check your best novels here

Thursday 13 April 2017

BAN SAKETA BA!!! 3&4

*____________________________*
              *BAN SAKETA BA!!!*
  *_______________________________*
                        *NA*
        *BILKEESA IBRAHEEM* 
               *{Bilyn Abdul}*
*________________________________*
https://mrsbilkisa.blogspot.com 




_Sadaukarwa_*~ ya Abdul (City phone's)*




*MIYAKAMATA NAYI???.*
       _Kasancewata uwa yakamata nayi 'kyakykyawan lafazi ga ďan daba nawaba alokacin danaga yayi ba dai2ba, karna la'anci ďan wani kona kirashi lalatacce, shiriyar ALLAH yakamata na ro'ka masa, domin ďa na kowane, bansan mi gaba zata haifarba akan nawa 'ya'yan._
   *ALLAH yasa mu gane.*



_Page..._3⃣

       Ya majeed kam yana office ďin Dr Isma'il, bayan sun zauna Dr Isma'il ya kalli ya majeed abokina ba wata matsala bace take damun 'kanwarmu ba, ciwonsu ne na mata, dan tafara period ne, saidai yazo mata da matsalar ciwon mara, amma karku damu dama hakan yana faruwa, zamu bata magani insha ALLAHU komai zaiyi dai2, inagama zuwa anjima zan sallameku inasha ALLAH.
    to abokina mungodefa sosai ALLAH yabar zuminci.
   Daga nan sukaďanyi hira ya majeed ya fito dan Dr Isma'il yanada masu jiransa.
  
Aranar aka sallamemu muka dawo gida, washe gari da yamma saiga Dr Isma'il yazo gidan ya majeed.
   An masa tarba ta mutunci, bayan an gama gaishe2 ya ce, "ni banga patient ďinaba kumani ita nazo dubawa.
   Aunty salma ta ce, "tana ďaki tanakuma jinmu inaga miskilancinne ya motsa mata, bari nakirata, bayan aunty Salma ta kirani na saka hijjab nazo, suna zaune a falo Affan yana cinyar Dr Isma'il, na zauna a'kasa cikin jin kunya na gaidashi, duk miskilancina da shagwa6a inada tsananin kunya.
    Cikin fara'a ya amsa, ya ce, "my patient ya jikinki??,
 "Na ce, "da sau'ki.
  ''Ya ce, "ALLAH yakara sauki.
  Na ce, "amin.
     Nami'ke da nufin komawa ďaki, Dr Isma'il ya ce, "a'a my patient sai ina kuma??, Na ce, "zanje cikine, ya ce, "da wuri haka?, kofa gaisawa bamuyiba kuma zuwannan nakine.
   Nayi murmushi wanda mutane dayawa suke faďamin yana 'kara min 'kyau, kasancewar ban cika yiba saboda miskilancina, idan nayi kumatuna sukan lotsa.
    A zuciyarsa ya ce, "ya salam yarinya 'karama zata haukatani.
  Ganin kallon dayake mini yasani tashi da gudu na shige ciki, yabini da kallo yana murmushi harna 6acema ganinsa sannan yaja ajiyar zuciya.
   Ya majeed ya ta6ashi abokina miye damuwarka??, Dr Isma'il yasaki sassanyar ajiyar zuciya sanan ya ce, "brother 'kanwarka ce damuwata, saidai tayi 'kan'kanta dan na lura bata wuce sha biyarba.
    Ya majeed ya tuntsure da dariya kai Isma'il wlhy kaidai baka rabo da wasa, kai yanzu idan ance ka tsaya jiran iman saika tsaya??.
     Dr Isma'il ya ce, "kajika da wata magana, aini koba ace najirabama zan jira kuma zaka sha mamakina.. 
  To ALLAH ya taimaka amma saidai ta biyu ko??, harararsa Dr Isma'il yayi, ta biyu kota ďaya, aini kasan babu mata biyu a tsarina saidai kaddarar ALLAH, dan babu inda bata kai mutum.
    Ya majeed ya jinjina kai yana murmushi, amma abokina kana ganin ya Mansur da mama zasu yarda, yakamata fa ace kayi aure tuni, kosaika zama tunzurun zurun ne?.
    Dr Isma'il yay dariya, kana min wula'kanci wlhy majeed kaima naga duka shekararka nawa da auren?, su yaya kuwa banida matsala dasu, abinda nakeso suma shi suke so, kaidai katayani da addu'ar neman za6in ALLAH kawai.
    Shikenan ALLAH yaza6a mana abinda yafi alkairi.
  Amin Dr Isma'il yafaďa.

Da dai ya majeed ya fahimci Dr Isma'il da gsk yakeyi, saiya shige masa gaba awajen Abbah.
   Abbah yayima Dr Isma'il tambayoyi kamar yanda shari'a ta tsara, yako amsa masa yanda yadace.
   Saiya bashi izinin neman SO a wajena, nikam bammasan abinda ake cikiba, dan lokacin da nadawo gida mun koma makaranta.
       Kai kutashi muyi sallah ďaya ta wuce, kuma ALLAH yunwa nakeji, Xoxo ta harareta ALLAH iman kin iya wula 'kanci saida labarin yafara ďaukar daďi zaki 'kir'kiroma mutane wani jin yunwa, inama laifin muyi sallar??.
    Iman tayi dariya sorry dear karki damu aii idan tunbi ya ďauka labarin saiyafi daďi ko??.
   Reefat ta ce, "ALLAH ni ko yunwarma banaji, burina kawai naji 'karshen labarinnan, karku damu aii muna gamawa zan cigaba.
   To gsky saidai asiyo abincin ko asake cin indomi dan in ba hakaba girki zai 6ata mana lokaci, gsky ne Xoxo kunga kuyi sallar tunda ni an hutar dani, kafin ku idar naje na samo mana abinda zamuci ko bai yiba??.
   Sukace yayi.
 Bayan sun gama cin abinci iman ta ce, "saitayi wanka sanan, saida tagama ja musu rai sanan taci gaba.

Dr Isma'il yakasa sanar dani sirrin zuciyarsa saboda yana min kallon 'karamar yarinya, dan gsky asanan ban wuce sha biyar ba.
    Ahaka wata yazagayo al'adata tazo nasha wahala sosai, su gwaggo suka rasa yanda zasuyi dani, na daure na ce, "sukira aunty Salma.
    Babu 6ata lokaci aunty Salma tazo muka tafi asibiti wajen Dr Isma'il, shiyya dubani yamin allura yaďan kwantar dani na yini ďaya.
   Daga nanfa ciwon mara yazamemin jiki, har fargaba nake wata yazo, hakama gwaggo tana tausaya mini sosai.
    Ana haka Dr Isma'il yazo ma Abbah da zancen zai shiga soja, dan dama burinsa kenan tun yana yaro, amma saboda yayansa yanason yazama likita ya ha'kura yayi karatun likita, to yanzu damace tazo masa, shine yakeson yayi amfani da ita.
   Abbah ya ce, "ALLAH sarki, ai haka akeso Isma'il mutum duk inda yake yazama mai biyayya ga nagaba dashi, saiyaga yazama abinda baiyi zatoba arayuwa, dan masu iya magana nacewa dana gaba ake gane zurfin ruwa, to inamaka fatan Al'kairi arayuwar ka, domin kai yaron kirkine, ALLAH yabada abinda akaje nema, kuma ayo nasara.
   Amin Abbah nagode da addu'arka gareni ALLAH yasaka da al'kairi, babu damuwa abba yafaďa, kaga bari naturo maka iman ďin kuyi sallama ko??.
   Cikin jin kunya Dr Isma'il ya ce, "Abbah dama ka 'kyaleta.
   Abbah ya ce, "sabodami Isma'il?, ba sallama zakuyiba?, Dr Isma'l yaďan sosa gefen wuyansa saboda jin kunya ya ce, "Abbah karka damu, iman tayi 'karamane yanzu, inason saita gama koda secondary ne, saina fahimtar da ita nufina akanta, amma yanzu za'a raba mata hankali gida biyu.
   Abbah yay dariya to shikenan Isma'il ALLAH yay maka albarka, yakuma bada sa'a akan abinda akaje nema.
   Dr Isma'il ya ce, "Amin Abbah ngd da 'kaunarka gareni.
  Abbah ya ce, "karka damu aii kai yaron arzi'kine wanda ya cancanci a 'kaunacesa fiyema da haka..  
   Daga nandai sukayi sallama, Dr Isma'il yatafi training ďin soja na wata shidda..
   Nikam ban saniba, nagadai bana ganin yana zuwa wajen Abbah yanzu kamar yanda yakeyi da, ban ta6a yun kurin tambayar waniba, dan babu wata ala'ka tsakanina dashi banda ta mara lafiya da likita, haka nacigaba da shan wahala duk 'karshen wata, dukda wani likita yana dubani a asibitin su Dr Isma'il, amma bai iya shawo matsalata kamar Dr Isma'il.

Awata Asabar datayi dai2 da dawowar Dr Isma'il kano, dan ayanzu yazama soja, ALLAH yacika masa burinsa, yazama likitan sojoji, gashi likita gashi babban Soja.
   Aranar natashi da matsanancin ciwon mara wanda zan iya cemuku tamkar yafi na kullum ma dan har suma nake, gaba ďaya hankalin iyayena yatashi, ankira likitan dake taimaka min yaymin allurar amma abanza dan babu abinda ya canja agareni, har zuwa 'karfe huďu na yamma, saidai yalafa yadawo.
   Awanan lokacin tuni Dr Isma'il yana gida yana hutawa, amma sai barcin ya gagari idanunsa, dan tunda yashigo kano gabansa ke faďuwa zuciyarsa tanata kwaďaita masa son ganina, dan ba 'karamin kewata yayiba acikin shekara ďayar nan.. 
    Zumbur yami'ke yacanja kayansa zuwa shadda mai 'kyau ďinkin zamani, dan Dr Isma'il yanada 'kyau babu laifi, yafito falo yana ďaura agogo, auntynsa matar yayansa ta ce, "a'a angona sai ina kuma??.
        Dr Isma'il yay dariya angon iman dai, kekam ga angonki nan akusada ke, ya nuna yayansa dake zaune yana masu dariya.
   Ta ce, "wacece iman kuma??.
  Dr Isma'il yay murmushi karki damu zaki santa kwanan nan, yanzuma sauri nakeyi amma kibini bashi idan na dawo zan sanar dake iman, yafice yana faďin yaya aunty saina dawo, yanaji tana kwala masa kira amma bai sauraretaba, motar yayansa ya ďauka yafice danshi bashida mota sai mashin, yayansa kuma baya masa shamaki da nasa motocin.
    Yayansa ya tuntsure da dariya nikam kina bani mamaki keda Isma'il ke yanzu har kin yarda da zancensa ne??.
   To ya bazan yardaba tunda bai ta6a kawo mana makamanciyar wanan maganarba.
   Ito hakane ALLAH yasa da gsk yakeyi.

Dr Isma'il kuwa kaitsaye gidanmu yanufo, yay parking a kofar gida, yana tsaye gaban motar saiga deeni yadawo daga aika.
    Dr Isma'il ya ce, "zomana abokina, babu musu deeni ya'karasa garesa, ya gaishesa.
   Dr Isma'il ya ce, "dan ALLAH shiga gidanan kamin sallama damai gidan.
 Deeni ya ce, "wai Abbah??.
  Eh shinake nufi, ko kaima ďan gidanne ?, dan naga kana kama da Iman.
   Ya ce, "lah ina kasan aunty iman??, Dr Isma'il ya ce, "anan gidan, to aii yanzuma itace batada lafiya dan har suma takeyi, aruďe Dr Isma'il ya ce, "suma kuma??, deeni ya ce, "eh suma, to yanzun Abbah na nan?, eh yana ciki, jeka ce masa Isma'il ne yazo gunsa.
   Deeni yazo ya sanar da Abbah, Abbah yanajin Dr Isma'il ne da hanxari yafito, bayan sun gaisa Dr isma'il ya ce, "yanzu wani yaro yake sanar dani Iman babu kafiya?.
  Eh hakane Isma'il.
      Sun shigo gidan, sanda suka shigo inata mur'kususu ajikin gwaggo dan har wani shiďewa nake saboda azabar ciwo, gwaggo sai kuka take.
   Dr Isma'il yakalli Abbah aruďe Abbah idan bazaka damuba na ďauketa muje asibiti mana.
  Abbah ya ce, "babu wata matsala Isma'il......aibai bari Abbah ya 'karasa faďaba ya sunkuceni yay waje, amota yasakani Abbah yakaraso da hanzari yashige muka tafi asibiti, acanma ďaukata yayi, ďaki guda aka waremini nikaďai, ya shiga bani kulawa ta musamman, cikin 'yan mintina ya shawo kan matsalata harna samu barci................







                           *♡☆♡
_Page......_4⃣

..........Washe gari nadawo dai2 ina kwance agado gwaggo tana zaune akusa dani, aunty Salma kuma tana tsaye tana waya, Dr Isma'il yaturo 'kofa yashigo da sallama, rissinawa yayi ya gaida gwaggo, gwaggo tami'ke tafita dan tanajin kunyar sirikin nata, itama aunty Salma saitayi waje, Dr Isma'il yajawo kujerar da gwaggo ta tashi ya zauna kusadani ya tsuramin idanu Iman ya jikin naki?.
    Cikin jin kunya na ce, "da sau'ki.
yanzun babu inda yake miki ciwo?.
 na ce, "babu, ya ce, "Alhmdllh.
   Ince dai kinci abinci ko?, naďan kalleshi ta gefen ido na ce, "a'a na koshi, ya ce, "mikikaci da har kika 'koshi?, na ce, "nasha tee ďazu.
    Yay murmushi kice na shirya nemo maganin cin abinci matata batason cin abinci, da sauri na kalleshi, ya kannemin ido ďaya tareda ďaga gira, hannu nasa na rufe fuskata saboda kunya, ya ce, "inson mace mai kunya ashe ALLAH zai bani, na kuma cusa kaina cikin cinyoyina.
   Yay dariya sanan ya ďauki filet, kulan da aunty salma tazo dashi ya buďe, ya ce, "iman lallai ke 'yar gatace, wannan irin farfesu haka, nidai kaina na tsakiyar cinyoyina nakasa ďagowa saboda kunyar maganganunsa.
     Ya zuba farfesun yace nazo naci nasha magani.
  Na ďago kaina cikin jin kunya na ce, "kawo to, ya ce, "waneni da barin gimbiya cin abinci da kanta, aii da hannuna zan baki, na ce, "A'a ngd zanci da kaina, ya ce, "nikuma ban yardaba, haka dole na hakura yabani da kansa, saidai cikin matu'kar jin kunya nake kar6a, shikam sai dariya yake mini.
    Aranar aka sallameni muka koma gida.. 
    Kunaga kutashi muyi sallar la'asar sanan saimu cigaba.
   Bayan sun idar da sallar la'asar iman ta ďora labari.

Iman tabi Reefat da Xoxo da kallo tareda jan numfashi, wato 'yan uwa bayan kwana ďaya da sallamata Dr Isma'il yazo gidanmu, an masa tarba ta mutunci, dan su gwaggo suna son Dr Isma'il sosai.
    Bayan sun gama gaisawa Dr Isma'il ya ce, "Abbah dama nazone nayi muku bayani akan ciwon iman.
   Abbah ya ce, "ina saurarenka Isma'il.
   Dr Isma'il yay 'kasa da kai sanan ya ce, "wato Abbah naďanyi bincikene akan ciwon iman, saina gano ta hanya ďayane kawai zata iya rabuwa da ciwon, hanyar kuma itace......saikuma yayi shiru, Abba ya ce, "inajinka Isma'il karkaji komai ka sanar dani, Dr Isma'il ya 'kara kasa da kai dan maganar tayi masa nauyi abaki, amma ya daure ya ce, "hanyar itace aii mata aure, ta wanan hanyar kawai nake ganin za'a samu mafita.
     Abbah yay murmushi to aii Isma'il inadai hakane banida damuwa tunda lafiyarta muke bu'kata, inaga indai har iyayenka sun amince saisu turo, inyaso saita cigaba da karatun a ďakinta, dan haka nabaka dama kaje kayi shawara da nagabatanka, nima zanyi da gwaggonsu dakuma 'yan uwana.
 Dr Isma'il ya ce, "to ngd ALLAH ya 'kara girma.
  Abbah ya ce, "amin, yami'ke yana faďin bari na turo maka maman tawa.
      Bayan Abbah yashigo ya ce, "naje falon ba'ki ana jirana, na ce, "to, hijjabi nasaka na nufi falon, yana zaune akujera mai zaman mutum ďaya, yana cikin farar shadda ďinkin boda amma babu hula akansa, yayi min 'kyau sosai, dan Dr Isma'il farine 'kyakykyawa, yanada suma mai 'kyau wadda take shan gyara, bayida saje saidai wani ďan gemu na gayu daya ajiye, wanda ya'kawata 'kyawun fuskarsa, dogone sosai yanada 'yar kiba daidai misali, akwaishi da yawan fara'a, dan a yanda nakula kamar ba miskili bane.
    Da sallama na shigo 'kamshin turarensa ya bigi hancina, inason kamshin turaren tun sanda aka fara kaini asibitinsa, yaďanja gilas ďinsa kaďan zuwa 'kasan ido, yakuramin idanunsa matsakaita girma, na zauna saman carpet, yay saurin faďin a'a ban yardaba tashi ki hau kujera, cikin jin kunya na ce, "nanma ya isa.
    To shikenan nima bari na sauka kasan tunda nan kikeson mu zauna, ganin zai zauna kasa nayi saurin hawa saman kujerar,    ya tuntsure da dariya to shikenan gimbiya,  nidai kaina yana 'kasa na gaisheshi, ya amsa cikin fara'a, sanan ya ce, "ya jikinki??.
    Na ce, "aii ni na warke.
    Ya ce, "zakidai warke in sha ALLAHU nan gaba kaďan.
   Murmushi kawai nayi batareda nayi maganaba.

Ya gyara zamansa sosai, tareda 'kara daidaita nutsuwarsa, yayďan gyaran murya alamar maganar dazaiyi tanada muhimmanci.
    Ya ce, "imaniii nasan kin sanni tunba yanzuba, tun sanda aka fara kaiki asibiti a matsayin patient ďina??, na ďaga kai alamar hakane, ya jin jina kai, to tun aranar naji kin kwanta min arai, nakamu da sonki na gsky, dalilin dayasa na sanar da majeed abinda ke raina kenan, shine ya shige mini gaba zuwa wajen abbah, banyi kasa aguywa ba wajen sanar da abbah sirrin zuciyata.
    Alhmdllh Abbah ya fahimceni yakuma kar6eni amatsayin siriki, tunkuma a wancan lokacin ya mallaka minke, yakuma bani damar neman so awajenki.
    Alokacin nayi wani nazari akanki, dan na lura ke yarinyace karama, wanan dalilin yasa na ce, "abarki sainan gaba, dama na sanar dasune kamar yanda addinina ya koyar dani, to saikuma wani uzuri yatasomin alokacin, natafi training ďin soja saboda tuni inason zama soja, saidai yayana yafison nazama likita, ina girmama bukatarsa dan haka nacika masa burinsa nazama likita, tonima sai ALLAH yacika min nawa burin nasamu damar zama soja ayanzu.
     Ranar dana iso kano saina tarar bakida lafiya, danayi bincike akan ciwonki saina gano nine maganinsa, dan haka nazo yaunayima abbah bayanin komai.
    Ya gyara zamansa to yanzudai zancen danake miki abbah yabani izinin turo iyayena su nemamin aurenki, shiyyasa nakeson jin tabakiki dan kar asoya mai amanta da albasa iman kina *SONA* kuwa???, nayi miki??, karki 6oyemin sirrin zuciyarki  kinji..
      Gsky naji kunyar zancensa dan haka na 6oye fuskata da tafin hannuna, Dr Isma'il yazare gilas ďinsa karkimin haka Saudat!!, ki daure kisanar dani kina *SONA???.*
     cikin jin kunya naďaga kaina alamar eh.
    Yasaki murmushinsa mai 'kayatarwa ya ce, "Alhmdllh, iman nagode da soyayyarki gareni, ALLAH yabarmu tare har abada, yakuma kaďe duk wata fitina dazata wanzu a tsakaninmu, ala66ana na ce, "amin ya rabbi.
     Ya kalli agogon hannunsa idan bazaki damuba zan sanar dake koni wanene dan naga munada sauran lokaci.
    Na ce, "babu damuwa.
  Lemo ya ďauka ya tsiyaya acikin kofi, yasha kaďan sanan ya ajiye, ya ďauki gilas ďinsa yasaka, gilas ďin yana matu'kar kara masa 'kyau sosai.

                 *♡☆♡*

Nidai sunan Isma'il Muh'd Basheer, mu biyu iyayenmu suka haifa, yayana Mansur saini auta, mu 'yan asalin garin sakoto ne, aikine yakawo mahaifinmu kano, mamata kuma 'yar tarabace Jalingo kenan, bafulatanace ta asali, dan harta bar duniya hausarta bata fita sosai, tuni mahaifinmu ALLAH yay masa rasuwa saka makon haďarin mota dayayi daga kano zuwa sokoto, sanan ina wata 6 a duniya, Rasuwarsa ta girgiza maman mu dan haka takamu da ciwon zucuya itama babu daďewa tabi bayansa, inada wata 10 sanan aduniya, 'kanuwar maman muce tacigaba da ri'konmu, itama tana aure anan kano dawani abokin Abbanmu.
    Sun nuna mana gata sosai wanda har muka manta da maraicin dake kanmu, dansu basu ta6a haihuwaba, sun taimaka mana munyi karatu mai zurfi, ina shekarar 'karshe a secondary ALLAH yayma uncle    rasuwa, akabar mama da ďawauniyarmu, karatunmu tarbiyyarmu, cinmu shanmu, saidai abinda 'yan uwa suka taimaka mata.
      Natashi mutum mai yawan laulayi na ciyo, ina yawan yin rashin lafiya akai2, idan ina cikin wanan halin mama takan ruďe itada yayana, hakadai rayuwa tacigaba da garawa har yayana ya kammala digiri ďinsa, bai tsaya neman aikiba ya tsunduma kasuwanci, nikuma sanan na kammala sacondary, kullum burina bai wuce nazama sojaba, amma awajen yayana da mama ba haka bane, burinsu nazama cikakken likita, dan haka burinsu ya danne nawa, nadage nazama likita domin na faranta musu, yayana yayi aure tuni, yanzu haka yanada yara biyu, Marwan da Hadeeza, (deexerh) saidai sun rabu da maman yaran, yanzu yana auren wata mata mai suna Ramla, agida ďaya muke zaune muduka, yayi mana gini kowa da 6angarensa saikuma na mama agefe, wannan shine tarihina a ta'kaice, ALLAH yasa kin gamsu.
     Murmushi nayi ina satar kallonsa, na gamsu sosai, kuma tarihinka ya 'kayatar dani, ALLAH yajikansu mama ya yafe musu, yabamu hakurin rashinsu, ameen doctor yafaďa yanamai jin daďin addu'ata.
    Ya kalli agogon hannunsa sanan ya mi'ke iman bari na wuce ko, magriba tana gabatowa.
    Na ce, "to aii bakaci komaiba sai lemo, yayi murmushinsa mai 'kyawun gani, karki damu kasancewa dake kawai ya wadatar dani, na ce, "to na gode, naďan rakoshi bakin 'kofar falon ina faďin ka gaidamin dasu deexerh da marwan, saida yajuyo ya kalleni sanan ya ce, "zasuji insha ALLAHU.
     bayan fitarsa daga gidan na lumshe idona ina murmushi da maida nannauyan numfashi, babu 'karya nima inason doctor Isma'il, domin kuwa ya cancanci asoshi, mutumne mai kwarjini a ayuka da kuma dangan taka, ga yawan fara'a, uwa uba 'kyawawan halaye, amma baza'a kirasa mutum mai tsananin 'kyauba, saidai tsaka tsaki.
     Lalai na more da samun miji nagari, kamshinsa kawai ya wadatar dani burin kasancewa dashi har abada, saidai ina ba'kin cikin katsewar karatuna, dukda nanda wata shekarar zan kammala, amma ina bukatar rabuwa da wananan azababben ciwon dakansani tagumi tunkan kamawar wata, ALLAH dai yaza6a mana abinda yafi alkairi.
   Kwala kiran sallar limance tasakani fitowa daga falon nanufi cikin gida..............


*Kuyi ha'kuri dani, wlhy ina busy*

*Luv u oll my fan's* 
*((S))......2017*
*battery low*
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *