check your best novels here

Thursday 27 April 2017

BAN SAKETA BA!. 15

*________________________________*
      *BAN SAKETA BA!*
*________________________________*
                       *NA*
      *BILKEESA IBRAHEEM*
             _*{bilyn Abdul}*_
*________________________________*






_sadaukarwa_ *ya Abdul {city phone's}*




*MIYAKAMATA NAYI?.*
         _'yar uwa! ďan uwa!, yakamata dani dake da kai mutaru mu mutunta juna, k'yautata mu'amularku da jama'a 'yan uwanku, walau musulmai ko ba musulmaiba_
     _karku zama masu girman kai, saboda wata ďaukaka ta duniya, babu wanda yafi wani gurin ALLAH sai wanda ya k'yautata ibadarsa, to ashe nidake da kai duk bamuda tabbas, domin duk k'ok'arin ibadarka wani yafika, ballema yanzu damuka lalace, muka shagala aduniya da kayan cikinta._
    _saika samu mutum yahaďa shekara ďaya bai karanta *alkur'ani* ba, baya sallah akan lokaci, baya neman ilimi akan addininsa, baya tunawa da *ubangijinsa* sai masifa ta rikesa sanan ya ce, "ALLAH ne ya ďora masa, humm kaji ďan adam sarkin butulci da izgilanci, duk sanda alkairi yasamesa saiya ďauka wayonsa da iyawarsace tabasa, wanan kuskurene da jahilci._
    _mudaure murunga neman _ilimi akan addini, bawai aboko_ kawaiba, _saikaga mutim yanata_ _fafa shi yanada digiri ko_ _difloma_ _ko yana karatu a jami'a kaza, amma_ _wlhy idan zaka tsaresa bazai iya_ _kawo maka alwala cikakkiyaba,_ _bare azo ga sallar kanta, amma_ _turanci da iya salo abakinsa ko_ _mista k'yarank'yan yashafa_ _masa lafiya, larabcikan sai ace_ _aiba yarena bane._
    _to hajiyata alhajina shi turanci yarenkine?, hasalima turancin namak'iyankine, afannin addini al'ada jinsi, dan bature bazai ta6a k'aunar musulmiba kuma bak'in mutum, larabci kam abin al'faharinkine tunda koba komai *Annabinmu* yafito daga wanan tsatsonne._
   _Inaga lokaci yayi dazaki gane ka gane na gane cewa da mutunci ake gano mutunci, da ilimi ake gano gyara, to *miya kamata nayi?* na nemi ilimi na addini bawai boko kawaiba._
   *ALLAH yasa muga ne.*




*~page.......15~*
     
          ..................da sauri deexerh ta rik'eni nafaďo hannunta dan tuni numfashina ya tsaya, k'arar da deexerh ta kwallace ta jawo hankalin jama'ar gidan harda yaya dadyn su deexerh.
      Da gudu suka iso 6angarenmu suna tambayar lafiya??, ganina akwance yabasu tabbacin nice babu lafiya ba deexerh ba, aunty ce tafara cewa akira doctor, amma yaya yahana, wani abokinsa aka kira, kafin ya iso yaya yazare takardar daya gani ahannuna, tuni zufa ta wanke masa dukkan sassan jikinsa, sai k'ara maimaita karanta takardar yake kamar wanda akabama hadda.
    Ya maimaitata yafi ak'irga, tuni kuwa ya haddace komai dake cikin takardar, mama tana lura da halin dayake ciki, zuwan doctor ne yahanata tambayarsa.
    Dr Auwal yadubani tareda mak'alamin k'arin ruwa, ya ce, "insha ALLAHU zuwa anjima zan tashi normal, yanzuma wani abune ya firgitani na suma, amma na farfaďo.
    Godiya sukai masa sanan yatafi.
     Dama tuni yaya yabar wajen, yana 6angaren mama, acan mama tasamesa zaune akujera kamar gunki, idonsa cike da kwallah, zuwan mama yasa yatashi sosai, yasa gefen rigarsa ya share kwallar data gangaro masa kaďan agefen ido.
    Jiki asanyaye mama ta zauna dan tabbas tasan ba lafiyaba, yaya yanada k'ok'arin 6oye damuwa komai tsananinta, amma yanzu hakan ya gagara, cikin sark'ewar murya mama ta ce, "Mansur miya faru ne?.
     Yaya yaja ajiyar zuciya, muryarsa naďan rawa ya ce, "mama Isma'il ya saki iman!!.
       Cikin wani irin yanayi mama take kallonsa, ta ce, "ban ganeba Mansur mikakeson faďamini?.
    Takardar hannunsa yamik'a mata, ta kar6a takaranta.....
    *ni Isma'il Muh'd basheer!. Nasaki matata saudat sulaiman saki uku!!. Idan tasamu miji tayi aure.*
      Tuni gumi ya wanke jikin mama, bata buk'atar k'arin bayani danhaka tayi tagumi kamar yanda yaya yayi.
    Yayane yay k'arfin halin faďin mama amma yaronnan ya cucemu, yanzu dan ALLAH dawane ido zamu kalli iyayen yarinyarnan?, ni abindama yake bani mamaki shine miya haďasu dahar zai mata saki har uku?, miya hau kan yaronnan haka?, kuma wlhy mama rubutunsane barema ya musa mana.
     Mama taja ajiyar zuciya toni Mansur ai komaima ya kwace mini, bansan yanda zan kira wanan abinba kuma.
    Haka mama da yaya sukaita tattaunawa, kuma wani abun mamaki sunkira wayar doctor arufe, mama ta ce, "tunda yasan miya aikata ai dole yakashe waya, kabarsa kawai.
     Nikam ina ďaki ina barci, aunty da deexerh da Raihan suna 6angarena, saidai basusan abinda yake faruwaba, dan deexerh ma bata karanta takardarba tunda tana zuwa ina suma.
    Haka akaita tafiya har zuwa yamma dana farka, mama dakanta ta taimaka mini nayi wanka, aka bani abinci naci kaďan har zuwa sanan kuka nake rurus.

*bayan kwana uku*
         Yau tsawon kwana uku kenan angaza samun number doctor kwata2, nikuma namatsa zanje gida, dan yakama iyayena su san halin da'ake ciki, mama da yaya basaso natafi, hakama deexerh da marwan, amma yaza'ayi da k'addarar ALLAH, ganin namatsa yasa mama da yaya suka kaini har gida.
    Bak'aramin ruďani gwaggo tashigaba itada Abbah dajin abinda yafaru, dan su yaya basu 6oye musu komaiba, suka ďora dabasu hak'uri.
    Abbah ya ce, "babu komai haka ALLAH ya k'addara aii, bayan ďan tattaunawa dabawa juna baki su yaya suka tafi aka barni agida.
     Tunda nadawo gida banida wata walwala, kulum cikin kuka nake, ga rashin lafiya data tasoni gaba, dandanan nayi bak'i na rame kamar baniba, lokacin da labari yakai kunanen aunty salma da ya majeed ransu ya 6aci matuk'a, ya majeed ya ce, "bazai k'yaleba saiya ďauki mataki akan doctor, da k'yar abbah da gwaggo suka shawo kansa ya hak'ura.
     Ganin yanda na k'untata kaina agidan yasa ya majeed rok'on abbah yabari nakoma wajensu k'ila zanfi samun sakewa, abbah baiyi musuba dan dama farin cikina yakeso, aranar muka tattara muka koma.
      Acanma haka nayita rashin lafiya wadda tasa dole suka kaini asibiti, tofa wata sabuwa, bayan gwaje2 da likita yayi ya tabbatar mana inada ciki na sati uku, tun agurin nasa kuka sai anzubar dashi, amma ya majeed ya hana.
     Ranar nayi kuka harna godema ubangijina, duk wanda yaganni saiya tausaya mini.
    Muna dawowa gida ya majeed yasanarma su abba halin da'ake ciki, aranar kuma aka sanarma gidansu doctor, mama da yaya sunyi matuk'ar murna da wanan abin farinciki, dan cikin zai zama sanadin cigaban zumincin mu.
     Har tsawon wata ďaya babu labarin doctor kota waya bare kuma ayi maganar dawowa.
     Nikam inanan a6oye inata k'ok'arin zubar da ciki, duk abinda naji ance yana zubar da ciki saina sha a6oye, amma abanza wai man kaza, dan ciki ko gezau, saidai nasha azabar ciwon cikina.
    Ahaka aka akai wata biyu da sati ďaya.
     Awata ranar alhamis doctor yazo kano, saidai kuma yatarar da sabon tashin hankali, dan kowa ya ďauke masa wuta agidansu.
    Kowa ya tambaya iman sai suyi masa banza harsu marwan da deexerh.
      Hankanlinsa yatashi matuk'a, inda yaga sunk'i bashi wata amsa ta gamsarwa sai kawai ya tsare deexerh da marwan da bulala.
    Tsoro yakamasu sosai dan ganin yanda yaburkice musu ďinnan zasu iya shan duka abanza, aiko suka sanar dashi komai, atake jikinsa yay sanyi, yanufi wajen mama hankali tashe.
     Agabanta yashiga rantsuwar wlhy *BAN SAKETA BA!* mama, na rantse da ALLAH k'arya takemini.
     Mama tayi masa banza, wuni guda yana magiya da rok'o amma kowa yak'i saurarensa, dayaga nan babu ci saiya nufi gidanmu, to gara nan abbah yayi masa nasiha da nuna masa muhimmancin yarda da k'addara.
    Shidai doctor bashida wata magana sai *ban saketa ba*, tun suna kallon abun amatsayin wasa harya fara zarta tunaninsu, dan doctor neman zare musu yakeyi, awani daren litinin sai a asibiti ya kwana.
     Wasa2 dai al'amira sun fara tsauri, doctor baisan waye akansaba, kuma indai idonsa biyu bashida magana saita *ban saketa ba*, wannan yasa hankalinsu yayansa yafara tashi suka fara tausayinsa kuma, dan abin yafara wuce makiďi da rawa.
    
   Ahaka cikina yashiga wata biyar, nima kaina nazama mara lafiyar, kulum daga tunani sai kuka, duk sanda na kalli cikina sainayi kuka, har banason tuna inada ciki, duk halin da doctor yake ciki labari yana zuwa mini, dansu aunty salma suna zuwa ganinsa hakama su gwaggo.
    Jikin doctor yay tsanani dole aka maidashi k'asar indiya, dan ciwon zuciya yana neman aikashi lahira, kowa yana tausaya masa.
    Ban ta6a zuwa ganinsaba saidai kusan tare muke jinyar dan kullum zuciyata tana damuwa da halin dayake ciki.
       Karna jaku da nisa, haka cikina harya cika wata tara, zuwa sanan jikin doctor da sauk'i amma ba'a dawo dashi 9ja ba yana indiya abinsa.
    Awani dare juma'a na farka da nak'uda, cikin hanzari muka nufi asibiti, tun anasaran zan haihu acikin awa biyu har likitocin suka fidda rai, dan har washe garin ranar haihuwa shiru sai bak'ar azabar danake sha.
     Har k'arfe sha biyun rana haihuwa shiru, zuwa sannan k'arfina yagama k'arewa, ko ďaga hannuna bana iyawa bare kuma nayi wani nishi, ganin halin danake ciki aka yanke shawarar yimini aiki.
     Babu musu su abbah suka yarda, dadyn su deexerh yasa hannu a maimakon doctor, aka shiga dani  ďakin tiyata.
     Ancuromin yaro namiji k'ato mai kama da babansa kamar an tsaga kara, lallai yau naga farinciki wajen dangin doctor danawa dangin, kowa kamar yacinye yaron haka yakeji, haka nima kowa yana tausaya mini da addu'ar samun lafiya.
     Duk wata hidima yayansa yayita, kuma shima ansanar dashi na haihu, yayi farinciki kuma yasha kuka, dan ranar saida ciwonsa yak'ara tashi, likitoci sunata faďa akan adaina gaya masa komai daya danganci 6acin rai.
    Ina gadon asibiti har tsawon sati uku, dan haka ba'ayi taron sunaba, andai raďama yaro suna *Musayyeef*, to iman ALLAH yaraya mana musayeef, amin.
     Bayan sati uku aka sallamemu, amma wannan karon gidanmu aka dawo dani, dan ina buk'atar kulawar gwaggona, haka nacigaba da rainon musayeef wanda kulum kallonsa yanasani tunawa da ubansa, dan kamarsu tayi yawa matuk'a, kullum mama tana k'ok'arin kwantar da hankalina, ahankali yauda gobe harna dake, komai yafara zama tarihi na maida hankalina akan rainon musayeef.
      Musayeef yanada wata ďaya da kwanaki aduniya aka dawo da doctor gida, danya samu sauk'i sosai, shima yawan addu'ar da aka dage ana masa yasa yadake yanzu, kwanansa uku da dawowa yayansa yarakosa yaga musayeef, jiyayi kamar yamaida musayeef acikinsa, yana matuk'ar k'aunar ďansa gudan jininsa, dak'yar yayansa ya lalla6ashi suka tafi.
    Yayi yayi yaganni amma nak'i amincewa, dole yahak'ura suka tafi wani abu na sukar zuciyarsa.
    Daya koma gida saida aka haďa da lalashi, dan yanzu ba'aso yana tada hankalinsa.
    
Haka naci gaba da rainon musayeef nida gwaggo harya shiga shekara ďaya, asanane kuma ya majeed yabada shawarar nazana s,s,c,e ďina nakoma karatu, abbah ya yarda da shawararsa, dan haka nayi Exam, cikin amincin ubangiji nasamu result mai k'yau, dan haka ba'asamu matsalaba wajen nema mini makaranta.
     ALLAH yacidani samun nan (A B U zariya), samun makarantar yasa na yaye musayeef na maida hankalina akan karatuna.
       Shima doctor yakoma aikinsa yabarma ubangiji komai, amma lokaci2 yana zuwa duba musayeef, hakama yaya da mama da aunty.
    To yanzudai ansaka musayeef makaranta kuma yayansa ne da wanan aikin, idan anyi hutu yana zuwa gidansu hakama weekend ana kaisa yayi kwana biyu.
    Tunda nabaro gidan bansake haďuwa da doctor ba, bamma k'ara zuwa gidanba, idan yazo ganin musayeef kuwa bana yadda muhaďu, zadai akai masa ďansa, kuma susha hirarsu da gwaggo, ammani yagagara ganina, garama lokacin da maman su deexerh zata koma gidan naso zuwa amma ALLAH bai k'addaraba.
    Xoxo ta ce, "oh maman su deexerh takoma??.
   Eh yaya ya maidata yanzu hakama tana gab da haihuwa deexerh tace min.
    ALLAH sarki kai natayata murna wlhy, musamman ma su deexerh dan babu abinda yafi karayu da 'ya'yanka daďi.
    Wlhy hakane xoxo Reefat tafaďa.
     Iman ta ce, "to wanan shine sirrin dana daďe ina 6oye muku.
   "To miyasa kike yawan waige2? cewar Reefat.

 Iman tayi murmushi, wato tunda nazo makarantarnan lokuta da dama nakanji turaren doctor ya yawaita awaje, wanan shine ke sakani yawan kuka da waige2, kuma kunga ranar nagansa, wanan yatabbar mini dashi ďinne saidai yana 6oyema ganina.
     Tabbas labarin iman ya girgiza k'awayenta Reefat da miss xoxo, kuma sunyi alk'awarin taimaka mata har agano gsky, dan suma basu yarda cewa doctor ya saketaba, sunaji ajikinsu *bai saketaba*, amma basu sanar da ita zasuyi komaiba.
    Saidai sun tanmbayeta yanzu ina deexerh?.
      Deexerh tana nan, tana karatu a jami'ar abuja yanzun.
    "Kuna waya?".
 Eh muna waya sosai da ita, kuma aii kunsan haka, saidai sanan bakusan wacece itabane.
   Hakane suka faďa, xoxo ta ce, "yakamata mukaima deexerh ziyara.
    Iman tazaro ido ziyara kuma?, tanafa makaranta nece, eh aii makarantar zamuje, amma sai weekend, tunda bawani nisa bane tsakanin zariya da abuja.
     Shiru iman tayi dan batasan amsar daya kamata tabasuba, Reefat ta ce, "iman kinyi shiru.
    Ajiyar zuciya iman tayi, bashiru nayiba Reefat kawai ganin abun nake abaibai.
    Babu wani baibai, deexerh sa'ar muce, kuma tana k'aunarki aii yakamata zumincinku yacigaba karya yanke.
    Xoxo ai zumincinmu bai yankeba tunda muna gaisawa, kuma idan ina kano tana zuwa aii mugaisa, tana zuwa ta ďauki musayeef.
   Eh dukda haka, yakamata mukai mata ziyara.
    To shikenan saimu duba ranar daya dace saimuje kenan.
   Okey ALLAH yakaimu.

Ammafa iman kinsamu akwali, wlhy da duk zatonmu gwaggo ta haifi musayeef.
   Dariya iman tayi ta ce, "tokuyi hak'uri.
   Suma suka dara tareda faďin yayuce, munyimi uzuri.................







_*((S)).........2017*_
_*luv u oll my fan's*_
_*battery low*_
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *