check your best novels here

Thursday 13 April 2017

BAN SAKETA BA!!! 5&6

*________________________________*
        *BAN SAKETA BA!!!.*
*________________________________*
                     *NA*
     *BILKEESA IBARAHEEM*
             *{bilyn Abdul}*
*________________________________*
https://mrsbilkisa.blogspot.com



_Sadaukarwa_*~ya Abdul {city phone's}*


*invitation*! *invitation*!! *invitation*!!

U ar cordially invited to d wedding events of *Reefat Yahya*

*Walima* on 13th April 2017
   Venue -Barr Yahya j Bobboi's residence @ marware ward Jada,
Adamawa state.
Time: 3:30pm

*Arabian night*
On 13th April 2017
Venue Atiku Abubakar science hall Jada.
Time: 9:00pm

*Kamu day* on 14th April 2017
Venue Atiku Abubakar science hall
Time: 3:00pm

*wedding fatiha* on 15th April 2017
Venue Barr.Yahya j Bobboi's resident marware ward Jada, Adamawa state.

   Allah ya bada ikon zuwa
          _Sako daga_ *bilyn Abdul*

*_________________________________*
*WANNAN* _page ďin nakune._
    *KODA YAUSHE INA ALFAHAREE DAKU*
*Faty axlad*   *maryam 'yar mama*
  *humy luv*   *first lady*
   *hudallah*   *salma Ali wada*                                                           *Suhana*         *classic feedoh*
  *Zeenur*          *Fareedat musa*      *Esher sale*
    _Kuďin nadabanne agareni, inafata alkairi da tarin basira da kwarin ido agareku, ALLAH yakara baku ikon nishaďantar damu da faďakar damu, yakuma karemu daga sharin ma'kiya baki ďiya._
    *(Maryam 'yar mama)*
*MAHAUKACI ko BOYAYYAYEN MOSOYI!!!!!!???????.* 



_Page....._5⃣

           .......Babu 6ata lokaci aka shiga shirin bikinmu da doctor, domin iyayena basa son wata yacika al'adata tazo ba'a gidan mijinaba.
    Aranar wata juma'a aka ďaura aurena da doctor Isma'il, mutane dayawa sunsha mamakin aurar dani da'akayi, saidai basuda dama tsogumi tunda gidansu doctor Isma'il ba wasu masu 'kazamin kuďi bane saidai rufin asirin ALLAH, wannan ya hana mutane ďafewa aka kuďi abbanah yagani, saidai hakan bai hanasu yawan hasashe da hange2n daliliba, saidai sun rasa tsani ko tubalin hangowa, dan masu iya magana nacewa wani sirri sai hanji kasanshi.
   Da yamma akaje walima mai 'kayatarwa da birgewa, dayawa abokan Dr Isma'il sunyi mamakin ganina amatsayin matarsa, suna mamakin yanda akayi ya auri 'karamar yarinya haka, amma tunda basuda mai basu amsa sai sukayi gum, kamar ansakama kofar fada kwaďo.
    Waleemar ta 'kayatar sosai, karfe tara na dare aka tashi, gida aka maidani sanan akayi shirin iza 'keyata makarantar samun ladan aljanna, wato gidan miji, nasha kuka sosai na rabuwa da iyayena dakuma ďan kanina Deeni.
    An kaini gidansu doctor wanda zai zama familyna na biyu ayanzu, 6angaren mama aka kaini, dukda idanuna suna sinkife cikin hijjabi, ina a kwatan kwacin makauniyane, wanan bai hanani ďaukar sautin maganganun danginaba masu ambatar sunan wadda zata maye gurbin uwar mijinaba ayanzu, an dan'ka amanata ahannun mama, kuma ta kar6a tayi ammanar ri'keni amatsayin ďiya kamarsu doctor, to nimadai tawa zuciyar ta rungumeta amatsayin uwa tunda aure ya nisantani da gwaggota, bayan ďan faďa da nasiha aka kaini 6angarena wanda zai kasance fadata afanin sarautar gidan miji, masu kawoni basu wani ďauki dogon lokaciba suka fara kama gabansu dan komawa tasu fadojin domin kula danasu iyalin, kafin na farga gidan yayi tsit tamkar anyi ruwan sama anďauke, aunty salma kawai aka bari tana ďan gyaramin inda aka 6ata, itama zuwa wani lokaci tayimin halin ruwa, dankuwa bansan ta suďaďa ta ficeba saidai na riski shiru wai rai yayi halinsa.
    Abu biyu suka giftamin awanan lokacin, wato tausayin kai, da jimamin rabuwa da iyaye gatan 'ya'ya, agefe kuma ga wani tsoro dayake neman titsiyeni sakamakon jin shiru danayi narashinjin rai mai motsi akusadani.
    Ina nan cikin halin gajeren numfashi da dogon tunani, naji sallamar angon 'kamshi da gayyar abokansa masu masa rakiyar zuwa ďakin amaryar tasa, saidai afalo ya taka musu birki tareda mi'ka godiyar 'ko'karin dasuka nuna na fiddashi kunyar wanan rana, suduka sai suka shanya baki suna masa kallon sama da 'kasa, yayi murmushi yayinda shima yake maida musu murtanin kallon kwaji dashi, Raheem ya ce, "mutumina abin 'yar hakace ko?", doctor ya kaďa kai alamar babu shakku akan furicin abokin nasa da inda yadosa, to suma sun masa uzuri, dan dama daniyyar haka suka iso, tunda al'adarsuce haka, idan sun rako aboki basa fiya zazzarin shiga inda amarya take, daga bakin 'kofa suke tsayawa aja doguwar addu'a kowa yacika rigarsa da iska.
   To shima sun masa addu'ar da fatan alkairi harda na dawowa suna awata tara masu zuwa, 'yar dariya kawai yayi yana musu sallama dafaďin ALLAH ya huce gajiya.
    Ina zaune akan gado lullu6e cikin gyale jaa sai zabga 'kamshi nake wanda akasan amarya dashi, doctor yashigo da sallama cikin muryarsa mai shiga 6argon jiki da jini, tuni wata sabuwar nutsuwa tazo mini danjin ma'abocin 'kamshi yana kusantoni, acan kasan ma'koshi na amsa, cikin takunsa na burgewa ya 'karaso inda nake, ya ajiye ďan madaidaicin jakka mai kyawun gsk akusada gadon.
   Gadon ya hawo yana faďin amarsu ta ango mai daďin suna, ta angonta Isma'il, ya zauna akusadani tareda yaye gyalen dana lullu6a dashi, ahankali yafurta *"AMINCIN ALLAH YA TABBATA AGAREKI HASKE MAI HASKAKA ZUCIYA, IMAN MAI FASSARAR IMANIIIII!!!".*
     kasa nayi da kaina inaďan murmushi, yay 'yar dariya mai 'kayatarwa aikunya ta 'kare, tunda yau kin zama tawa ni kaďai, hannu nasa na rufe fuskata.
              Iman Ta hurema Reefat idanu, ajiyar zuciya Reefat taja mai 'karfi, suka tuntsure da dariya gaba ďaya, iman ta ce, "kai Reefat gaba ďaya kin zuba min idanu, xoxo ta ce, "kamar tana hangen daren farkonku!."
    To 'yammata aini ba haka nake nufiba, dama abinda kuke jira kuji kenan to bazan faďaba, aiko da kin cucemu dan nan muke jira muji, o, ke xoxo zan faďama momy aimiki aure kafin ki ida 'konewa wlhy, garama Reefat kaďan yarage ale'ka turaka *lol,* ta faďa tana shiga bayi domin yin alwala.
     Tayo alwala tafito, xoxo ta ce, "oh ke iman ashe kinsan hanyar.........saikuma tayi shiru dan ganin hararar da iman take watsa mata, suka tuntsure da dariya itada Reefat, yayinda iman ta kabbara sallah tana murmushi.
    Bayan sun idar da sallah suka sake zama, Reefat ta ce, "dan ALLAH iman kibamu labarin komai karki rage mana, dan nasanki da shegiyar kunya.
   Iman ta ri'ke ha6a kai Reefat ALLAH ya shiryaki, zandai faďi abinda bakina zai iya, amma ba komaiba, xoxo ta ce, "da wanan surutun mudai aci gaba".
       Iman taci gaba da faďin, cikin sanyin murya na ce, "masa ina yini fuskata na rufe da tafin hannuna.
   Ya ce, "a'a bazan amsaba saikin buďe fuskarki, dole na buďe fuskata sannan na gaisheshi, ya amsa cikin shau'ki ya ce, "ya gajiyar biki?, nai murmushi bance komaiba, yaďanja hancina miyasa kike da yawan kunya iman?, nanma shiru nayi dan gaba đaya atakure nake, kunyarsa duk ta gallebeni.
    Mik'ewa yayi yana murmushi yafice, babu daďewa yadawo da filet ahannunsa da kofuna, saman kafet _(carpet )_ ďin dake gaban gadon yazauna, yajuye gasassaun 'yan shila daketa tashin kamshi, yazuba madarar akofuna.
     *Saudatttt!!!* Yakira sunana ahankali, tareda ďanjan sunan, na ďago ina kallonsa tareda faďin na'am, ya ce, "taso kici abinci nasan kinajin yunwa.
   Na ce, "na k'oshi".
  Ya ce, "k'oshi kuma?, zadai ki k'oshi yanzu, yafaďa yana k'arasowa gareni, cak ya ďaukeni ya dire ak'asa sanan shima ya zauna, jikinsa yajawoni bari kiga ďura zan miki yanzu.
   Na ce, "dan ALLAH kayi ha'kuri zanci da kaina, haka nayita tura naman nan ina kora madara badan nasoba.
    Bayan mun gama ya ce, "yana zuwa, na ce, "masa to", yana fita nasakama k'ofar key.
   wai kunsan wani abu??.
  Sukace a'a saikin faďa.
Nifa duk wanan abun dayake faruwa babu tsoronnan da ake faďa na amarya ga angonta araina, danni wlhy bansan idan anyi aure mi'akeyiba, rufe ďaki danayi, nayi hakane dan inajin kunyarsa, amma badan ina tsoron faruwar wani abuba.
   Su xoxo sukasa mata dariya, lallai 'yammata kin haďu.
   Iman tayi 'yar dariya, ina gaya muku nacire kayana nasa na barci, na ďane gado na kwanta.
                      Cikin barci naji ana shafani, abinda baka sababa dan haka natashi afirgice tareda wage baki zanyi ihu.
   Doctor yasa lallausan hannunsa ya rufe mini baki yana faďin iman nine fa,  cikin rawar jiki na ce, "dan ALLAH ka dainamin wanan abun, wlhy gwaggo ta ce, "mini iskancine, kullum tanamin gargaďi, kokanaso na zubar da mutuncina??.
   Doctor ya kunna fitilar dake gefen gadon, yakamo hannuna ya zaunar ya ce, "tokiyi ha'kuri nadaina yimiki zoki kwanta, na ce, "saidai na koma 'kasa, ya ce, "a'a yi kwanciyarki, nibari na kwanta saman kujera.
   Haka yakoma saman kujerar dake a ďakin ya kwanta, nima na koma nakeanta atsorace, cikin ikon ALLAH babu daďeqa barci yay gaba dani dan akwai gajiyar biki a tattare dani.
    Shikam doctor yakasa barci, yana mamakin dama azamaninnan da aka lalace akwai yaran dabasu san minene aureba, lalai shikam yayi babbar sa'a, idan yatuna abokansa dayawa, waďanda bayan aurensu suke masa tambaya akan suffofin mace mai cikakken burci, saboda kokwanto dasuka shiga akan nasu matan, yagodema ALLAH dabai kasance mazinaciba, bare ALLAH ya jarabceshi da auren mazinaciya, haka yayta tunane tunane har barci ya saceshi.
      Kiran sallar farko ya farka, yatashi yaje bayi yay alwala, yayi raka'atainul fijir, saida aka kira sallar farko sanan yatasheni yafice masallaci.
     Saida gari yaya sha sanan doctor yadawo, zuwa lokacin harna sake 6ingirewa akan sallayar dan barcin bai isheniba, yabini da kallo yana murmushi, akan la66ansa yafurta 'yarrigima kenan, ďaukata yay caj yadire agadon sanan shima ya hawo, ahankali yanutsani da jikinsa gudun karna tashi nayi masa mazurai, nikam nariga nayi nisa abarci bansan bikin dayakeyiba ma...............


                           *♡☆♡*

_Page....._6⃣

        Karfe 8:00am nafarka sainajini ajikin doctor, da sauri nazare jikina daga nasa amma bai farkaba, dan haka na nufi bayi danyin wanka, harna fito na shirya cikin riga da siket na atanfa bai farkaba, ganin haka yasa na nufi falon dan inga tsarin gidan, na tsaya cak atsakiyyar falon inabin ko ina da kallo babu 'karya komai yayi atalauce ba'a sarauceba, iyayena sun taka rawar gani saidai fatan ALLAH yabiyasu da mafificin alkairinsa, an k'awata falon da wasu manya2n hotinanmu nida doctor, wanda nibammasan lokacin danayisuba, wata zuciya tacemin tsarin computar ne kawai, jinai anbuďa k'ofa, da sauri na juyo azatona shine yatashi.
   Amma sainaga wata matace 'kyakykaywa, tanada ďan jiki babu laifi, na ce sannu, fuskarta babu walwala sosai ta amsa min da yauwa, na rissina ina gaisheta, batareda ta amsaba ta ce, "min ina isma'il ďin??, na ce, "yana barci.
    Barci kuma?, ta maimaita ayatsine, na ce, "eh".
   Ta kalli agogon dake manne afalon, ta ce, "karfe takwas da rabi mutum bai tashiba, yana inane??, da hannu na nuna mata ďakina, kai tsaye ďakin ta nufa, niko nayi sakake ina binta da kallon mamaki, saiwata zuciyata ce, "kibita kiga abinda zatayi.
    Aiiko nabita amma natsaya akofa, tana shiga ďakin tanufi bakin gadon, doctor yanata barcinsa hankali kwance, tasa hannu ta yaye bargon daya lullu6a dashi, ALLAH yasama dogon wandone ajikinsa da doguwar rigar dayaje masallaci.
    Tasa hannu taja yatsansa na kafa, yabuďe ido ahankali yana faďin iman yadai??, ta ce, "aii ba itabace, da sauri ya mik'e zaune danjin muryar auntynsa, cikin mamaki ya ce, "aunty kece?".
     Ta ce, "eh nice, saboda kayi sabon aure zakabar tsohuwar zuma.
    "Kamar yaya aunty?".
 Tokaga amarya ka manta da uwar gida mana.
   Azuciyata na ce, "uwar gida kuma?.
    Maganar doctor ta katseni a'a ni rabani dawata uwargida kije can kiji da tsohon mijinki, nima naji da amaryata.
   Naga alama maganar ta sosa mata rai amma saita dake, fuskarta ta 6oye fushinta, ta ce, "oh masu amarya, santin amarcin haryasa kafara mantawa damu?, to ka mi'ke".
   Breakfast yakammala kaida amaryarka kawai ake jira.
         Yaďan ja hancinsa to muna zuwa, yafaďa atakaice.
    Maimakon ta tafi saita zauna abakin gadon, tana faďin a'a bari najiraku anan salon ku kara shanyamu.
   Yarage fara'arsa, kinga aunty kije zanyi wankane, idan mungama zamuzo, duka yanzu karfe nawa?, kuma nasan yau yaya ba Zaije kasuwaba ya faďa tareda kallon agogon dake manne aďaki".
     Ganin fuskarsa ta nuna alamun 6acinrai yasata mik'ewa ta fito, ina kallo yarakata da harara sanan yay magana wadda nikaina banjitaba.
   Nashige cikin labulale dankar taganni, tafito tanabin falon da kallo tana ta6e baki, idanunta suka sauka akan hotunanmu ta kalla sainaga taja tsaki ta fice.
   Nabita da kallo ina tambayar zuciyata wanan kuma wacece??".
    Ina nan tsaye yafito, yabini da kallo a'a iman tunanin mikikeyi haka?, nayi 'kasa dakai ina murmushi na ce, "babu komai, narissina ina gaishesa.
    Ya ce, "bazan amsaba, tunda kika tashi kikaki tashina.
   Na ce, "to kayi ha'kuri bazan sakeba.
     Ahankali yak'araso tareda rungumeni, cikin kunnena ya ce, "to kin tashi lafiya??, na ce, "lafiya 'kalau, hannuna yakama zomuje ďakina nayi wanka, muje muyi breakfast kinga su yaya suna jiranmu, na ce, "kaje kayi wankan, nikuma bari nagyara ďakin kafin kafito.
   Yayi murmushi kedai bari kimin wayo kawai", a'a bahaka bane nafaďa ina murmushi dake kara bayyana kyawun fuskata, to shikenan jeki gyara bari nayi wankan.
    Dakina nanufa inata 'kokarin gyarawa, saboda sabo da gyara gadon gwaggo yasani gamawa da wuri, har falo nafito nakara gyarawa.
     Babu daďewa saiga doctor yafito cikin kananun kaya, yayi kyau sosai, sai tashin kamshin turarensa yake, ya ce, "taso muje nasan suna jiranmu, na ce, "to, naďakko gyale zansaka, ya ce, "anan gidannefa, kike niyyar saka mayafi, nađan kalleshi ina faďin kayi hakuri ALLAH inajin kunyar zuwa haka, yay murmishi to sarkin kunya mije.
    Munfito daga 6angarenmu muka nufi wani 6angare dayake iri đaya danamu, kuma zasu iya zuwa girma ďaya, saikuma wani acan gefe wanda bai kai girman namuba,  tabaya yabi damu zuwa wata 'kofa wadda nake da tabbacin tanan zamu riski falon mai gidan, wato yayansa, k'ofar doctor ya kwankwasa, babu daďewa akazo aka buďe, matar dataje 6angarenmuce ďazu tabuďe, taja baya muka shiga sanan ta maida 'kofar tarufe.
    Falon ya haďu iya gwargwadon hali, sai tashin k'amshi yake, wajen wani k'ak'yk'yawan mutum muka k'arasa zan iya cemuku yafi doctor k'iba da haske sosai, suna tsananin kama, daka gansa kasan yayansane, saidai doctor ya nuna masa k'uruciya kawai, yana ganinmu yafara fara'a yana faďin oyoyo k'anwata sannunnku.
    Nikam cikin jin kunya na'kara nesa dashi kaďan, nazauna saman kafet ina gaisheshi cikin ladabi.
   Da sauri ya ce, "tashi kihau kujera kinji.
    Nak'ara k'asa da kai ina faďin nanma ya isa yaya".
   Shikam doctor kusada yayansa ya zauna, yawani narke ajikinsa kamar k'aramin yaro, yaya yarungumo doctor jikinsa yana faďin auta kuntashi lafiya kaida k'anwata??.
    Lafiya lauw muka tashi yayana".
    Alhmdllh yaya yafaďa".
    Yaďora da faďin k'anwata yagajiyar biki??.
    K'asa nayi dakaina saboda inajin nauyinsa sosai.
   Doctor ya ce, "ka gantanan yaya tacika kunya dayawa wlhy.
   Tokai idan banda abinka auta aii anason kunya, domin kunya tana ďaya daga cikin alamun tarbiyya.
     Hakane kuma yayana, doctor yafaďa yana masa jinjina........ 
      Aunty ta katse doctor da faďin to kutaso breakfast yana jiranku, muduka muka kalleta sanan muka mik'e.
    Doctor ya ce, "wai ina yaranane??, yayansa ya amsa masa da faďin suna 6angaren mama, kasan suna ganin ba'ki bazasu tuna damuba, sai bak'in sun tafi sanan.
     Doctor yaya dariya, yarana kenan sunaso sudai suga ba'ki.
     Munzauna cin abinci nidai duk akunyace nakecin abincin, dan ban saba dasuba.
   "Yaya ya ce, "k'anwata miyasa bak'ya son cin abinci?, ko baki son wannan acanja miki wanine?".
    "Da sauri na ce, "a'a".
  Yayi murmushi to kisaki jiki kici abincin nan gurin duk family ďinki ne, kuma gidankine.
   Na ce, "to.
Doctor ya ce, "konazo nabaki da kaina??:"
   Da sauri na girgiza kaina.
  Ina kallon matar yayansa ta ta6e baki, dama tunda muka fara magana bata tankaba, abincinta kawai take dannawa.
     Hakadai muka gama.
Yaya ya ce, "yakamata kuje 6angarenku, dan ba'ki zasu ringa shiga yimuku sallama, wasu yau zasu wuce.
    Okey doctor tafaďa yana mik'ewa.
    "6angarenmu muka koma.
  Muna shiga doctor yakwanta saman doguwar kujera wai yagaji, ya kalleni ko kema kinajin barcinne??.
   Kai na girgiza masa batare danayi maganaba.
   Yayi murmushi shikenan matana gwanar kunya.
    Muka ďanyi shiru zuwa wani lokaci, dan ni inajin nauyinsa, yajuyo idanunsa matsakaita yana 'karemin kallo, tafin hannu nasa na kare fuska, ya tuntsure da dariya, my iman rowar fuskarki kikemin??.
    Na kaďa kai alamar a'a".
  Yatashi zaune yana faďin babu waninan, bagashi dan ina kallonkiba kin rufe fuska, ban bashi amsaba saima na k'ara cusa kaina cikin cinyoyina, yataso tsam daga inda yake, ban ankaraba sainaji ya ďaukeni cak, yamaye gurbin inda nake zaune, nikuma ya ďorani saman cinyarsa.
   Da sauri na buďe idanu, kallo ďaya na masa nayi k'ok'arin kauda kaina, amma yarik'e fuskata yahanata juyawa.
    Ahankali yafurta wanan kunyar taki tayi yawa iman, yakamata naďan rageta, yana gama faďa yak'ara matseni ajikinsa.
   Kafin nayi wani yunk'urin kwacewa ya haďe bakina da nasa, hummm, ba tsoroba har ruďani nashiga, jikina sai karkarwa yakeyi, gashi yahanani wata damar dazanyi motsi bare nayi yunk'urin kwatar kaina.
    Yanda yaso yake sarrafa bakina da harshena, tamkar yasamu alawar _lollipop._
    Sai ambatar sunayen ALLAH nake a zuciyata, dan banta6a tunanin faruwar hakaba tsakanina dashiba.
   Munkai tsawon minti shabiyar ahaka doctor yana abu ďaya yayinda tuni fuskata ta gama jik"ewa da hawaye, har shima tasa fuskar tasamu tsaraba.
    Ya zare bakinsa dak'yar yana maida numfashi asark'e, nikuma nayi saurin direwa daga jikinsa dan bashida karfin dazai iya rik'eni awanan lokacin, saboda laushi da nauyi da kasalar da suka kanainayesa.
   A ďari na afka ďakina na kulle, na haye gado can k'arshe kamar wadda tayi gamo da dodon mayu, sai maida numfashi nake da sauri da sauri..  
    Shikam ďan murmushi yayi saboda ganin gudun danakeyi, ya maida kansa ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa yana cigaba da murmushi tareda 'kara lashe la66ansa  *(yayi k'yau likita bokan turai) lol.................*


*Kucigaba damin uzureeeee!!!!*
  *Plzzzzzz!!!!!!!*

*Luv u oll my fan's* 
*((S))........2017*
*battery low*
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *