check your best novels here

Thursday 27 April 2017

BAN SAKETA BA!. 13/14

*_______________________________*
       *BAN SAKETA BA!!!*
*________________________________*
                        *NA*
       *BILKEESA IBRAHEEM*
               _*{bilyn Abdul}*_
*________________________________*






_sadaukarwa_ *~ya Abdul {city phone's}*




*MIYAKAMATA NAYI!??.*
             _ZAKA IYA MUTUWA YANZU_
     _SHIN BA ZAKA JI KUNYAR ALLAH BA??, YA KAI 'DAN ADAM!!, Shin ba zaka ji kunyar ALLAH ba?? Kullum SHI yake baka ci da sha da numfashin da kake shk'a, Amma godiyarka ta tafi zuwa ga waninsa, Sa6onka kuma ya tafi zuwa ga ALLAH mahaliccinka._
       _Kana nuna ma mutane kamar cewa kai mutumin kirki ne, alhali akwai Miyagun ayyukanka da kakeyi a 6oye, da kuma Miyagun tunanin dake Qunshe a zuciyarka._
    _*Ubangiji* Ya san dasu amma bai ta6a tona maka asiri ba, Kullum rufa maka asirinka yakeyi, amma kai kuma kana Qara butulce masa._ 
      _Kullum Qara turo maka_
_Ni'imominsa yakeyi, amma_ _Maimakon ka gode Mai sai kake_ _ganin kamar hikimarka ce ko kuma wayonka ne suke baka,_ _Yanzu idan kana dauke da Olsa_ _*(Ulcer)* ko Hawan jini ko_ _*Diabetes* (Ciwon Sugar) duk_ _abincin da likita ya hanaka ci,_ _Sai kayi shekaru baka cishi ba,_
_saboda mi??,  Saboda kana_ _tsoron_ *MUTUWA!!!.*
       _Amma Ubangijinka wanda Ya hakicceka Yace maka_

_*- QARYA BABU KYAU.*_
_*- GULMA BABU KYAU.*_
_*- SATA BABU KYAU.*_
_*- SHIRKA BABU KYAU.*_
_*- GIRMAN KAI BABU KAYU.*_
_*- ZINA BABU KYAU.*_
_*- TUNANIN AIKATA FASADI*_ _*KOWANNE IRI MA BABU*_
_*KYAU..*_
       ```Yace maka duk wad'annan HARAMUN NE, Kuma zasu kai ka Zuwa ga shiga Wuta, Amma duk da
haka gashi nan kana yinsu babu dare babu rana...```
        *SHIN GASKATASHI NE BAKAYI BA?? KO KUWA LIKITAN ASIBITI YAFI* *UBANGIJINKA* *FA'DAR GASKIYA NE???*
       _Ya Allah mun tuba Ka yafe mana... Idan mu halinmu ne muyi sa6o saboda raunin zukatanmu,  To Kai kuma halinka ne yin Gafara da Rahama da Afuwa ga bayinka ba tare da hisabi ba, Ya Allah Ka_
_Tsaftace zukatanmu daga_ _dukkan abinda baka so._
     _Ka sanyamu cikin bayinka Masu shiryuwa da kuma_
_shiryarwa zuwa gareka, Ba_ _Batattu ba, kuma ba masu_ _batarwa ba_
   *ALLAH yasa mu gane*





*~page.......13~*
     
          ..................iman tacigaba da faďin, koda yazame tawul ďin sainayi saurin buďe idanuna, ganina zir yasa na ranta cikin na kare zan shige bayi, taku ďaya ya damk'oni.
   Tuni jikina yafara 6ari dan haka nasa masa kuka, sakina yayi yana faďin sorry my iman jekiyi wankanki.......aii kafin yagama faďa nakai cikin bayin.
    Ya zauna bakin gado yana fidda huci, idanunsa sunyi jajur, yasan iman tabbas yarinyace, amma zata iya ďaukar nauyinsa, saidai yakula yarinyar tanada tsoro sosai, baisan yanda za'ayi ta fahimcesaba, gashi bayason binta da k'arfi, yafison komai ya wakana cikin ilimi da fahimtar juna.
   Wato da yardarta kenan.

Tuni nagama wanka amma nakasa fitowa saboda kunya, ina bayi da tunanin yanda za'ayi na fito sainaji maganar deexerh tana kwala kiran uncle!.
    Ya ce, "baby shigo ganinan, daďan k'arfi yafaďa yanda zataji.
    Tashigo da sallama, yatashi zaune yana faďin harkun dawo?, ta zauna kusadashi tana dariya eh uncle, ashe kadawo daga kasuwar?.
   Nadawo tuni, kinsan banason hayaniya.
   Tayi dariya akaro nabiyu, wlhy rayuwarka tana burgeni uncle, shiyyasa kullum nake burin nayi koyi dakai, amma bakina baya iya shiru bansan miya saba.
    ďan murmushi yayi yana kallonta, to kizo nakoya miki.
   Ta ce, "da gsk uncle."
  Kai ya jinjina mata yana lumshe idanunsa.......kafin tabashi amsa Raihan tashigo ďakin.
     Suduka suka amsa, saidai gogan kamar baiyi maraba da zuwan nataba, gefensa itama ta zauna suka sakashi tsakkiya itada deexerh, sai kawai ya haye gadon sosai ya kwantan.
     Raihan tabishi da kallo dan tasan saboda ita yayi haka, suka haďa ido ya kauda kai, itakuma taja ajiyar zuciya, deexerh ta ta6e baki tana mik'ewa, uncle wai ina my aunty??.
     Muryarsa aďan ďarare ya ce, "tana bayi wanka take.
     Mik'ewa tayi tanufo k'ofar bayin tana kwankwasawa, da kiran aunty!!.
    Nayi gyaran murya dan babu damar magana abayi.
    Ta ce, "wai wanka kikeyi??.
   Kaďan na buďe k'ofar nalek'o tunda ta juyawa gadon baya, dan haka bazanga su doctor ba suma bazasu ganniba.
    Na ce, "dee.... kun dawo?.
Kai taďaga mini alamar eh, tabini da kallo wai bazaki fitobane??, zan fito mana amma ďan ďakkomin zani da hijjabi a duriwa.
     Dariya tayi kai aunty kincika kunya, na ce, "babu komai nidai bani kawai.
    Babu daďewa takawo min zani da hijjab, lokacin doctor da Raihan sun fice, abin ya6atama deexerh rai sosai, dan haka tana bani zanin tarufa musu baya.
     Nikam dabansan wainar da ake toyawaba nafito nahau shirina.
    Adurkushe deexerh ta tarar da Raihan gaban doctor; da alama rok'onsa takeyi kokuma wani abun daban, shikuma yaďan kauda kai gefe fuskarsa babu yabo babu fallasa.
    Tana ganin deexeh tamik'e, tasamu kujera ta zauna, ďan siririn tsaki deexerh tayi itama tanemi guri ta zauna.
    Koda nagama shiri saina nemi gado na haye, babu daďewa barci yay gaba dani, ni azatonama sunbar gidan.
    
  Sai gab da magriba na farka, nabuďe ido ahankali saina ga doctor tsaye yana shirin masallaci.
   Yak'araso kusada gadon yana faďin my saudat kin tashi?, na ďaga masa kai ina yunk'urin tashi zaune, da sauri yatadani ya zaunar, ya ce, "kinsha barci ko?.
    Kai naďaga masa ina lumshe matsakaitan idanuna.
   Ya summbaci kumatuna yana faďin bari naje masallaci naji suna shirin tada sallah.
    Ban takashiba dan miskilancin yana kusa.

_*bayan kwana uku*_
         Bayan kwana uku nadawo normal, nayi wankan tsarki, dukda ban sanar da doctor ba yasani dan yana rik'e da adadin kwanakin danakeyi.
    Muna zaune nida deexrrh da Raihan muna kallo, dan takan shigo tareda deexerh, saidai bansan dalilintaba tunda har yanzu bansan abinda ke tsakaninta da doctor ba, kuma nakasa tambayar deexerh.
       Munacikin kallon saina farajin barci, dan haka nazame saman doguwar kujera na kwanta, nabarsu suna kallonsu.
    Doctor bayanan yafita tun ďazun.
   Cikin barcina nakejin k'amshin turaren doctor, nasake ware hancina dan ina matuk'ar son turaren, zan iya cemuku awajensa kawai nata6ajin turaren nan, nabuďe idanuna ahankali saboda kusantowar turaren sosai kusada hancina.
    Ware idanu nayi saboda ganin fuskar doctor kusada tawa, harma munajin saukar numfashin juna, naďan kauda kaina gefe saboda kunyarsu deexerh.
    Cikin jin kunya na ce, "doctor yaushe jadawo??.
    Hannunsa yasa yadawo da fuskata inda take da, idanuna naruntse dan bazan iya kallon kwayar idanunsaba.
    Bakina yasumbata ahankali yafurta my iman inason kunyarnan taki wlhy.
      Bance komaiba sai mik'ewa danayi dan nagashi bayajin kunyarsu deexerh dake folon.
     Karaf na haďa ido da Raihan tana kallonmu, ta haďe fuska tamkar zata haďiyi zuciya tamutu, tai k'asa da kai saiga hawaye sharrrr akan kumatunta, da sauri tashare dankar agane, saidai ta makaro dan duk mungani, deexerh ta ta6e baki.
    Amma fuskar doctor ta nuna alamun gizago.
       Deexerh ta ce, "sannu da zuwa uncle.
   Yauwa babyna ya gidan??.
Ta ce, "Alhmdllh.
    Ganin haka itama Raihan ta ce, "sannu dazuwa yaa Isma'il. 
  Itama ya amsata damar yanda ya amsawa deexerh.
       Dukda bansan matsalartaba tabani tausayi.
     Najuyo ina kallon doctor danufin tambayarsa mizan kawo masa, saiya saki murmushin basarwa kawai.
      Na ce, "mikakeso akawo maka?.
    Yaďan sosa sumar kansa yana satar kallon deexerh da Raihan, sai kawai yamik'e yakama hannuna muka nufi ďakinsa.
      Hummm wai kunsan miya faru?.
   Sukace a'a".
        Damuka shiga saiya hau tambayata wai miye matsalar Raihan??, yabani matuk'ar dariya, saboda kular danayi yana matuk'ar yimini kallon k'aramar yarinya.
   Sai kawai nayi amfani da damata na ce, "saboda kai take kuka mana.
     Aďan razane ya ce, "kamarya sabodani?.
    Nayi murmushi ina kallonsa, na ce, "nima amsar wanan tambayar nakenema, ina gama faďa nayo waje.
    Bina yayi da kallon mamaki, yakasa koda yunk'urin ďaga yatsa bare ya iya kiran sunana, nikam wallahy maganar tazominne kawai amma bada niyya nafaďaba.
     Abubuwan motsa baki nahaďo masa, har nadawo bai matsa daga inda nabarsaba, na ajiye tiren hannuna ina murmushi, naje nakamo hannunsa na zaunar abakin gado, nazuba ruwa akofi na đora masa abaki.
     Yako buďe baki yashanye dan yana buk'atar buk'atar abinda zai jik'a masa mak'oshi yasamu damar haďiyar yalwataccen yawu.
    Yanasha idonsa akaina, nima kaina mamakin kaina nake da irin wanan abubuwa, kwata2 babu kunya ataredani, ya shanye tas, sanan najanye kofin.
     Kusada shi na zauna ina faďin lfy kuwa doctor?.
     Wata wawuyar ajiyar zuciya yaja, yay saurin basarwa dan fuskarsa tana da k'ok'arin 6oye sirri, ya ce, "mamaki maganarki tabani kawai.
     Wata 'yar dariya nayi na ce, "lah nifa tsokanarka nake, bammasan maganartawa tayi kama da abin mamakiba aii.
    Nafaďane kawai dannaji tabakinka.
    Ya rausayar da kai gefe yana bina dawani shu'umin kallo, tabbas yasan nacanja salone, amma na burgeshi, dan hakan ya nuna masa bayyanar wayona, shima saiya basar kawai yay dariya.
    Amma iman kin iya kulli wlhy, harkinsa hankalina tashi, dan banason abinda zai 6ata mini ranki ko kaďan.
    Na ce, "ko?"
 Yajinjina mini kai alamar eh".
      Yayi k'yau nafaďa ina k'ok'arin mik'ewa, da sauri yajowoni saman cinyarsa, yamatseni akan faffaďan k'irjinsa daketa tashin k'amshi.
    Cikin kunnena ya ce, "kishi ko iman??, nasaki sassanyar dariya wadda yakejinta harcikin kwakwalwarsa, na ce, "a'a wlhy, tsam ya rungymeni a k'irjinsa yana fidda numfashi a sark'e.
    Yanda yake fidda numfashin sai tsoro yakamani, na ďago daniyyar tambayarsa lafiya saiya haďe bakinsa da nawa, naga takaina nafaďa azuciyata dan nasan saina sha murza bata wasaba.
    Aiko nashata dan yau har inda hannunsa baya kaiwa saida yakai, tuni tsoro da rawar jiki sun shigeni, nafara tsunguninsa da k'ok'arain zame jikina amma nakasa.
     Saida yayi mai isarsa sannan ya sakeni yana murmushi da fidda hakki, idanunsa sunyi matuk'ar ja.
    Da sauri na nufi k'ofa zan fice, ahankali ya ce, "plz karki fita su Raihan suna falon, zasu ganki awani iri.
     Cak natsaya amma ban juyoba saidai nabi jikina da kallo, gsky yafaďa dankuwa duk ya yamitsemin jikina da kayana, maimakon nadawo saina jingina kaina da k'ofa.
    Azatonsa kuka nake dan haka cikin nauyin jiki yataso gareni, tabaya yarungumeni yana magana ahnkali, sorry iman kibar kuka, badan na6ata miki raiba nakemiki hakan, saidai tsananin k'aunarki danakeyi, amma indai bak'yason hakan danakemiki nayi miki alk'awarin zan daina har saikin buk'ata da kanki.
    Da sauri najuyo dan muryarsa kamar yana kuka, ganin idona k'amas babu akamar kuka yasashi zaro idani waje.
   Sai kuma ya rungumeni, ya ce, "tsokana ko iman?, babu komai zan ramane.
    Nayi shiru dan nakasa bashi amsa...
   Bayan kamar minti talatin mun daidaita sai muka fito falon, amma wayam babu deexerh babu Raihan.
     Sainaga kamar doctor yaji daďin hakan.
   Amma ni sainace doctor bari nakira su Raihan su dawo ko?, kaga ka koresu.
    Da sauri ya ce, "A'a barsu kawai, aii hakan dasukayi shine daidai.
    Shuri nayi ina kallonsa dan ni aganina babu k'yau.
    Kallo ďaya yamin ya kauda kai, dan yakula zancen bai shigeniba.
   Babu yanda zanyi dole nazauna na barsu.

       Har zuwa dare yahanani zuwa ko ina, hakan ba k'aramin haushi yabaniba, nayima deexerh test akan sudawo.
    Amma saita turomin...
_*hhhhhhh haba auntyna, babu wani dawowa dazamuyi, munbama uncle filine ya huta, dan haka saida safe, asamo mana baby mudai dan ALLAH*_
      Na ce, "ALLAH yashiryaki deexerh, zamu gauraya da safe aii.
     Har isha'i ban je ko inaba, saida yatafi masallaci sanan naje nayoma mama saida safe, natarar deexerh da raihan suna 6angaren aunty, dan haka najuyo danba zuwa wajen nakeba da daddare saidai idan takama dole.
              Ana idar da isha'i doctor yadawo, hannunsa ďauke da leda, bayan nayimasa sannu yabani umarnin juye abinda ke ledar.
    Nasamo filet najuye gasassun 'yan shila lafiyayu da madara mai sanyi.
    Gabansa natura duka yabini da kallo yana faďin kefa??, naďan marairaice murya na ce, "nak'oshi".
     Dariya yayi ya ce, "ko?".
Na ďaga kai".
     K'asa yasauka yana cigaba da dariyarsa wadda bansan inda ta dosaba dan bansan *Sirrin zuciyarsa ba* sabon littafina mai zuwa insha ALLAHU, *(SIRRIN ZUCIYA)*.
      Baikuma cemin komaiba yajawoni jikinsa, yafara danna mini naman abaki, dole nakar6a inaci, yana koramin da madara mai sanyi.
    Bayan munci munsha yasa tishu yagoge min baki, daganan yamik'e zuwa ďakinsa, nima na gyara wajen nayi nawa ďakin.
      Na kalli agogo ko goma batayiba amma naga yau doctor kwanciyar wuri yake shirinyi.
    Nidama banida matsala da wuri nake barci.
   Nayi shirin barci tsaf na gyara kaina, nahau gado zan kwanta zuciyata fes babu wata damuwa.
    Doctor yaturo k'ofar da sallama yashigo, na amsa ina kallonsa dan ganinsa da jallabiya sa6anin kayan barci.
      Saida ya shimfiďa sallaya sanan ya ce, "taso kiyi alwala.
    Kaina tsaye na ce, "nafayi sallar isha'i.
   Eh nasani aii, zamuyi nafilane.
  Na ce, "yanzu nayi alwalar kwanciya ma.
   "Okey to taso".
  Tashi nayi na ďora zani akan kayan barcina, nasaka hijjabin sallata, shi yajamana sallah raka'a biyu, bayan munyi sallama ya dafa kaina tareda karanta addu'a kamar yanda addininmu ya koyar damu, daganan kuma yacigaba da kwararo mana addu'oi na musamman, tun yanayi har muryarsa tafara zuga alamar zuwan kuka, dan yanama iyayensa addu'ane, tonimadai tayasa nafarayi dan yabani tausayi.
    Yashafa nima nashafa sanan yajuyo yana kallona fuskarsa ďauke da murmushi.
    Nayi k'asa dakai dan kallonnasa yana bani kunya.
   Tambayoyi yaymin afannonin addinina.
   Alhmdllh nabashi amsa yanda yatambaya saboda ina zuwa islamiyya.
   Nakula ba k'aramin daďi yajiba.  

Reefat ta ce, "oh ke iman ashe kinsan turaka..........iman tabuge mata baki kafin ta k'arasa suka tuntsure da dariya.
    Miss xoxo ta ce, "ai gskyar Reefat wlhy, ashemu nan duk kallon kitse kike mana.
    Tashi tayi tana dariya da faďin kudai kuka sani........ 
                       
                 









*MIYAKAMATA NAYI??.*
         _da mutuwa tana duban girma dabata ďauki tsofaffiba._
     _da mutuwa tana duban milki dabata ďauki masu mulkiba._
      _da mutuwa tana duban tsantseni dabata ďauki malamaiba._
   _da mutuwa tana duban tausayi, dabata ďauki talaka da yaraba._
    _da mutuwa tana duban jarumta, dabata ďauki matasa ba._
    _da mutuwa tana duban addini, dabata ďauki musulmaiba._
     _da mutuwa tana duban jin daďi, dabata ďauki turawaba._
       _da mutuwa tana duban imani, dabata ďauki kafiraiba._
   _da mutuwa tana duban kunya, da bata ďauki 'ya'ya, agaba iyayensuba, maza agaban matansuba, mata agaban mazansuba, iyaye agaban 'ya'yansuba._
   _da!. da!!. da!!!!..........dayawa, sabodasu da mutuwa tabar kowa aduniyarsa._
   _amma kash, itama tana cika umarnin *ubangijinta ne*, tunda mala'ikan mutuwa ya iya ďaukar ruhin mafificin halitta,_ _ma'abocin_ milki, imani, tausayi, talaka, _masoyi, mafifici, domin_ _addinima shine mai koyar da_ _muminai, dukiya,_ _(domin annbinmu baya cin sadaka,_ _kunga kuwa wadataccene,_ _danba tarin dukiya bace_ _wadata, a'a wadatar zuci,_ _dukmai wadatar zuci yawuce akirasa talaka), amma wanan bai hana yakusanci ubangijiba._
   ```To yakamata, nida kai da ke da su da ku damu gaba ďaya, muringa tunawa akwai mutuwa maizuwa maka akowane irin hali, akowane kuma irin lokaci.```
   ~Idan ko hakane yakamata kasancewarka musulmi mai imani, yaringa tunawa da zuwan mutuwa aduk halin daya tsinci kansa, walau alkairi ko sharri, inaganin idan muna tunawa da mutuwa zamu ringa rage aikata aikin sa6o.~
   _Ka gwada na gwada ki gwada mu gwada mugani kozamu dace._
   *ALLAH yasa mugane* 






~*page........14*~

            .................bayan mun kammala na haďa sallaya ďin na linke da hijjabina, doctor kuma yazauna bakin gado yana kallona da mamaki, dan ganin hankalina kwance babu wata fargaba.
   Na kammala linkewa na hawo gadon na kwanta acan nesa dashi kamar yanda na saba.
    Shima saiya gyara filo ya kwanta a k'arshen gadon.
   Shiru zuwa wani lokaci, ni ina addu'ar barci, shi yana tunanin ta ina zai fara, nagama shafa addu'ata tareda gyara kwanciya ina faďin saida safe doctor, mai makon ya amsa mini kamar yanda yasaba saiya jehomini tambaya.
    Iman! na tambayeki wani abu?.
   Naďan waigo da fuskata na ce, "eh tambayeni".
    Yaďanja numfashi yana matsowa tsakkiyar gadon, ya ce, "miyasa ni baki shafa min addu'arki??.
   Nayi shiru ian tunanin amsar dazan bashi.
  Ya ce, "kinyi barci?."
   A'a nafaďa".
 Okey ina saurarenki!.
      Na ce, "babu komai, amma aii ina tofawa ko ina na kusurwar ďakinnan, hakane yafaďa a sark'e.
    Tokuma miyasa bakison kwanciya kusada ni?.
   A wanan karon saida na kalleshi muka haďa ido kasancewar akwai wadatar hasken fitila, na ďan kauda idona daga kansa, na ce, "saboda kai namijine, nikuma mace.
   Murmushi yayi, saboda yaga amfara zuwa wajen, ya gyara kwanciya yana faďin amma aini mijinkine ko?.
   Na ce, "eh."
   Ya ce, "masha ALLAHU."
       To zoki shafa min addu'ar.
 Dukda ina jin kunyarsa hakan bai hanani amsawaba, saboda yauda kullum, sabo da soyayyarsa sun k'ara tasiri acikin zuciyata fiye da tunanin mai karatu.
    Koda nazo daf dashi sainace to kashe fitilar.
   'Yar dariya yayi, saboda mi?, sai ankashe fitila?.
    Na ce, "inajin kunya.
  To sarkin kunya nakshe azo amin, yafaďa yana kashe fitilar gefen gadon.
   Na matso kusada shi sosai, dukda yakashe fitilar sai nake gani tamkar yana kallona, dan haka na rintse idanuna sannan nakai hannuna ajikinsa ina shafa masa addu'ar.
   Wadda shikuma yakejinta tamkar tafiyar tsutsa nake masa, ban ankaraba sainajini kwance a faffaďan k'irjinsa..........dan ALLAH basaina faďaba abarshi haka, iman tafaďa tana kallon fuskar Reefat da miss xoxo.
   Tab!!, suka faďa atare, wlhy babu ďaga k'afa sai an faďa mana komai.
    Iman tashiga lalla6arsu amma sukace basu yardaba saita faďa, basa son kwange.
   Babu yanda zatayi dole taci gaba, tunda alk'awari ta ďauka musu.
   ........'yar rungumenin daya sabayi yasa banji komai arainaba, bankuma kawo komaiba, saima k'ara nutsa kaina danake cikin k'irjinsa ina shak'ar daddaďan k'amshinsa, turarurrukan doctor sun kama jikinsa sosai wanan yasa duk motsin dayayi sai k'amshinsa ya baza waje.
   Nashagala da shak'ar k'amshin sai naji hannunsa wata tashar daban, naďago da zummar kwace kaina amma ina saiya k'ara matseni gam, cikin muryar mai fara shirin kuka na ce, "doctor pls kasakeni, muryarsa naji cikin kunnina yana faďin nutsu my saudat, zan ďansha k'amshinkine.
   Yanda yake maganar hannunsa kuma nacigaba da shafa inda tunanina baita6a kaiwa doctor zai ta6aminba, sai jikina yakama rawa, na fara kuka, bakina ya laluba ya haďe danasa.
   Tuni labari ya sauya salon tafiya, doctor yanata k'ok'arin kaiwa inda yake kwaďayin zuwa, nikam tuni kuka yaci k'arfina, amma doctor yakasa control ďin kansa domin lallashina.
   Hummm! aranardai doctor bai barniba saida ya maidani cikakkiyar mace, saidai nasha matuk'ar wahala, nayi kuka harna rasa hawaye, har sumar wucin gadi nayi.
   Shima kansa yasha bak'ar wahala, saidai yauďin yanajinta rana tadaban agareshi, har yarasa irin addu'ar dazaiyimin awanan lokacin, yana gefe yana maida numfashi, yayinda nikam naketa kuka mara sauti, saidai hawaye daketa zurara a kumatuna.
   Bayan kamar minti 15 yaja jiki kusadani, sosai ya ringumeni, nikan atunani zai k'arane dan haka na ruďe dabashi hak'u cikin magiya da dashashshiyar muryata.
   Yanda narikice masa saina bashi tausayi, ya janye jikinsa yana faďin sorry iman babu abinda zan sake miki, nima ina tausayinki.
     Mik'ewa yayi ya kunna fitilar ďakin, wata leda yabuďe yafiddo da magunguna kala2, wannan ya tabbatarmin da dama yashirya zuwan wanan rana kenan.
    Dakansa yayimin wanka ya sakani aruwan ďumi, har sanan ban daina kukakaba, shima yanata aikin lallashina, bayan an kammala wankan yasani nayi wankan tsarki sanan ya naďoni kamar wata jinjira yadire saman kujera, kasancewar gadon duk ya6aci da jini, saida ya cire zanin gadon ya juya katifar, yasake shimfiďa wani sananan ya maidani saman gado.
  Madara yabani nasha kađan, dan bana sha'awar komai asanan, bai takuraniba ya bani magani nasha, yamatseni yamin allura.
    Yasha raki kafin barci ya saceni.
   Ya tsuramin ido tareda sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, fuskarsa cike da murmushi mai k'ayatarwa, acan k'asan zuciyarsa kuwa sai kwararamin addu'oi yake na musamman.
   Wanda ballagazar mace bata samun irinta.
   Jiyake kamar shi kaďai ALLAH yayma wanan gatan na samun nutsatstsiyar mace, nagartacciya, kamila, ahankali yake shafa kaina yanata murmushi abinsa, aii dolene yayta godiyar ubangiji shikam daganan har wayewar gari, bargo yaja ya k'ara lullu6eni sosai saboda sanyin fanka, nikam bammasan yanayiba, inata barcina.
       yamik'e shima zuwa bayi domin gyara jikinsa.
   Yana fitowa yafara jera nafilfili da mik'a godiyarsa ga sarkin sarakuna, shugaban talikai, har k'arfe uku sanan yahawo gadon tareda rungumeni tamkar za'a kwace masani, cikin nishaďi barci yay awon gaba dashi.

     Da asuba yarigani tashi, dan haka bai tadaniba yay alwala suka tafi masallaci shida yayansa da marwan.
    Shidai yayansa sai kallonsa yake cikin mamaki, dan ganin yanda gabaďa ayyukansa ke nuna kasancewarsa cikin farinciki, saboda marwan kawai yakasa tambayarsa harsuka idar da sallah suka fito.
    Koda suka shigo gida sai marwan yawuce 6angaren mama, to anan yayansa yasamu damar tambayarsa ko lafiya?.
    Yayi murmushi yana sosa tsakkiyar kansa, babu komai yayana mikaganine?.
    Yaya yaďan tsura masa ido yana murnushi, ban yardaba auta akwai labari atareda kai gsky, gabaďaya ayyukanka suna nuna alamomin farinciki atareda kai.
    Nanma murmushi yayi yana ďan duk'ar da kai, yayansa yay dariya shikenan tunda ba'aso nasani, k'iladai k'anwatace tajagoranci farincikin, ALLAH yak'ara baku zaman lafiya.
    "Amin doctor yafaďa yana 'yar dariya cike da kunya.
   Kafaďarsa yayansa yaďan buga yana dariya shima, daganan kowa yanufi 6angarensa.
     Har zuwa sanan ban tashiba inata barcina, doctor yazauna gefen gadon saitin fuskata yana murmushi, ahankali ya janye bargon danake k'udundune aciki, ya rankwafo ya sumbaci kumatuna, saikuma yakoma shafa kaina ahankali.
    Na buďe idanuna dasuka ďan kumbura saboda kuka saikuma na maida na lumshe, cikin muryarsa mai daďi ya ce, my saudat adaure atashi ko?, yafaďa yanaďanjan hancina.
    Nakuma buďe jajayen idona na waresu akansa, kallo ďaya namasa na rufe fuskata da hannayena, yayi murmushi mai sauti tareda yaye bargon gaba ďaya, har yanzu idanuna arufe suke, dan haka yaďaukeni gaba ďaya zuwa bayi.
    Da sauri nabuďe idanuna danjin ansakani aruwan ďumi, narik'eshi da sauri da zummar tashi, amma saiya yimini k'yak'yk'yawan rik'o.
    Ashagwa6e nafara faďin ruwan da zafi doctor!.
    Cikin sigar lallashi yake ya ce, "sorry my iman, kinga idan baki shiga ruwan zafinnanba sosai gurin zai ringa miki ciwo, kidaure kinji jarumata, hakadai yaytamin kalamai masu daďi har ruwan ya huce.
   Yamin wanka, na ďauro alwala muka fito.
   Yaďakkomin zanin sallata da hijjab, yashinfiďamin sallaya nayi sallah, ina idarwa na kwanta akan sallayar na hau barci, shikuma yana bayi yana ďauraye zanin gadommu daya jik'a jiya da daddare.
   Cak ya ďaukeni yamaida saman gado, yarungumeni muka koma barci.
   
_*9:30 am*_
        Sai k'arfe tara muka farka, konace bugun k'ofa ya tadamu, doctor yatashi da k'yar yaje yabuďe k'ofar, aunty sadiya ce, bata jira wani abuba tadanno kai cikin falon, yabita da kallo tareda faďin lafiya kuwa?, wani kallo tasakar masa mai tattare da abubuwa masu tarin yawa, ya ďan kauda kai daga kallonta.
   Ta ce, "kalli agogo isma'il k'arfe tara da rabi baku tashiba kaida matarka, kunbarmu munata jiranku ayi break.
   ďan k'aramin tsaki yaja tareda nufo ďakina, saida yaje bakin k'ofa sanan ya ce, "kije muna zuwa, baijira amsartaba yashigo ďakina ya murza key.
   Jitayi kamar yadaka mata kulki akai, tacije le6e tana ballama ďakin harara sanan tafice tana k'unk'uni.
    Shikam yak'araso gaban gadon yatadani, dak'yar na iya tashi ina kare fuska nashige bayi, yakula kamar tafiyata taďan canja, dan haka yabiyoni yana faďin nak'ara shiga ruwan zafi, to na amsa masa akunyace.
   Shima ďakinsa yanufa domin yin wanka.
    Cikin 'yan mintuna muka shirya muduka, ina k'ok'arin fitowa yana k'ok'arin shigowa mukayi karo.
    Ya rungumoni da sauri yana faďin sorry dan naďan bige kaina ajikinsa, na lumshe idanuna saboda k'amshin turarensa dana shak'a.
    Ya ce, "harkin shirya?, kai kawai naďaga masa ina ďan murmushi, na ce, "ina kwana?, lfy lau tawan, yajikinki??, ahankali nafurta lafiyata k'alau nikam, ya ce, "ko?.
    Naďaga kai batarda nayi maganaba, shima 'yar dariya yayi yakama hannuna muka fice zuwa 6angaren mama.
     Da sallama muka shiga, kowa ya hallara mukaďai ake jira, muka gaida mama da yaya, na gaida aunty, su deexerh ma muka gaisa bayan sun gaida uncle ďinsu, na kalli kujerar danake zama yau Raihan ta zauna.
    Deexerh tasan wani k'ulline kawai, dan haka tamik'e akan tata takoma kusada aunty inda yakamata Raihan ta zauna, dama kujerarta kusada doctor take, nida ita muke sakashi tsakkiya, koda tatashi sai muka zauna, doctor yazauna inada deexerh ta tashi, nikuma nazauna kujerar dayake zama.
     Muka fara break, babu abinda kakeji saik'arar cokali da filet, mamadai sai kallona take, dan takula banida walwala ga idanuna sunďan kumbura da kuma ja.
    Nidai akunyace nakecin abincin dan gani nake kamar kowa yasan halin danake ciki, munhaďa ido da aunty yafi ak'irga tana hararata, nikam ko kallo bata isheniba wlhy, dan inada uzuri mai yawa agabana.
   Bayan mun kammala mama takasa hakuri ta ce, "iman kobakida lafiyane??.
    Cikin rawar baki nabuďe baki zanyi magana, idanuna kuma akan doctor, shima kallona yake, ganin kamar zan 6aro masa aiki, yay saurin cewa mama kantane yake ciwo tunjiya da daddare.
    Mama ta ce, "ayya sannu kinji ďiyata, auta tasha magani dai ko??, da sauri ya ce, "eh mama tasha, yanzuma idan munje zata k'ara sha.
   Yayansa dai dariya kawai yayi, dan tuni ya harbo jirgin k'anin nasa, amma dukda haka saida yaymin sanu, da kuma nuna tausayinsa akaina, hakama aunty ta gane komai dan haka adak'ile tamin sannu, Raihan ma dai dan dole ta ce, "sannu.
    Marwan kuwa da deexerh sun nuna tausayinsu sosai, marwan harda faďin aunty bari naje nasamo miki kayan jinya, gasassar kaza kikeso ko mi??, gaba ďaya akasa dariya afalon amma banda aunty, doctor ya ce, "lalai my son yau momy tazama abokiyar wasa kenan?.
    Nandai mukaita dariyarmu, daga baya doctor yajani muka koma 6angarenmu, yakuma bani magani nasha.
     Tsawon kwana uku doctor yana jinyata da riritani, aranar kuma yake shirin tafiya washe gari, jinake kamar karya tafi, gashi inatajin faďuwar gaba, harma na sanar dashi, ya ce, "nayita addu'a insha ALLAHU babu komai sai alkairi.
      Shawararsa nabi nayita addu'a azuciyata, da daddare koda muka kwanta yaso raya sunna, amma saiyaji jikina da zazza6i dan haka ya k'yaleni yabani magani nasha muka kwanta.

_"sosai iman take kuka, wanda yabama su xoxo mamaki, hardai suka kasa hak'uri suka shiga tambayarta dalili, bata basu amsaba saida tayi kuka sosai, konace saida taga k'awayen nata suma sun fara, (kai jama'a wanan k'awance yana burgeni, dan cike yake daso da k'yaunar juna), ta tasagaita da kuka tareda share hawayenta"._
    Ta ce, "abinda yasani kuka, shine tunowa da ranar cin amana, ranar data zamemini barazana arayuwata, har yanzu nakasa mantawa da ita.
    Bayan doctor yatadani yatafi masallaci hakanan na tashi jiki babu kwari, nayi sallah, kasancewar nasan tafiyar wuri yakeyi yasa ban koma barciba, sainaje na haďa masa shayi, nasoya kwai kawai dan banaso yatafi baici komaiba.
    Yana dawowa yatadda ina kicin sai kawai yaje ďakinsa yay wanka, yafito yashirya cikin kakin sojoji, kayan suna masa matuk'ar k'yau, yabaza turarensa na kullum, sanda yafito harna jera masa komai afalon.
     Cikin tsokana ya zauna yana faďin tawan kinaji dani wlhy, yanzunan har an haďamin breakfast, dariya kawai nayi na ce, "aika isane, ya ce, "ko?".
   Na jinjina kai ina murmushi, to nagode yafaďa shima yana shan shayi, saida yagama tsaf, sanan yashiga yimin nasiha mai ratsa jiki, daga nan yaje 6angaren mama da yayansa, bai daďe sosaiba tunda tun dare sukayi sallama, saiya dawo, duk abinda nake buk'ata tun adaren jiya yabani shi, dan haka koda yadawo saiya rungumeni yana faďin dama mama da yaya zasu yarda dasai muyi tafiyarmu musha amarci acan iman.
    Amma nasan bazasu yardaba, insha ALLHU nanda sati biyu zan dawo kinji.
    Nashare kwallar data cikamin ido na ce, "to ALLAH ya tsare minkai, yabada sa'a, yaka'ara ďaukakaka mijini.
    Amin yafaďa yana k'ara matseni ajikinsa, daga nana yahaďe bakina danasa, ayaudai nabada gudummawa, dan sosai nataimaka masa yasamu farinciki wajen sumbata, wadda inada tabbacin yasamu ďin kuma.
     Saida yayansa yakirashi awaya sanan yazare bakinsa daga nawa akasalace, baiyi maganaba ya ďauki jakarsa yasa akafaďa yana ďagamin hannu, nikam nai k'asa dakai saboda hawayen dasuka cikamin ido.
    Banyimasa rakiyaba gudun karnaje gaban mutane ina kuka, saikawai nakoma đakina nakwanta ina kukana.

       _*11:56 am*_
   Har k'arfe shaďaya dawani abu ban tashiba, nayi kuka harna gaji, nikaina bansan dalilin kukan nawaba, saboda bayau doctor yata6a tafiya yabarniba, amma nafijin zafin tayau da kewarsa, zuwa shabiyu saura na hak'ura natashi domin gyara ďaki, ina cikin kakka6e gado naga takarda tafaďo.
    Harna ajeta saman durowar gado dazaton doctor ne ya manta da ita, saikuma zuciyata takasa nutsuwa na ďauka nabuďe.
   _"Inna lillahi wa'inna ilaihirra raji'un"_, kawai nake ammbata, jikina sai rawa yake.
    Adaidai wanan lokacin deexerh tashigo ďakin...............



_*kuyi hak'uri dajina shiru, wlhy abubuwane suka min yawa, amma insha ALLAHU bayan biki zaku cigaba da samun book ďin yanda yakamata masoyana, ina alfahari daku sosai*._
   *luv u oll*







_*((S))..........2017*_
_*luv u oll my fan's*_
_*Battery low*_
Share:

BAN SAKETA BA!. 15

*________________________________*
      *BAN SAKETA BA!*
*________________________________*
                       *NA*
      *BILKEESA IBRAHEEM*
             _*{bilyn Abdul}*_
*________________________________*






_sadaukarwa_ *ya Abdul {city phone's}*




*MIYAKAMATA NAYI?.*
         _'yar uwa! ďan uwa!, yakamata dani dake da kai mutaru mu mutunta juna, k'yautata mu'amularku da jama'a 'yan uwanku, walau musulmai ko ba musulmaiba_
     _karku zama masu girman kai, saboda wata ďaukaka ta duniya, babu wanda yafi wani gurin ALLAH sai wanda ya k'yautata ibadarsa, to ashe nidake da kai duk bamuda tabbas, domin duk k'ok'arin ibadarka wani yafika, ballema yanzu damuka lalace, muka shagala aduniya da kayan cikinta._
    _saika samu mutum yahaďa shekara ďaya bai karanta *alkur'ani* ba, baya sallah akan lokaci, baya neman ilimi akan addininsa, baya tunawa da *ubangijinsa* sai masifa ta rikesa sanan ya ce, "ALLAH ne ya ďora masa, humm kaji ďan adam sarkin butulci da izgilanci, duk sanda alkairi yasamesa saiya ďauka wayonsa da iyawarsace tabasa, wanan kuskurene da jahilci._
    _mudaure murunga neman _ilimi akan addini, bawai aboko_ kawaiba, _saikaga mutim yanata_ _fafa shi yanada digiri ko_ _difloma_ _ko yana karatu a jami'a kaza, amma_ _wlhy idan zaka tsaresa bazai iya_ _kawo maka alwala cikakkiyaba,_ _bare azo ga sallar kanta, amma_ _turanci da iya salo abakinsa ko_ _mista k'yarank'yan yashafa_ _masa lafiya, larabcikan sai ace_ _aiba yarena bane._
    _to hajiyata alhajina shi turanci yarenkine?, hasalima turancin namak'iyankine, afannin addini al'ada jinsi, dan bature bazai ta6a k'aunar musulmiba kuma bak'in mutum, larabci kam abin al'faharinkine tunda koba komai *Annabinmu* yafito daga wanan tsatsonne._
   _Inaga lokaci yayi dazaki gane ka gane na gane cewa da mutunci ake gano mutunci, da ilimi ake gano gyara, to *miya kamata nayi?* na nemi ilimi na addini bawai boko kawaiba._
   *ALLAH yasa muga ne.*




*~page.......15~*
     
          ..................da sauri deexerh ta rik'eni nafaďo hannunta dan tuni numfashina ya tsaya, k'arar da deexerh ta kwallace ta jawo hankalin jama'ar gidan harda yaya dadyn su deexerh.
      Da gudu suka iso 6angarenmu suna tambayar lafiya??, ganina akwance yabasu tabbacin nice babu lafiya ba deexerh ba, aunty ce tafara cewa akira doctor, amma yaya yahana, wani abokinsa aka kira, kafin ya iso yaya yazare takardar daya gani ahannuna, tuni zufa ta wanke masa dukkan sassan jikinsa, sai k'ara maimaita karanta takardar yake kamar wanda akabama hadda.
    Ya maimaitata yafi ak'irga, tuni kuwa ya haddace komai dake cikin takardar, mama tana lura da halin dayake ciki, zuwan doctor ne yahanata tambayarsa.
    Dr Auwal yadubani tareda mak'alamin k'arin ruwa, ya ce, "insha ALLAHU zuwa anjima zan tashi normal, yanzuma wani abune ya firgitani na suma, amma na farfaďo.
    Godiya sukai masa sanan yatafi.
     Dama tuni yaya yabar wajen, yana 6angaren mama, acan mama tasamesa zaune akujera kamar gunki, idonsa cike da kwallah, zuwan mama yasa yatashi sosai, yasa gefen rigarsa ya share kwallar data gangaro masa kaďan agefen ido.
    Jiki asanyaye mama ta zauna dan tabbas tasan ba lafiyaba, yaya yanada k'ok'arin 6oye damuwa komai tsananinta, amma yanzu hakan ya gagara, cikin sark'ewar murya mama ta ce, "Mansur miya faru ne?.
     Yaya yaja ajiyar zuciya, muryarsa naďan rawa ya ce, "mama Isma'il ya saki iman!!.
       Cikin wani irin yanayi mama take kallonsa, ta ce, "ban ganeba Mansur mikakeson faďamini?.
    Takardar hannunsa yamik'a mata, ta kar6a takaranta.....
    *ni Isma'il Muh'd basheer!. Nasaki matata saudat sulaiman saki uku!!. Idan tasamu miji tayi aure.*
      Tuni gumi ya wanke jikin mama, bata buk'atar k'arin bayani danhaka tayi tagumi kamar yanda yaya yayi.
    Yayane yay k'arfin halin faďin mama amma yaronnan ya cucemu, yanzu dan ALLAH dawane ido zamu kalli iyayen yarinyarnan?, ni abindama yake bani mamaki shine miya haďasu dahar zai mata saki har uku?, miya hau kan yaronnan haka?, kuma wlhy mama rubutunsane barema ya musa mana.
     Mama taja ajiyar zuciya toni Mansur ai komaima ya kwace mini, bansan yanda zan kira wanan abinba kuma.
    Haka mama da yaya sukaita tattaunawa, kuma wani abun mamaki sunkira wayar doctor arufe, mama ta ce, "tunda yasan miya aikata ai dole yakashe waya, kabarsa kawai.
     Nikam ina ďaki ina barci, aunty da deexerh da Raihan suna 6angarena, saidai basusan abinda yake faruwaba, dan deexerh ma bata karanta takardarba tunda tana zuwa ina suma.
    Haka akaita tafiya har zuwa yamma dana farka, mama dakanta ta taimaka mini nayi wanka, aka bani abinci naci kaďan har zuwa sanan kuka nake rurus.

*bayan kwana uku*
         Yau tsawon kwana uku kenan angaza samun number doctor kwata2, nikuma namatsa zanje gida, dan yakama iyayena su san halin da'ake ciki, mama da yaya basaso natafi, hakama deexerh da marwan, amma yaza'ayi da k'addarar ALLAH, ganin namatsa yasa mama da yaya suka kaini har gida.
    Bak'aramin ruďani gwaggo tashigaba itada Abbah dajin abinda yafaru, dan su yaya basu 6oye musu komaiba, suka ďora dabasu hak'uri.
    Abbah ya ce, "babu komai haka ALLAH ya k'addara aii, bayan ďan tattaunawa dabawa juna baki su yaya suka tafi aka barni agida.
     Tunda nadawo gida banida wata walwala, kulum cikin kuka nake, ga rashin lafiya data tasoni gaba, dandanan nayi bak'i na rame kamar baniba, lokacin da labari yakai kunanen aunty salma da ya majeed ransu ya 6aci matuk'a, ya majeed ya ce, "bazai k'yaleba saiya ďauki mataki akan doctor, da k'yar abbah da gwaggo suka shawo kansa ya hak'ura.
     Ganin yanda na k'untata kaina agidan yasa ya majeed rok'on abbah yabari nakoma wajensu k'ila zanfi samun sakewa, abbah baiyi musuba dan dama farin cikina yakeso, aranar muka tattara muka koma.
      Acanma haka nayita rashin lafiya wadda tasa dole suka kaini asibiti, tofa wata sabuwa, bayan gwaje2 da likita yayi ya tabbatar mana inada ciki na sati uku, tun agurin nasa kuka sai anzubar dashi, amma ya majeed ya hana.
     Ranar nayi kuka harna godema ubangijina, duk wanda yaganni saiya tausaya mini.
    Muna dawowa gida ya majeed yasanarma su abba halin da'ake ciki, aranar kuma aka sanarma gidansu doctor, mama da yaya sunyi matuk'ar murna da wanan abin farinciki, dan cikin zai zama sanadin cigaban zumincin mu.
     Har tsawon wata ďaya babu labarin doctor kota waya bare kuma ayi maganar dawowa.
     Nikam inanan a6oye inata k'ok'arin zubar da ciki, duk abinda naji ance yana zubar da ciki saina sha a6oye, amma abanza wai man kaza, dan ciki ko gezau, saidai nasha azabar ciwon cikina.
    Ahaka aka akai wata biyu da sati ďaya.
     Awata ranar alhamis doctor yazo kano, saidai kuma yatarar da sabon tashin hankali, dan kowa ya ďauke masa wuta agidansu.
    Kowa ya tambaya iman sai suyi masa banza harsu marwan da deexerh.
      Hankanlinsa yatashi matuk'a, inda yaga sunk'i bashi wata amsa ta gamsarwa sai kawai ya tsare deexerh da marwan da bulala.
    Tsoro yakamasu sosai dan ganin yanda yaburkice musu ďinnan zasu iya shan duka abanza, aiko suka sanar dashi komai, atake jikinsa yay sanyi, yanufi wajen mama hankali tashe.
     Agabanta yashiga rantsuwar wlhy *BAN SAKETA BA!* mama, na rantse da ALLAH k'arya takemini.
     Mama tayi masa banza, wuni guda yana magiya da rok'o amma kowa yak'i saurarensa, dayaga nan babu ci saiya nufi gidanmu, to gara nan abbah yayi masa nasiha da nuna masa muhimmancin yarda da k'addara.
    Shidai doctor bashida wata magana sai *ban saketa ba*, tun suna kallon abun amatsayin wasa harya fara zarta tunaninsu, dan doctor neman zare musu yakeyi, awani daren litinin sai a asibiti ya kwana.
     Wasa2 dai al'amira sun fara tsauri, doctor baisan waye akansaba, kuma indai idonsa biyu bashida magana saita *ban saketa ba*, wannan yasa hankalinsu yayansa yafara tashi suka fara tausayinsa kuma, dan abin yafara wuce makiďi da rawa.
    
   Ahaka cikina yashiga wata biyar, nima kaina nazama mara lafiyar, kulum daga tunani sai kuka, duk sanda na kalli cikina sainayi kuka, har banason tuna inada ciki, duk halin da doctor yake ciki labari yana zuwa mini, dansu aunty salma suna zuwa ganinsa hakama su gwaggo.
    Jikin doctor yay tsanani dole aka maidashi k'asar indiya, dan ciwon zuciya yana neman aikashi lahira, kowa yana tausaya masa.
    Ban ta6a zuwa ganinsaba saidai kusan tare muke jinyar dan kullum zuciyata tana damuwa da halin dayake ciki.
       Karna jaku da nisa, haka cikina harya cika wata tara, zuwa sanan jikin doctor da sauk'i amma ba'a dawo dashi 9ja ba yana indiya abinsa.
    Awani dare juma'a na farka da nak'uda, cikin hanzari muka nufi asibiti, tun anasaran zan haihu acikin awa biyu har likitocin suka fidda rai, dan har washe garin ranar haihuwa shiru sai bak'ar azabar danake sha.
     Har k'arfe sha biyun rana haihuwa shiru, zuwa sannan k'arfina yagama k'arewa, ko ďaga hannuna bana iyawa bare kuma nayi wani nishi, ganin halin danake ciki aka yanke shawarar yimini aiki.
     Babu musu su abbah suka yarda, dadyn su deexerh yasa hannu a maimakon doctor, aka shiga dani  ďakin tiyata.
     Ancuromin yaro namiji k'ato mai kama da babansa kamar an tsaga kara, lallai yau naga farinciki wajen dangin doctor danawa dangin, kowa kamar yacinye yaron haka yakeji, haka nima kowa yana tausaya mini da addu'ar samun lafiya.
     Duk wata hidima yayansa yayita, kuma shima ansanar dashi na haihu, yayi farinciki kuma yasha kuka, dan ranar saida ciwonsa yak'ara tashi, likitoci sunata faďa akan adaina gaya masa komai daya danganci 6acin rai.
    Ina gadon asibiti har tsawon sati uku, dan haka ba'ayi taron sunaba, andai raďama yaro suna *Musayyeef*, to iman ALLAH yaraya mana musayeef, amin.
     Bayan sati uku aka sallamemu, amma wannan karon gidanmu aka dawo dani, dan ina buk'atar kulawar gwaggona, haka nacigaba da rainon musayeef wanda kulum kallonsa yanasani tunawa da ubansa, dan kamarsu tayi yawa matuk'a, kullum mama tana k'ok'arin kwantar da hankalina, ahankali yauda gobe harna dake, komai yafara zama tarihi na maida hankalina akan rainon musayeef.
      Musayeef yanada wata ďaya da kwanaki aduniya aka dawo da doctor gida, danya samu sauk'i sosai, shima yawan addu'ar da aka dage ana masa yasa yadake yanzu, kwanansa uku da dawowa yayansa yarakosa yaga musayeef, jiyayi kamar yamaida musayeef acikinsa, yana matuk'ar k'aunar ďansa gudan jininsa, dak'yar yayansa ya lalla6ashi suka tafi.
    Yayi yayi yaganni amma nak'i amincewa, dole yahak'ura suka tafi wani abu na sukar zuciyarsa.
    Daya koma gida saida aka haďa da lalashi, dan yanzu ba'aso yana tada hankalinsa.
    
Haka naci gaba da rainon musayeef nida gwaggo harya shiga shekara ďaya, asanane kuma ya majeed yabada shawarar nazana s,s,c,e ďina nakoma karatu, abbah ya yarda da shawararsa, dan haka nayi Exam, cikin amincin ubangiji nasamu result mai k'yau, dan haka ba'asamu matsalaba wajen nema mini makaranta.
     ALLAH yacidani samun nan (A B U zariya), samun makarantar yasa na yaye musayeef na maida hankalina akan karatuna.
       Shima doctor yakoma aikinsa yabarma ubangiji komai, amma lokaci2 yana zuwa duba musayeef, hakama yaya da mama da aunty.
    To yanzudai ansaka musayeef makaranta kuma yayansa ne da wanan aikin, idan anyi hutu yana zuwa gidansu hakama weekend ana kaisa yayi kwana biyu.
    Tunda nabaro gidan bansake haďuwa da doctor ba, bamma k'ara zuwa gidanba, idan yazo ganin musayeef kuwa bana yadda muhaďu, zadai akai masa ďansa, kuma susha hirarsu da gwaggo, ammani yagagara ganina, garama lokacin da maman su deexerh zata koma gidan naso zuwa amma ALLAH bai k'addaraba.
    Xoxo ta ce, "oh maman su deexerh takoma??.
   Eh yaya ya maidata yanzu hakama tana gab da haihuwa deexerh tace min.
    ALLAH sarki kai natayata murna wlhy, musamman ma su deexerh dan babu abinda yafi karayu da 'ya'yanka daďi.
    Wlhy hakane xoxo Reefat tafaďa.
     Iman ta ce, "to wanan shine sirrin dana daďe ina 6oye muku.
   "To miyasa kike yawan waige2? cewar Reefat.

 Iman tayi murmushi, wato tunda nazo makarantarnan lokuta da dama nakanji turaren doctor ya yawaita awaje, wanan shine ke sakani yawan kuka da waige2, kuma kunga ranar nagansa, wanan yatabbar mini dashi ďinne saidai yana 6oyema ganina.
     Tabbas labarin iman ya girgiza k'awayenta Reefat da miss xoxo, kuma sunyi alk'awarin taimaka mata har agano gsky, dan suma basu yarda cewa doctor ya saketaba, sunaji ajikinsu *bai saketaba*, amma basu sanar da ita zasuyi komaiba.
    Saidai sun tanmbayeta yanzu ina deexerh?.
      Deexerh tana nan, tana karatu a jami'ar abuja yanzun.
    "Kuna waya?".
 Eh muna waya sosai da ita, kuma aii kunsan haka, saidai sanan bakusan wacece itabane.
   Hakane suka faďa, xoxo ta ce, "yakamata mukaima deexerh ziyara.
    Iman tazaro ido ziyara kuma?, tanafa makaranta nece, eh aii makarantar zamuje, amma sai weekend, tunda bawani nisa bane tsakanin zariya da abuja.
     Shiru iman tayi dan batasan amsar daya kamata tabasuba, Reefat ta ce, "iman kinyi shiru.
    Ajiyar zuciya iman tayi, bashiru nayiba Reefat kawai ganin abun nake abaibai.
    Babu wani baibai, deexerh sa'ar muce, kuma tana k'aunarki aii yakamata zumincinku yacigaba karya yanke.
    Xoxo ai zumincinmu bai yankeba tunda muna gaisawa, kuma idan ina kano tana zuwa aii mugaisa, tana zuwa ta ďauki musayeef.
   Eh dukda haka, yakamata mukai mata ziyara.
    To shikenan saimu duba ranar daya dace saimuje kenan.
   Okey ALLAH yakaimu.

Ammafa iman kinsamu akwali, wlhy da duk zatonmu gwaggo ta haifi musayeef.
   Dariya iman tayi ta ce, "tokuyi hak'uri.
   Suma suka dara tareda faďin yayuce, munyimi uzuri.................







_*((S)).........2017*_
_*luv u oll my fan's*_
_*battery low*_
Share:

BAN SAKETA BA!. 11/12

[27/04 16:20] bilyn Abdul: *________________________________*
         *BAN SAKETA BA!!!*
*________________________________*         
                      *NA*
     *BILKEESA IBRAHEEM*
          *{bilyn Abdul}*
*_______________________________


*MIYAKAMA NAYI???.*
          _ba matane kawai suka shagala a *duniyaba* harda abokan jinsinsu wato *maza*_
    *maza* _ma sun shagala a *duniya* wlhy, zakaga babban mutum magidanci mai tarin *zuri'a* amma yana wasa da ibada, saboda uzurin office kona kasuwa._
    _wani akan kunnensa liman zai kwala kiran sallah, amma saiyace bari yagama sallamar *customers*  sannan, wani kuma idan a office ne saiya kawo uzurin k'are takardun dake gabansa_
   _Haba ďan uwa duk abinda kakenema yana wajenfa wanda aka kiraka domin bauta masa, magidanta sunada matuk'ar sakaci awajen yawan nafilfili na dare da azumin nafila, saboda hujarsu tacewa sunje nema sun gaji_.
    _A'a ďan uwa gyara sai ALLAH ya gyara maka, gyara kodan iyalinka suyi koyi dakai, amatsayinka na uba, miji, shugaba._
     _Abinda mukayi da shi 'ya'yanmu zasuyi koyi, su tsira mu tsira, aranarda aikinmune kawai garkuwarmu!!!!!!!._
    *ALLAH yasa muga ne.*






~page........11

                ................bayan sun idar da sallah suka sake zama.
    Iman ta ďora labari."

         Bayan nagama tsara kwalliya na baďe 6angarena dawani sabon k'amshin, dan nasan mijina ma'abocin son k'amshine, gida yaďauki haramin k'amshi tamkar gidan saida turare.
    Duk wanan aikin cikin dauriya da jarumta nakeyinshi, ina zama saiga deexerh tashigo da sallama, hannunta ďauke da filet.
    Naďago ina amsa mata tareda tsokana, ďiyar uncle mi'aka samomanane?.
    Kusadani tazauna tana dariya, abinda kike matuk'ar so nasamo, ammafa saidai ayi cinikinsa.
    Da sauri na ce, "indai har abinda nakeson ne, to mikikeso nabaki??, taďan langa6e kai alamar tunani, saikuma taďago tana faďaďa murmushinta, ba kuďi nakesoba, sonake ki lalla6a min uncle yasa dady yakaimu wajen mom ďinmu gobe idan ALLAH yakaimu mu wuni acan.
    Tabani tausayi matuk'a, amma gudun karna karya mata zuciya sainayi murmushin k'arfin hali, na ce, "insha ALLAHU dee.....ďin uncle zanyi wanan k'ok'arin.
   Ta faďaďa murmushinta tareda faďin ngd sosai auntyna k'awata, mamana, kuma ta biyu, shiyyasa akulum nake k'ara sonki, zuwanki gidannan yasa muka k'ara rage maraicin rashin uwa akusa, dukda k'ok'arin mama na son sharemana hawaye itada uncle, ta k'are magana da matso kwalla.
    Hannu nasa ina goge mata hawayen, badan karna k'ara tada mata hankaliba dana tambayeta dalilin barin mom nasu gidannan, amma saikawai nacigaba da lallashinta.
     Bayan wasu 'yan mintina ta lafa da kuka ta bani filet ďin dake rufe, cikin zaro ido na ce, "lah dee.... ina kika samo fara??.
    Tayi 'yar dariya, wlhy a school na siyo miki saboda nasan kina sonta sosai.
    Rungumeta nayi ina murna damata godiya harda addu'ar fatan alkairi arayuwa..........da sauri muka juyo danjin k'arar buďe k'ofa da matuk'ar k'arfi.
    Cikin sanyin jiki muke kallonta, sa6anin ita datake kallonmu cikin tsana da tsangwama, ta ta6e baki tana yatsina, bazanyi mamakiba domin yanzu mace da macema haďuwa suke su sa6i ALLAH.
    afirgice muke kallonta danjin ficinta mai matuk'ar muni da firgici.
     Deexerh ce ta iya daurewa tafurta wani abu, ta mik'e tana kallon matar baban nata cikin tsana, ''k *Sadiya!!!* kishiga hankalinki wlhy, muba shaiďanu bane bare ki jinginamu da wanan fasik'ancin, kuma tabbas daga yau munta haďaki da ALLAH kenan acikin sallolinmu harsai ya saka mana, kuma zakiga fasik'ai insha ALLAHU a zuri'arku, _tsumma mak'ullin cuta kawai_ *ALLAH zaimana maganinki komai daren daďewa* deexerh nagama faďa tafice daga falon tanufi 6angaren mama tana kuka.
        Nikam aii mutuwar tsaye nayi ga marata ta k'ulle tamau, itama auntyn tana tsaye tamkar gunkin da aka dasa awaje ďaya, ta maido da kallonta gareni zuwa sanan nafara shiga mawuyacin hali..... dan 6acin ran maganarta yasa marata tayi wata muguwar wakitawa, kafin tayi wani yunk'uri nafaďo k'asa ina murk'ususu, adai dai kuma wanan lokacin doctor yashigo falon.
      Da gudu yak'araso gareni yana kiran _iman! Iman!!_ ina nayi nisa cikin ciwo, arikice yaďagoni jikinsa yana girgizawa saiga su mama da deexerh sun shigo.
     Mama tak'araso arikece tana tambayar lafiya??, tanayi tana kallon aunty sadiya dan deexerh taje ta sanar mata abinda aunty taimana.
    Aunty ta ce, "wlhy mama bansan miya sametaba, nima naga kawai ta faďi tana rik'e ciki........doctor yakatse musu zancen da faďin karku damu mama nasan matsalarta, rik'eta ina zuwa.
     Mama ta kar6eni doctor kuma yafice domin nemo allura.
   Tunda yatafi nake murkususu ajikin mama dakiran sunan gwaggo, dakuma duk addu'ar datazo bakina.
    deexerh sai kuka take azatonta abinda auntyn tayi manane yakawo ciwon, lokacin da soctor yadawo har suma nake dan azaba, tareda yayansa suka shigo.   
    Mama ta rik'eni yay min allurar, zuwa wani lokaci sainayi sakwat alamar ciwon ya gudu, harma barci yafara ďibata.
    Mama ta ce, "isma'il  ďaukrta kakaita ďaki.
   Kamar jaririya haka ya ďaukeni yakai saman gado yadire, yana mai k'ara jin tausayina da tuhumar kansa akan sakaki, dan yasan shine maganin matsalata amma yakasa min maganin tunda wuri, saboda shagalal dayayi akan wata yawuce banyiba.
     Rashin lafiyata ta hana tada maganar da aunty tayi mana.

    Har dare ina barcina ba'a tadaniba.
   Dak'yar suka lalla6a doctor ya halarci wajen cin abincin, sai asanan mama da deexerh da marwan suka san da zuwan Raihan, basu canja da komaiba suka k'ar6eta kamar yanda suka saba, dan sunsan laifin yayartane, _(laifin wani kuwa aii baya shafar wani)_.
       Sai bayan isha'i na farka, lokacin doctor yatafi masallaci shida yayansa da marwan, deexerh ta taimaka min na gyara jikina tsaf kamar komai bai faruba, sanan muka nufi wajen mama.
    Tana falo zaune muka shigo, tabini da kallon mamaki 'yar nan wanan ciwo naki tamkar iska?.
   Nayi dariya tareda risinawa ina gaisheta, ta ce, "yajikin??.
   Da sauk'i mama aii yakuma tafi.
   To ALLAH yak'ara sauk'i ya kiyaye gaba, na ce, "amin mama, anan ne mama take bani hak'uri akan abinda yafaru ďazu, takuma rok'eni karna gayama mijina.
   Babu komai mama insha ALLAHU bazai jiba, kumani wlhy harma na manta.
   Yauwa ďiyar kwarai ALLAH yayi miku albarka kunji, nida dee....mukace amin.
       
Muna nan zaune muna 'yar hira saiga marwan yashigo, mukai masa sannu da masallaci ya ce, "yauwa auntys, yajiki aunty??, da sauk'i marwan aina warke........kafin yabani amsa Raihan tashigo falon, muka amsa mata sallamar datayi, nidai sai binta nake da kallon mamaki dan bansantaba, saidai suna kama da aunty kam.
    Ta zauna tana min sannu da jiki, cikin sanyin jiki na amsa mata, deexerh ta ce, "k'anwar aunty ce, ďazu tazo.
     Na ce, "ayya sannu da zuwa".
  Ta amsa da yauwa kema sannunki.
    Doctor yashigo shima yana faďin dama kinan nan iman??, eh ina nan babu daďewa muka shigo nida dee...., okey yafaďa yana zama kusadani, ya ce, "yajikin naki??, Alhmdllh nafaďa kaina ak'asa saboda kunya.
     Mama ta ce, "auta kundawo?.
 Eh wlhy mama mundawo.
   Ta ce,  "sannunku."
 Yauwa mama.
      Sau wajen huďu ina kama Raihan da doctor suna kallon juna, shi idan ya kalleta yakan janye idonsa amma ita ko gezau bare kunyar mama.
    Zuciyata tashiga nazarinsu, dan suna kallon junane cikin rashin gsky da alalomin tambaya??.
   abinda na kula bani kaďai nagane hakanba, harsu mama suna kallonsu, kallo ďaya nayima mama kuma nagano alamar 6acin rai afuskarta, da ga k'arshema sainaga kawai ta tashi tabar falon.
    Lokacin maga tamkar alamun tsoro sun bayyana afuskar doctor, akasalance yakama hannuna mukabar falon muma, tareda faďin saida safenku.
   Koda muka koma 6angarenmu ban tanbayesa wacece Raihanba?, zama kawai nayi saman kujera, shima yazauna yana shafa kaina my iman sannu kinji, wlhy lokaci k'an k'ani kinsha wahala.
    Ban cemasa komai ba, dan wasu abubuwa suna yawo akaina, ganin bazan tanka masaba yasashi mik'ewa yashiga ďakinsa.
    Babu daďewa yafito sanye da gajeren wando da bes,  yazauna k'asan kafet ya ce, "nakawo masa kayan marmari yasha.
    Akasalance namik'e zuwa kicin yayinda shikuma yabini da kallo mai cike da tunani iri2.
   Nakawo masa yankakkun kayan itatuwa na ajiye.
   ya ce, "sannunki.
   na ce, "yauwa.
 Harna juya zan koma ya ce, "zo mana, babu musu nadawo, ya nunamin kusadashi, nanma ban musaba na zauna.
    Ya ďako abarba zuwa bakina, amma saina girgiza kai na ce, "nak'oshi.
    Yaďan rage fara'a, idan na amince kin k'oshin ko??, yafaďa yana 'yar hararata.
       ban ta6a ganin fuskarsa a haďeba sai yau, dan haka na buďe baki yasaka mini, haka yayta bani shima yana sha har muka k'oshi.
    Daganan falon muka zauna saidai yau babu hira, idan na kalli doctor ma sainaga bashida walwala, dahaka har goma tayi mukaije muka kwanta konace na kwanta.
   Dan harna fara barci sanan naji motsin shigowar doctor ďakina.
  Ban motsaba bare yagane na farka, ya hawo gadon ya kwanta saidai amamakina yau bai rungumeniba tamkar yanda yasaba, abin yabani mamaki amma saina danganta hakan da gajiyar tafiya dakuma fashin sallah danakeyi.
    Wasa2 har wajen k'arfe ďayan dare doctor bai runtsaba, nima ko barcin ya ďaukeni saina farka saboda yawan motsin da yakeyi, yanzu tunanina yatashi daga zargin farko, yakoma akan Raihan k'anwar aunty.
   Tabbas akwai abinda bansaniba, akwai wata alak'a tsakaninta da doctor da Raihan.
   _" wai wacece *Raihan* ne???._
Mutum ďayace zata bani amsar tambayata, wato _*deexerh!!!!.*_.
       Sai gabannin asuba barci ya ďaukemu, wanan yasa muka makara sallar asuba.
    Ban koma barciba nafice wajen aunty kamar yanda nafara kwanan nan dan yanzu dani ake girkin gidan.
    Shikam doctor barci yakoma.
   Haka mukayi aikinnan nida ita bamaima ďan uwansa magana dama haka mukeyi dan babu shak'uwa tsakanina da ita.
   K'arfe bakwai na safe muka gama haďa break 'yan aiki suka kwasa zuwa 6angaren mama, mukuma kowa yanufi ďakinsa.
    Koda naje ban kwantaba saikawai na hau gyaran 6angarena dukda bawani datti bane, tunda nakula doctor baya ra'ayin masu aiki nima saina daina sakasu gyaran wajena, nazage inayi da kaina.
    Bayan nagama nayi wanka nashirya tsaf cikin rigar material doguwa, ina fesa turare doctor yatashi.
    Yadaďe datashi ban saniba, idonsa na kaina duk motsin danayi saiďan murmushi yake yana lumshe idanu, tacikin madubi nagansa tsaye abayana sanye cikin pink ďin kayan barci.
    Najuyo ina faďin lah katashi?.
   Murmushi yayimin ya ce, "badoleba tunda gimbiyata tatashi bata tadaniba.
   Kaina ak'asa ina wasa da zoben hannuna na ce, "kayi hak'uri to dan ALLAH, naga bakayi barci ishashshe bane jiya.
   Maimakon  yabani amsar tambayata ta k'arshe, saiya ďauki ta farko yay sharhi akai. 
    hannuna yakama yana murzawa karki damu na hak'ura, aike bak'ya laifi awajena my iman, kinrigaya kin mallake zuciyar Isma'il daduk wani aikinsa.
    Huumm to shikenan ngd, yakamata kayi wanka ko?.
   Nafaďa ina zare hannuna daya rik'e.
                  Bai iya amsaminba saidai bina da kallo dayayi harna fice, aďakinsa na haďa masa ruwan wanka, sanan nadawo shikuma yatafi.
                              ☆
A falon mama duk mun hallara muna break, yauma tamkar jiya haka doctor da Raihan suke satar kallon juna, zuwa can kuma saina farga da taka k'afar doctor da Raihan takeyi ta k'ark'ashin tebir, shikuma yana janyewa.
     Abisa tsautsayi ta taka k'afata saboda nike kusada doctor, na kalleta muka haďa ido sosai, saitayi k'asa da kai cikin jin kunya.
    Dahakadai muka kammala break, yayansa ya ce, "yazo su tafi kasuwa..
    Sallama sukai mana suka tafi, muka rakasu da ALLLAH ya kiyaye hanya..

    _*miss xoxo da Reefat*_ sukace tofa kaji wata sabu kuma??, iman kin k'ara sakamu atunanifa.
   Shin wacece Raihan!!.?
_*iman*_ tasaki murmushin basarwa, karku damu 'yan uwana, zuwa gobe zakusan wacece Raihan, ammafa kar tazame muku matsala, dan ita ba matsala baceba.
    To ALLAH yasa hakan, suka faďa kowa yana kwanciya................




Page 12

 *MIYAKAMATA NAYI??,*
                 _Komai ka rasa zaka iya samun wanda ya fishi, Amma banda kwanakin rayuwarka, idan sun tafi sun tafi kenan, Domin haka karka 6ata rayuwar ka wajen abinda bazai amfane ka ba, yi kokari wajan yin abinda zai amfaneka duniya da lahira...""_
       _kyautata ibadarka domin danmu bautama ALLAH ya halicemu, idan baka iyaba  ko kanada k'arancin ilimi nemi malami ya koya maka, ba'a ibada da jahilci, "ubangiji baya kar6ar ibadar jahili._
    _muguji salwantar da yininmu da kwananmu akan duniya da abinda ke cikinta, domin lokacin ďan adam mai tsadane, asarar second ďaya ga mumini daidai take da asarar shekara dubu._
    _Mizai hana mutsara lokacinmu domin ammafanarsa a ranar data dace_.
   ```Karka bari duniyarka taringa tafiya tamkar cin abinci, dakaci saikayi kashi, kaga kuwa sara kenan```.
   _gyara yau da gobenka domin amfanar jibinka_
  *ALLAH yasa mugane.*


_*wannan page ďin nakune 'yan group ďina, ina alfahari daku sosai, ina k'aunarku har bansan iya adadiba, ALLAH yabarmu tare, kuďin nadabbane agareni, luv u wujiga wujiga, lol.*_


~*Page.......12*~

         ..................Bayan tafiyarsu kowa yakama gabansa, deexerh da Raihan suka fita raka mama wani guri, aunty ma takama gabanta, nikam saina tashi nashiga gyara 6angaren mama wanda ayanzu nice nake gyarwa na hana masu aiki yi.
     Bayan na kammala na koma 6angarena, wanka na sakeyi dan 12 ta wuce, yau banajin kwalliya dan haka nashafa fauda kawai da abinda ya sauwak'a, bak'ar doguwar riga nasaka nayi k'yau sosai saboda k'ibar dana ďan k'ara, ga fatata ta murje gwanin sha'awa.
    Falo nadawo na kwanta saman doguwar kujera tareda lumshe idanunana ina tunanin karatuna, inason na koma makaranta na k'arasa karatuna.
    K'amshi yacikamin hancina, na buďe idanu ahankali, doctor nagani tsaye akaina yana min murmushi.
   Na mik'e da sauri ina faďin sannu dazuwa, ince dai lafiya??, ya ce, "saiba lafiya mai gida yake dawowa gidansa?."
   Na ce, "a'a, na kar6i ledar hannunsa dayake mik'omin, ya ce, "rakene nagani ahanya shine nasiyo miki ban saniba kozaki sha?.
     Murmushi nayi na ce, "ina sha mana".
     Na ajiye ledan saman tebir nanufi kicin, ruwa nakawo masa yasha, ya ajiye kofin yana faďin ngd sosai _gimbiya_, nikam duk kunya ta isheni dan haganin mayataccen kallon dayake bina dashi.
    Kamar daga sama mukaga an banko k'ofa, gaba ďaya muka maida kallonmu wajen, aunty sadiya ce, ta ce, "lallai Isma'il dawowa kayi da wuri haka, lafiya kuwa??.
    Ya daure ya ce, "lafiya lau aunty nazo ganin k'anwarkine.
  Ta ta6e baki yo har yanzu batada lafiyar??.
   Yaďan rage fara'a ta warke ina kwaďayin gani k'yak'yk'yawar fuskartane kawai.....nikam gaba nayi zuwa kicin domin haďo mada abin motsa baki.
   Batace komaiba tanemi guri ta zauna, ta jawo ledan raken gabanta mikuma aka kawo mana ne??, baice mata komaiba dan al'amuranta sun fara bashi haushi, nashigo falon da sallama, shikaďai ya amsa mini, naje gabansa na ajiye filet đin kayan marmari.
    Ya ce, "ngd babyna".
 Nayi ďan murmushi kawai sanan nakoma kujerar nesa dashi na zauna.
   Ya kalleni taso kisha mana?, na ce, "a'a duk nakane......kafin yayi magana aunty ta ce, "nida ba'amin tayiba bari nazo nasha, kan kujerar dayake zaune tadawo ta zauna kusadashi daf, taďauki cokali tahausha.
    Ya ce, "a'a aunty mu mun isa muk'i yimiki tayi yafaďa yana matsawa, dayake doguwar kujerace.
   Nikam nayi gum dan mamaki take bani idan tana wani 'yan kamancin, ya kalleni iman yadai?, ďan murmushin k'arfin hali nayi na ce, "babu komai.
   Itakam ko kallo ban ishetaba sai danna abinta take.
   Ya mik'e bari naje na watsa ruwa dan duk nagaji, na ce, "afito lafiya.
    Ya nufo inda nake ya kama hannuna yana faďin aikece zakimin wankan, baibi takan auntyba muka nufi ďakin yana faďin aunty muna zuwa.
    Wata uwar harara tarakomu da ita wadda nikaďai nagani, taja tsaki tatashi tafita, azuciyata na ce, " *kishin banza*.
      Miss xoxo ta ce, " *kishin banza kam* tunda ba miji kuka haďaba, wai dama ana samun irin haka??.
   Reefat ta ce, "sosaima, wannan shi ake kira kishin sauri, wlhy wasu irin wanan kishin yakesa suraba zumincin family ďin mazansu, akwai mata dayawa dake kishin banza kamar haka, kiga matar k'ani ta tsani matar wa, matarwa tana kishi da matar k'ani, tamkar mijinsu ďaya.
   Miss xoxo da iman sukace to ALLAH ya shiryamu
        *(ni bilyn Abdul na ce, "wanan asarar lokacine, yakamata mata kugane badan kishi aka haliccemuba bare ki 6ata lokacinki awajen kishin, garama ki nutsu kisan inda yake miki k'aik'ayi ki sosa, baki k'are akan kishin banza mara amfaniba, ALLAH yaganar damu)*
      Reefat tamik'e taje tayo fitsari tadawo, drinks ta ďakko musu tazubo cincin afilet ta ajiye musu dan labarin sai anayi ana jik'a makoshi.
      _(nima bilyn Abdul ina gefe danawa na katsire ina korawa dan inji daďin kwaso muku rahoto *lol*)_
     Miss xoxo ta ce, "sis....jamije mana."
     Iman ta haďiye lemon dake bakinta, taci gaba.
   Bayan mun shiga ďaki ya zaunar dani bakin gado shima ya zauna kusadani, naďan takure jikina dan bako yaushe nakeso yata6aniba.
  Hannuna yakamo ya damk'e anasa yamatso kusadani sosai, yana faďin abinda bak'ya son, dan tuni nakula bakison na ra6u jikinki bansan miyasaba?.
    Na duk'ar dakai k'asa, ya ce, "faďamin kobaki sonane??, na girgiza kai alamar a'a,  ya ce, "to minene dalili?.
     Ahankali nađago kai ina kallonsa, ganin ya tsura min idonsa yasa nayi saurin maida kaina k'asa, na ce, "dama umma ta ce, "mana karmu yarda namiji yarik'e hannunmu, inkuwa ba hakaba zamu samu ciki.
     Bai san sanda ya tuntsure da dariyaba harda kwanciya akan gado, nikam nasaki baki ina kallonsa, dan ba k'aramin k'yau dariyar taimasaba, inason sa sosai, harma bansan yanda zan musalta ba.
    Jinayi an huremin idanu, naja wata ajiyar zuciya mai k'arfi, yay murmushinsa mai k'ayatarwa, sannan yagyara zamansa ya ce, "saudat!....yakira sunan dawata irin murya mai cike da kasala.
   Na ce, "na'am".
   Ya ce, "aii gwaggo tafaďa miki hakane danki kare mutuncinki ga wanda ba mijinkiba, nikuma mijinkine yafaďa tareda nuna kansa, aii ni yanzu ko rik'e hannun naki nayi kika samu ciki babu matsala, su gwaggoma murna zasuyi da samun jika.
   K'asa nak'arayi dakai, shikuma yarungumoni sosai zuwa kikinsa yana faďin inasonki dayawa iman, ya ďago ya mannamin summba akumatu mai shiga jiki da 6argo.
   Nikam sai k'ara sinne kaina nake ajikinsa ina k'ara shak'ar daddaďan k'amshin turarensa.
   Jin anturo k'ofa ko sallama babu yasa yaďago kai da sauri yana kallonta, nima namik'e zaune sosai inaďan janye jikina daga nasa.
   Lafiya kuwa?, doctor yafaďa yana kallonta.
   Ta juya idanunta dasuke manya sosai nazo kiran iman ne mu ďora abinci.
     Ya ce, "to tana zuwa, ta kalleshi yanda yawaniyi kicin2n da rai, tasan halinsa sarai idan ransa ya6aci dan haka tayi waje tana kun kuni.
    Na kallesa ya haďe rai sosai kamar bashine yagama dariyaba yanzu, tsaki yayi sanan yamik'e yana faďin kwanannan zanyi maganin 'yar isakar matannan wlhy, nidai bance komaiba, yashige bayi.
   Nimadai abin mamaki yake bani dukda k'arancin shekaruna, kuma gidanmu bantaso naga kishiyaba, bare nasan yanda ake kishi, saidai nakanji ana faďar kishi kishi.
    To amma su waďancan ai mijinsu ďaya, nikuma ba mijinmu ďayaba, to kenan wanan kishin banzane takeyi??.
   Maganar mama naji tana faďin ina iman ďin takene?, namik'e da sauri na nufo falon ina faďin mama ganinan kundawo??.
   Ta ce, "eh nadawo su nabarasu acan.
  Na ce, "sannu dazuwa."
  Ta ce, "yauwa sannunki kema"
         Makullin 6angarenta naďauka muka tafi, nabuďe muka shiga, ruwa maisanyi naďako nabata tasha, ta ce, "ALLAH yayimiki albarka.
   Na ce, "amin mama".
 Doctor yafito daga bayi yaga bana nan, sai zuciyarsa tak'ara tunzura, wato yarinyarnan tafiya tayi wajen girkin tabarni saboda kiranta yafini ko??, yaja dogon tsaki yafice, ďakinsa yanufa yashiga wanka, yafito yay shirinsa cikin k'ananun kaya, yayi k'yau sosai.
    Yadawo falon yazauna, yana kallo yana shan raken daya siyo.
    Yaji shirun yayi yawa dan haka yamik'e yanufi 6angaren mama yagani idan tadawo.

     Da sallama yashigo ganin inama mama matsar k'afa sai yayi turus.
   Mama ta kallesa a'a auta kadawo?, ince dai lafiya?.
   Ya ce, "lafiya lau mama nadai dawone kawai, zaman kasuwarnan saisu yaya surutun yayi yawa, har kaina yafara juyawa shiyyasa nagudo.
    Yazauna yana hararata.
Mama ta ce, "mitayi maka kake harararta ne?.
   Da sauri ya ce, "babu komai mama, yana magana yana sosa gefen wuyansa.
   Nayi k'asa dakai ina murmushi danya bani dariya sosai.
    Mama data fahimci inda muka dosa saitace yauwa ďiyata barshi haka ai k'afar tama saki sosai ngd.
  Nayi murmushi ta reda faďin to mama sannu.
    Namik'e nafita batareda na kalli doctor ba.
    6angaren auntyn nanufa, kai tsaye nanufi kicin dan nasan sunacan da masu aiki.
   Koda nashigo saita haďe girar sama data k'asa, na ce, "sannunku da aiki, masu aiki kaďai suka amsa amma ita ko kallo ban ishetaba.
   Nima banbi takantaba dan indai miskilancine gidan ta taras.
    Haka mukayi aikin muka gama batareda mun kula junaba.
       6angaren mama muka kai abinda yadace, har yanzu doctor yana can suna hira da mama, muka gama jere komai, sanan muka fita.
    Saida mukayi sallar azuhur sanan aka ci abincin, yauma saimu huďu kawai, tunda muka zauna cin abincin doctor yaketa haďe rai, nasan saboda aunty yakeyi dan haka abin bai dameniba.
    Muna gamawa na nufi 6angarenmu dan naji zufa ta tasomin, gashi arayuwata idan ina cikin al'ada sainatayin k'yan k'yamin kaina, sainayi wanka sau shida arana bai wadaceniba.
    Babu daďewa saiga doctor yabiyoni har yanzu fuskarsa babu walwala sosai.
   A bedroom yasameni ina shirin shiga wanka, nayi k'asa da kaina dan ganin ya nufo inda nake, gashi dagani sai guntun tawul, kama tawul ďin yayi kamar zai kwance, da sauri narik'e tawil ďin da hannunsa ina zaro ido ..........yaďan murmusa kaďan iman kincika tsoro wlhy, ahaka wai zaki haifamin yaran danake mafarki? , hannu nasa narufe fuska yayinda shikuma yasamu damar zame tawul ďin daga jikina.......
     Kai jama'a mutashi muyi sallah, miss xoxo ta harareta kai iman ALLAH kina jamana rai, wlhy kuwa xoxo Reefat tafaďa tana kwa6e fuska, yakamata kiďan k'ara mana nan.
    Dama muna binki bashi akan sanin wacece Raihan?. 
    Mik'ewa iman tayi tana faďin 'yan duniya kudai wlhy sai gyaran ALLAH, yara baku tafasaba zaku k'one.
    Raihan kuwa kumanta da batunta ita bakomai bace.
   Xoxo da Reefat suka tuntsure da dariya suna faďin keda kika tafasa har kika k'one aii saiki nuna mana hanya.
   Dan wlhy duk kawaice2nki saikin bamu bayanin _firstnight_     , saikuma munsan wacece Raihan?.
    da sauri iman tashige bayi tana dariya, sumadai aminan nata dariyar suke tuntsurawa sosai...................  

*To nima bari na k'yak'yata*
_lol._








((S)).........2017
luv u oll my fan's
battery low
Share:

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *