check your best novels here

Thursday 13 April 2017

BAN SAKETA BA!!! 10

*_________________________________*
           *BAN SAKETA BA*
*__________________________________*
                        *NA*
     *BILKEESA IBRAHEEM*
           *{bilyn Abdul}*
*___________________________________*
https://mrsbilkisa.blogspot.com 






_Sadaukarwa_~*ya Abdul {city phone's}*




*MIYA KAMATA NAYI??.*
          _amatsayina na *MUSLIMI* baidace daniba nashagala da duniya da abinda kecikinta, a *DUNIYA* ake neman lahira, to tayaya zan nemi tawa_ *LAHIRAR?*.
     _mun shagala aduniya, kalon *FILM* karatun *NOVELS* awaya zuwa *biki*.......da sauransu sunsa mata dayawa mantawa da zan *MUTU* na riski *"UBANGIJINA"* ya salam, 'yar uwa ringa tunawa da mutuwa mai zuwa babu ďan aike, ringa tunawa da *sallah*  ringa nafila, zikiri akowace rana, karkibari nishaďin duniya yasaki dana sani awata rana mai cike da *hargitsi,* tsarama kanki lokaci yanda ke da mijinki da 'ya'yanku zaku amfana, a duniyarku da lahirarku, duk wanda yay asarar *aljanna* amatsyinsa na *musulmi* to dolene atayashi kuka da jaje_.
    _muhaďu agaba domin jin yanda yakamata ki tsara_ *Duniyarki 'yar uwata*_domin keda *zuri'arki*ku amfana_ *a lahirarku*
     *ALLAH yasa mugane*.




~page.......~10.

          *............*da sallam nashiga falon babu kowa alamun *doctor* yana cikin _bedroom_ kenan.
    Dukda inajin kunya wannan bai hanani nufar ďakinba, nashiga da _sallama_.
     Yana tsaye atsakiyar ďakin yana k'ok'arin cire kayansa, yajuyo ahankali yana kallona, nikam nayi k'asa da kai saboda kunyarsa danakeji.
    Yasaki _murmushi_ mai k'yatarwa, ahankali ya ce, " *my iman* k'araso mana.
     Nak'ara k'asa da kai saboda kunya, na ce, "bari naje falo idan kagama saina dawo, wlhy bammasan kana shirin wanka bane.
       Takowa yayi cikin takun k'asaita har inda nake tsaye.
     Nikam jinake tamkar na zura da gudu, amma babu dama.......kusantowarsa gareni tasa na ďago da sauri muka haďa ido.
     Nai saurin maida kaina k'asa.
  Baice min komaiba sai kama hannuna dayayi muka k'arasa cikin ďakin sosai.
   Ya zaunar dani abakin gado sanan yacigaba da cire kayansa.
   Araina na ce, "waishi doctor baisan inajin kunyarsa bane?.
    Ina nan zaune harya gama cire kayansa, ya k'araso yazauna kusa dani dagashi sai gajeren wando.
   Yaďan rungumoni jikinsa yana magana ahankali tamkar mai raďa ko baisan tada yaro mai barci.
     _farin cikina abar alfaharina, har yanzu kunyar tawa bata k'arebane?_.
    Maimakon nabashi amsar tambayarsa sainace kadawo lafiya?.
      Yakama hannuna danake wasa dashi yaďan matsa, naďago da sauri ina kallonsa dan naji zafi.
    *Ya ďaga min gira*
  Miyasa baki bani amsar tambayataba??, saikika sakko taki tambayar??.
      Nayi murmushi wanda yakeso yaga nakasance akoda yaushe inayi, amma ina niďin _muskilancina_ bazai barniba.
     To kayi hak'uri nafaďa atak'aice.
     To nahak'ura *saudat* nasameku lafiya?.
    Lafiya k'alau.
 Ya aiki?.
    Aiki *Alhmdllh* saidai kewarki da begenki sunta addabata musamman alokacin barci.
    Ban bashi amsabama yanzu.
   Ganin haka yasa yasake matseni sosai ajikinsa, saikuma nafara masa rawar jiki, nakan bashi mamaki idan yaga nashiga wani hali alokacin daya haďani da jikinsa, amma saiya basar.
     Yamik'e tareda mik'ar dani tsaye, zomuje ki haďamin ruwan wanka.
    
   Bayan gama haďa masa ruwan wanka na ce, "nagama.
      Kafin ya ce, "wani abu nafice.
 Rakani yayi da wani shu'umin kallo, ala66ansa yafurta iman kinkusa zuwa hannu aii, kunyar nan tana cutata dayawa.
         Bayin yashiga yayi wanka yafito, dashirin kwanciya yafito amma sai yaga lokaci yatafi kasancewar yau _juma'a_ shirin masallaci yayi cikin jar shadda sai maik'o takeyi.
     Ya murza bak'ar hula da bak'in agogo, turarensa na kullum ya fesa, tunkafin yafito k'amshinsa yayo gaba.
    Na tsurama k'ofar ďakinsa idanu, yayinda yafito aisai naga tamkar ba *Dr Isma'il* ďinaba, yayi kyau harya gaji.
   Sosai na dasa masa idanuna ko k'yaftawa banayi.
    Jinai anhuremin ido".
Na sauke nannauyar ajiyar zuciya, tareda cusa kaina cikin cinyoyi saboda kunyar yakamani ina kallonsa.
    Kusadani yazauna yana dariya da faďin ďago abinki ki kalli _mijinki_ matana, niďin nakine ke kaďai.
     Ina nakasa ďagowa saboda ba k'aramar kunya najiba wlhy.
    Da kansa yaďagoni yakuma rik'e fuskar tawa tamau atafin hanunsa yanda bazan iya kwacewaba.
    Rintse idona nayi dan bazan juri haďa ido dashiba, shikam yadasamin mayun idanunsa tamkar yau yafara ganina.
   Yakai tsawon minti biyar yana kallona.
    Ban fargaba naji bakinsa cikin nawa, cikin kwarewa yake sumbatata, ban hanashiba domin nima inajin daďin hakan dayakemin, *kunsandai SO yanda yake, yakansa ka aikata abinda bakayi niyyaba*
   _dan so yahaďu da so, sai ahaďu asoye tare_
     Munkai tsawon minti ashirin ahaka, doctor yana abuďaya, saida yayi mai isarsa sanan yazare bakinsa ahankali yana maida numfashi, fuskarsa cike da *annuri na musamman*.
     Yaji daďin yanda yau natayashi abinda yakeso.
    Saidai ni kaina nayik'asa ina fidda nawa numfashin ahankali.
    Wata sassanyar dariya yasaki akunnena, cikin sigar *Salon so* ya ce, "lallai my iman kin fara haddace karatun aure.........
     Bai k'arasaba marwan yashigo shima cikin shirin masallaci, doctor ya hararesa koma kayi sallama.
    Marwan ya narke murya *ALLAH* Uncle nayi bakujibane kawai.
     Banason k'arya".
*ALLAH* kuwa marwan yaske faďa kamar zaiyi kuka.
      Na ce, "yayi sallamafa.
 Ya maido da kallonsa gareni, kinji kenan?.
    Kai naďaga batareda nayi maganaba.
   Yay k'asa da murya, kece kika rikitani har nakasaji nakasa gani, *INASONKI DAYAWA SAUDAT*.
       ajiyar zuciya nasauke ahankali, yayinda shikuma yamik'e yana kama hannun Marwan.
   My boy ya akayi?".
Marwan ya ce, "daddy ne yadawo shine na ce, "bari na sanar dakai.
    Okey my son muje.
  Saida suka kai k'ofa sanan yajuyo ya ce, "idan kinjishiru munwuce masallaci.
   Kaina ak'asa na ce, " *ALLAH* yatsare, yadawo daku lafiya.
    Amin mungide yafaďa yana fita.

      Dr da Marwan suka nufi 6angaren yaya, da sallama suka shiga.
    Yayansa yana zaune shima cikin shirin masallaci da alama su yake jirama.
   Yamik'e da sauri tareda warema doctor hannu, alamar yazo.
     Aiko da sauri yak'arasa yashige, suka rungume juna da faďin kewar dasukayi na nisantar ruhinsu.
     Yaya ya ďago kan doctor suka haďa ido suna sakarma juna murmushi, autan mama *soja* kuma *likita*, katafi kabarmu da kewarka ko??.
    Kuyi hak'uri yaya wlhy nima nayi kewarku, duk son danake nazama *soja* yanzu sainaji yafita kaina.
    Yayansa ya nunasa yana dariya anya kuwa zan yarda dakai Isma'il??.
    Dr yayi dariya, wlhy gsky nake faďama yaya.
    Rungumesa yayansa yaskeyi saboda jin daďin maganarsa.
    Aunty ta balla musu harara batareda sun ganiba, azuciyarta ta ce, "naga *rai da mutum,* k'arewar 'yan uwantaka.
    Amma afili saita ce, "zakuyi missing ďin sallaffa Abban deexerh, dan ďaya harta kusa.
    Da sauri suka saki juna suna kallon agogo.
   Tak'araso tana salo ta fesama yaya turare tareda ďora masa hularsa akai.
    Ya ce, "ngd gimbiyata.
  Murmushi tayi masa, sanan tajuyo ga doctor zata fesa masa turaren, amma saiya kauce da sauri, yana faďin a'a wanda matata tasamin ya wadatar.
    Dariya yaya yamusu ya ce, " *ALLAH*  yashiryaka Isma'il, kazama mara kunya dai.
    Fita doctor yayi yana dariya.
  Gaff sukai karo da mutum abakin k'ofa.
      Yaďago da niyyar masifa amma saiyayi shiru dan ganin wadda sukai karon.
    Suduka sun k'urama juna ido cikin wani yanayi wanda bakowane zai iya fassarawaba,  
    Bawata bace illah *Raihan* k'anwar aunty Sadiya, matar yayansa.
    Shine yafara janye nasa idon akasalance, itako Kallonsa take tamkar zata cinyeshi ďanye.
    Yadaure ya ce, "Raihan kece a kanon mu yau??.
    Tasaki dariya cikin salo ta ce, "eh wlhy *yaa Isma'il*.
    Ya ce, "sannunki dazuwa to, yafaďa yana k'ok'arin kar6ar k'aton akwatin hannunta, wanda yanuna da shirin dogon zama tazo garin na kano.
    Taďan janye tana faďin haba yaa Isma'il aiiba girmanka bane.....
     Kafin yabata amsa yayansa yafito yana faďin kaidawa auta.......?
    Maganarsa ta kakare dan ganin Raihan tsaye da kaya nik'i2, wata 'yar fara'a yasaki maikama da yak'e, a'a Raihan kece tafe??.
    Ta ce, "eh yaya, ina yini.
 Bai amsaba ya ce, "shiga ciki mana.
    Suka kauce suna bata hanya.
   Taja akwatinta da jaka k'eeyyyy zuwa ciki.
    Wani ihun murna auntyn tasaki saboda ganin k'anwarta, doctor da yayansa suka fice kowa yana sak'a mai fisheshi azuciya.

   Nikam koda yafita saina mik'e nanufi ďaki domin fesa wanka, dan inason fara amfani da shawarwarin da deexerh take bani yau da kullum, akan narage kunya wajen kula da mijina, inba hakaba wata zata samu k'ofar dazata shigo rayuwarmu.
      Na yarda da batun deexerh musamman data bani na karanta wani *Novel na bilyn Abdul* mai suna *RASHIN SANI* naga yanda *Nazeefa ta ruďa ya Mus'aff* dayake mata kallon 'yar k'auye ada, har yana gudun aurenta, amma da aunty khadija ta gyarata yadawo yaganta saiya haukace akan *RASHIN SANI*.
       to barema ni nawa mijin yana sona. 
    Nikam son danakema doctor aii bana fatan haka koda amafarkine, dan haka daga yau na zage damtsen yimasa abubuwa na ban mamaki.
    Karnayi saken da *sopy ta akan Abdul* a littafin *NI DA AMINIYATA* har fareeda ta samu damar kwace matashi, kodayake tasamu *uncle G* wanda yafi Abdul komai. 
     Saidaifa ina hangen matsala kasancewar tun shekaranjiya marata take ciwo kaďan2, ina daurewane kawai saboda batamin ciwo kamar da.
      Haka na daure ina cije baki ina kwalliya tamkar dole.
  Na tsara kwalliya tagani da faďa, nasan kowa yaganni saiya sake kallo kodan k'yawun danayi na musamaman.
    Nidai doguwace sosai kamar yanda kuka sani, dan tsawona yasa har 'yar rankwafawa nayi kaďan, banida k'iba gsky dan kamar ahureni haka nake, bazance inada tsananin k'yauba amma *Alhmdllh* muna tsaka tsaki, inada ďan haskena iya gwargwado dan ba'a kirani faraba, idan ina kusada masu ra'ayin babu _chocolate colour_ aduniya, to dole akirani bak'a kuwa, _(dan wasu sunce kala biyu suka sani aduniya daga bak'i sai fari)_.
       Hancina kam ba dogo bane, saidai nace gajere, ga idanuna atsaka tsaki suba manyaba bakuma k'ananaba, ďan gashina daidai wadaida masha ALLAHU.
     wanan itace surata ni saudat amusalce, kunga kuwa niba mai mugun k'yau bace tafaďa da nunawa, irinmuma ba'a sakamu gaban mota ace za'a farty.
     Wata uwar harara *xoxo* tamata, ta ce, "iman aii dai godema ALLAH, duk wanda ya ce, "bakida k'yau saidai _hasidin iza hasada_ wanda yakali sama ya ce, "akarkace take".
     Reefat ta tuntsire da dariya, gskyar kine my xoxo.
   Bagashi ta haukata mana *Dr Isma'il* ba.
    Gaba ďaya suka shek'e da dariya suna tafawa.
    *(na ce, "kai 'yammatan nan suna burgeni ni bilyn Abdul)lol🏻* ...............🏻


    
*((S))........2017*
*luv u oll my fan's*
*Battery low*
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *