya yanda yakamata, saidai matsala ďaya nake fuskanta itace auntynsa, nakula ko kaďan bata sona agidan, tana nunamin abubuwa dayawa kawaidai ina sharewane.
     Kuma banta6a faďama kowaba, dan ba itabace agabana.
    Ana cikin haka kiran gaggawa yasamu doctor awajen aikinsa, dan haka yashirya yatafi badan yasoba.
     Ranar dazai tafi harda kuka nayi kashir6an mama na lallashina.
    Bayanda zanyi dole na hak'ura, deexerh tacigaba da tayani kwana, kodayaushe muna tare, dan haka shak'uwa ta musamman tashiga tsakanina da ita.
    Kullum kuma sai munyi hira da dictor ta waya indai yasamu lokaci kunsan soja sai ahankali.
    Wani abin mamaki shine tunda nazo gidan banyi al'adaba,  dan haka babu zancen ciwon mara.
     Hakan yayimin daďi, duk wata kuma sai doctor yatanbayeni, cikin jin kunya nake cemasa banyiba.
     Ana haka doctor yadawo a safiyar wata juma'a.
   Babu wanda yafaďama zaizo saidai muka gansa kawai, munyi farinciki sosai da ganinsa dan watansa na uku kenan da tafiya.
   A6angaren mama ya ara sauka. 
    Sai bina da kallo yake cikin mamaki dan ganin nayi k'iba kai harma da k'ara tsawo.
    Nikam duk kunya ta dabaibayeni dan ganin irin mayen kallon da yake bina dashi ko kunyar mama bayaji bare aunty..
    Bayan angama gaishe2, yaci abinci yak'oshi, sannan  yamik'e yana faďin mama bari naje nayi wanka na huta kafin lokacin masallaci.
    Mama ta ce, "to auta afito lafiya.
    Aunty ta ce, "nibazakamin sallamaba kenan, ko kallonta baiyiba yafice daga falon mama yana faďin ke asuwa kuma?.
   Dukda ta dake nasan maganarsa ta 6ata mata rai.
   Mama ta kalleni iman tashi kije wajen mijinki mana.
        Akunyace namik'e nafice, dan dama kunyartace ta hanani bin bayansa.

Kutashi muyi sallah ko sisters.
    Xoxo da Reefat suka mik'e kowa baiso aka katse labarinba.
    Amma damun idar da sallah zakicigaba ko??, xoxo tafaďa tana bin iman da kallo.
   Insha ALLAHU my hafsy zan cigaba damun idar..................

*Am busy* 



*Luv u oll my fan's*
*((S))......2017*
*Battery low*
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *